A yau za mu koyi yadda ake onion rings.
Onion rings abinci ne na maƙwalashe wanda ake yin sa daga albasa yana da matukar daɗi musamman ma idan aka haɗa shi da lemo me dan sanyi, ko kuma da shayi mai daɗi.
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Albasa
- Fulawa
- Man gyaɗa
- Garin burodi (Breadcrumbs)
- Yeast
- Baking powder
- Gishiri
Yadda Ake Haɗawa
- A samu albasa mai kyau manya guda biyu ko uku (ko adadin yawan sanwar da za ayi)
- Sai ta ɓare ta, sannan a yayyanka sala-sala (Slices)
- Daga nan sai a yi wara-wara da ita kamar yadda ake warware aworwaro na hannu sannan sai a ajiye a gefe
- Daga nan sai a ɗauko kwano a juye fulawa kamar gwangwani biyu a ciki sai ta ɗauko baking powder a zuba cikin cokali ɗaya
- Sannan a ɗauko Yeast shi ma cikin ƙaramin cokali
- Sai a dauko gishiri a zuba kaɗan, sai a dama a kwaɓin, amma kada ya yi ruwa sosai
- A dinga ɗauko wannan albasar ana tsomawa a cikin kwabin a jujjuya sosai sannan sai a tsame ta a saka a kan wannan garin burodin a jujjuya sosai sai a ajiye
- Sannan sai a ɗauko kaskon suya a ɗora a wuta sai a zuba man gyaɗa, bayan ya ɗan yi zafi sai a dinga ɗauko wannan haɗin albasar ana soyawa ana tsamewa
- Har a gama duka, amma a kula sosai kada suyar ta ƙone.
Domin sanin Yadda Ake Miyar Zogale danna nan.