Barkan mu da sake kasancewa cikin shirinmu na girka-girken WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu a jikin ɗan Adam cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah. A Yau za mu koyar da yadda ake Haɗin yaji na musamman, ku biyo ni domin mu koya tare.
Yadda ake Haɗin Yaji Na Musamman
Abubuwan da ake buƙata
Barkono
Citta
Kanumfari
Masoro
Kirfa (Cinnamon)
Tafarnuwa
Gyadar miya (Nutmeg)
Ƙuli-ƙuli
Sinadarin Ɗanɗano
Yadda Ake Haɗawa
1. A gyara komai a fitar da datti.
2. A daka komai daban-daban, a tankaɗe su, sai a haɗe su, a zuba sinadarin ɗanɗano a ƙara dakawa har su hade jikinsu.
3. A adana yaji a mazubi mai kyau, mai murfi.
Domin sanin yadda ake dambun nama danna nan