A yau za mu koyi yadda ake Plantain Pie. Plantain Pie abinci ne da ake yinsa daga plaintain, yana da matukar amfani a jiki.
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Ayaba
- Ƙwai
- Magi
- Tafarnuwa
- Citta
- Kori
- Attarugu
- Koren tattasai
- Albasa
- Takardar foil
Yadda Ake Haɗawa
- A ɓare ayaba, sannan a silala shi kamar yadda ake yin dambun tsaki.
- Bayan ya nuna, sai a saka a kwano a ɗaɗɗana ta da ludayi.
- A yayyanka albasa da ɗanyen tafarnuwa da citta ƙanana, sannan a daura man gyaɗa a wuta. Idan ya yi zafi, sai a zuba albasa da yankakkiyar tafarnuwa da citta a gauraya su.
- Sannan a zuba yankakken tattasai da da yankakken karas, a yi ta soya su, sai a zuba magi da kori, sannan a ɗauko ƙwai kamar huɗu ko biyar, a fasa a ciki, a yi ta gaurayawa har sai ya soyu sannan a kwashe a ajiye a gefe.
- Sai a wanke hannu a goge, sannan a shafa man gyaɗa a tafin hannu, sannan a mulmula ayabar.
- A shimfiɗe ta a kan takardan ‘foil’ sai a baza ta kamar yadda ake ‘meat pie’.
- Sannan a zuba wannan ƙwan a cikin ta sai a rufe ta da ɗayan gefen.
- A sami cokali mai yatsu a ɗaɗɗana bakin, sai a ɗaura man gyaɗa a wuta bayan ya yi zafi sai a riƙa jefawa, idan ya soyu sai a ajiye a gefe.
- Za a iya cin wannan girkin da shayi a matsayin abin buɗa baki ko karyawa da safe lokacin da ba na azumi ba.
Domin sanin Yadda Ake Mashe danna nan.