Turaren wuta ana yin sa ne da itace, domin turara ɗaki, da dukkanin jiki da na tsugunno, da kuma na sutura . Ana zuba shi cikin gaushi (garwashi) ne a kasko. Nan da nan kuwa ka ji ƙamshi ya gauraye ko’ina a cikin gida. Daga cikin Itatuwa da ake turare da su kuwa Sun haɗa da:
Icen Sandal
Ice, Hawi
Icen Gab-Gab
Icen Durot
Da dai Sauransu.
Ana yin turare na soyawa kuma ana yin na jiƙawa. Ya danganta da buƙatar mutum.
Larabawa da kuma mutanen Maiduguri ne suka fi shahara wajen amfani da turaren wuta. Mazansu na taimakawa sosai, su siya wa matansu turare akai-akai. A wajensu tamkar dole ne amfani da turare . Mace ba ta da daraja sai da kasancewa cikin ƙamshi a kodayaushe .
KAYAN TURAREN WUTA
Icen Hawi
Matan Arewa
Farce
Misik
Alhaji Abdullahi
Salamalekum
Sasorabia
20 fragrances
Madara turare ( 8)
YADDA AKE HAƊAWA
Za a sa icen Hawi a turmi a daddaka shi sama-sama. A sa icen gab-gab shima haka. Sai a juye su cikin mazubi. A dauko ruwan turare Matan Arewa a zuba a kan itatuwa. A juye Soyayyen farce. A zuba Misik. Sai a ɗauko turaruka: Alhaji Abdullahi, da salamalekum, da Sasorabia, da 20 fragrances. Kowanne a buɗe a juye. Sai kuma a dauko madarar turare masu matukar ƙamshi a zuba su. A juya da kyau ko’ina ya samu ya haɗe . A samu mazubi a juye a ciki. Kuma a rufe shi sosai.
Littattafai da aka duba:
Taron karawa juna ilmi.
Hikimomin Kulawa da Mai gida.
Mu Koyi Sana’a.
7th Nuwanba, 2015,
Gidan Mumbayya, kano.