A zamani da can baya, Bahaushe ya yi rawar gani wajen kafa kyakkyawar tarbiyya da kuma yaɗa ta ga maƙota.
Hausawa a da can suna da kyakkyawar ɗabi’a ta fito da abinci. A zauna a ci tare a ƙofar gida. Wannan ɗabi’a ta sanya soyayya, da haɗin kai, da sanin halin da maƙoci yake ciki.
A Wancan Lokacin ɗa nakowa ne “. Maƙoci ko sauran manyan uguwanni na tsawatar wa yara, a duk inda yaro yai kuskure.
Su Kuma iyaye da aka tsawatarwa ɗansu. Suna godiya idan suka ji labari. Sannan su ƙara ladabtar da ɗansu.
Hausawa suna da kunya akan Al’amuran yara. Akwai zumunci mai ƙarfi a da can baya. ‘Ya’yan Uba ko ƙannensa, suke zartar da hukunci a kan ‘ya’ya ɗan uwansu. Kuma duk hukuncin da suka yanke ya zartu. Suna taimakawa juna sosai.
Duk abin da Uba zai yi kamar ɗinki. Shi ne zai haɗa na yara ‘yan uwansa ya yi musu Babu nuna bambanci.
Budurwa ‘yar Bahaushe tana zance ne cikin kunya, tare da ɗan rakiya. Ba ta shiga lungu ko duhu. Ta san tana da daraja da tsada. Tana da ƙayyadadden Lokaci da ranaku zance.
Al’ada ta girmamawa kuwa, kowa ya san cikakken ɗan Hausawa ya tashi da gaida na gaba da shi. Gaisuwa ma har sai ya tsugunna. Kuma in zai wuce iyayensa ko malamai sai ya cire takalmansa.
In kuwa haka ne, kyawawan halaye da ɗabi’un Hausawa. To a Ina aka haihu a ragaya? Har mu ka tsinci kanmu a wannan Lokaci da tarbiyya ta lalace.