Yadda ake plantain chips
To ga yadda ake plantain chips kamar haka dalla dalla:
Abubuwan haɗawa
- Ɗanyar plantain
- Gishiri kaɗan
- Mai
Yadda ake haɗawa
- Ki samu ɗanyar plantain ki yanka ta falan-falan.
Sai ki barbaɗa gishiri kaɗan, ki juya ko’ina ya ji.
- Ki ɗaura mai a kan wuta, in ya ɗan yi zafi, sai ki zuba ki soya, in ya yi, sai ki tsane.