Yadda Al’ada (Jinin Haila) Yake

1
783

A wannan shafin za mu tattauna akan abubuwan da suka shafi al’adar ‘ya mace. Yadda zaki san in al’adarki daidai take ko kuma kina da matsala. Abubuwan da za kiyi amfani dasu idan kina al’ada kamar: Auduga (Pad) da tsumma da sauransu. Yadda zaki tsaftace jikinki da suturar ki idan kina al’ada.

Mecece Al’ada?

Ita al’ada jini ne ko kuma gudan jinni wanda yake fitowa daga mahaifa a jikin mace. Al’ada na zuwar wa mace duk wata. Aduk sanda kika ga irin wannan jinin to shi ake nufi da al’ada.

Me Ake Nufi Da Lokacin Al’ada (Jinin Haila)

Lokacin Al’ada lokaci ne da yake shiryawa jikin mace ɗaukar ciki duk wata. Lokacin al’ada na amfani da abubuwa guda biyu irin su estrogen da progesterone.

Bayaninsu ya tafi kamar haka: A jikin mace akwai ƙwayaye guda biyu, kuma kowanne yana riƙe da ƙwayaye ba adadi a cikinsa, kwayayen ƙananu ne, wanda idanu baza su iya ganin sa ba, sai da taimakon na’urar gani. Lokacin al’ada, ƙwayayen suna girma, wanda hakan shi yake nufin cewa maniyi yake jira su haɗu, su haifar da ɗa.

Bayan mace ta gama al’adar ta, akwai wani mataki da zata shiga, wanda ake kira da “Ovulation”. Da yawan mata basa sanin lokacin da sukeyin ovulating, saboda ba abu bane da mutum zai tayar da hankalin sa. Alamomin ovulation su ne; ciwo a ƙasan mara, wanda zaki ji a ɓari ɗaya ko duka biyun. A turance; bloating, spotting da sauransu.

Lokutan Da Al’ada Take Farawa Da Kuma Tsayawa

A wani lokacin girman ‘ya mace, wasu matan suna fara al’ada a shekara sha biyu zuwa sha huɗu. Amma wasu suna ganin nasu da wuri, tunda yanayin jiki ba ɗaya bane; kuma babu tabbacin ga lokacin da zaki ga al’adar. Amma idan baki ga al’adar kiba, har kika kai shekara goma sha shida (16), to ki tuntuɓi likita.

Yawancin mutane suna daina ganin al’adarsu idan sun kai kimanin shekaru arba’in da biyar (45) ko hamsin da biyar (55), wanda aka fi sani da menopause (lokacin da mace zata daina al’ada). Al’adar mace tana farawa da tsayawa, kamar yadda ragowar mutane suke yi. Amma taƙaitaccen lokacin dainawa shi ne daga shekara arba’in da biyar zuwa hamsin da biyar.

Abubuwan Da Mace Zata Iya Amfani Dasu Idan Tana Al’ada

Mace idan tana Al’ada zata iya amfani da su audugar mata da tissue da tsumma da sauransu. Su waɗannan da aka lissafo, suna da inganci a rayuwar mace. Su suke taimakawa wajen tsafta da kuma hana jinin ya ɓata jikin ki.

1. Audugar mata (Pad): Auduga ce mai fiffike guda biyu, wadda zaki yi amfani da ita wajen hana jinin ya ɓata jikinki. Ita ce mafi ingancin auduga da zaki iya amfani da ita, suna nan kala-kala kamar su: Lady Care da Virony da Always da Molped da 7-layer da sauransu.

2. Tissue: Zaki iya amfani da wannan idan al’ada ta same ki a waje, ko kuma bakya ɗiga da yawa, amma ba ta ɗaya daga cikin audugar mata da take da kyan amfani. Ita amfanin ta yafi zuwa idan audugar ki ta ƙare, to sai ki yi amfani da shi.

3. Tsumma: Shi ma amfanin su ɗaya da audugar mata, amma shi wannan zaki wanke shi ne duk sanda kika cire shi.

Hanyoyin Da Zaki Bi Wajen Tsaftace Jikinki Idan Kina Al’ada

Idan kina amfani da pad ne, to duk bayan awa shida (6) zuwa takwas (8) ki tabbata kin cire, kin saka wani, idan kuma kina zuba da yawa, to ki dunga cirewa da zarar kin ji ta jiƙe.

Masu amfani da tsumma kuma, su dunga wankewa, basai sun jira ya jiƙe ba, don da zarar kin jira ya jiƙe, zai iya ɓata ki, kuma abinda ake gudu kenan.

Tissue kuma bashi da tsayayyen lokaci, tunda shi kamar na agaji ne, zaki iya cire shi duk sanda kika so, ko kike buƙata, amma ki tabbatar bai jiƙe sosai ba.

Zaki iya amfani da miski ko turare wanda zaki shafa a jikinki, don kashe ƙarni.

Wanke hannu a duk lokacin da zaki canza, ko bayan kin canza na da matuƙar muhimmanci.

Yadda Zaki Tsaftace Jikin ki Bayan Kin Gama Al’ada

Wanke hannu da sabulu mai ƙamshi ko kuma wanka da su turaren wanka.

Yin wankan tsarki

Ki sa miski a auduga sai kisa a pant ɗinki da sauransu.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Yin Wankan Tsarki Bayan Angama Al’ada danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Ciwon Mara Lokacin Al’ada danna nan.

Don shiga WhatsApp Group ɗinmu na Tsaftar Mata, ku danna nan.

labarin da ya wuceWa ya Kamata In Bayyana Wa Sirrina Idan Na Fara Al’ada
Labarin na GabaKaffarar Azumin Ramadan
Zainab Muhammad
Sunana Zainab Muhammad, nayi karatun firamari a Bennie International School Kano, sannan nayi secondary a Sheik Bashir El-Rayya school complex kano, yanzu ina yin digiri dina a jami'ar Federal University Dutse dake Jigawa, ina mataki na uku.

SHARHI ƊAYA