Abubuwan da ake buƙata
- Gero
- Kanunfari
- Girfa
- Citta
- Sugar
- Ruwa
Yadda ake haɗawa
- Ki samu gero ki sa ruwa ki wanke, sai ki jiƙa ta, kamar na awa biyu
- Sai ki raba shi kashi biyu, kashi ɗaya ki ɗaura ruwa a kan wuta, in ya tafasa, sai ki zuba a kai ki juya. Kashi ɗayan kuma, ki zuba ruwan sanyi akai, sai ki haɗa da ɗayan, ki juya su duka.
- Idan ya yi kaurin da kike so, shi kenan inda buƙatar ƙara ruwa, sai ki ƙara. Sannan ki samu abun tata ki tace, sai ki sa suga.
Ki nemi gora ki ɗura a ciki, sannan ki sa a fridge in ya yi sanyi a sha.
Domin karanta Yadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo danna koren rubutun nan.