Barkanmu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abinci, namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah.
A yau za mu koyar da yadda ake yin groundnut, rice, sweet potato shake, ku biyo mu a sannu domin mu koya tare.
Ko kun san Gyaɗa na da sinadarin minerals kamar su: copper, manganese, potassium, calcium, iron, magnesium, zinc da kuma selenium wanda suke ƙara ƙarfin ƙashi da haƙori.
Abubuwan Buƙata
- Shinkafa ½ rabin kofi
- Gyaɗa ½ rabin kofi
- Dankalin Hausa
- Gyaɗa soyayyiya
- Siga
- Madara
Yadda ake haɗawa
- A wanke shinkafa a jiƙa ta, sai ta yi laushi
- A fere dankalin Hausa a yayyanka
- A soya gyaɗa a busar da ita
- Sai a hade gyaɗa, dankali da kuma jiƙaƙƙiyar shinkafa a markaɗa a tace da abun tata
- A raba ruwan gyaɗa biyu da aka ɗora a wuta har sai ya yi kauri (kamar kunun gyaɗa). Sai a sauke, a haɗe da ragowar ruwan gyaɗar a saka madara da siga. Za a iya ƙara ruwa daidai ƙaurin da ake so.
- Za a iya tace shi da rariya, idan ya yi gudaji-gudaji, sai a saka a fridge ya yi sanyi.
- Asha lafiya.