A yau za mu koyi yadda ake sakwara a sauƙaƙe.
Sakwara abinci ne da ya samo asali daga doya, doya na ɗaya daga cikin abincin dake gina jiki. Sakwara ta kasance mai daɗi, tana ɗauke da fibre da (starch) a wanda ke ƙarawa jikin ɗan Adam kuzari.
Abubuwan da ake buƙata:
- Doya
- Ruwan zafi
Yadda ake haɗawa
- A fere doya a yanka ta ƙanana, ki zuba ruwa kaɗan blending dinta,
- Idan ta nuƙu sosai a ɗaura ta a kan wuta, tana dahuwa ana juya ta tare da muciya,
- Har sai ta janye ruwan jikin ta, ta yi kamar tuwo, sai a ƙara ruwan zafi kaɗan a kuma tuƙawa.
Domin karanta yadda ake Biredin kwakwa ko yadda ake tuwon masara