Abubuwan hadawa
- Kankana
- Mangoro
- Abarba
- Sugar
- Ruwa
Yadda ake haɗawa
- Da farko sai ki samu kankana, abarba da mangoro ki ɓare su, ki yanka su ƙanana.
- Sannan ki samo blender ki zuba su a ciki, ki sa ruwa Kaɗan,
ki rufe ki niƙa, sai ki tace ki sa sugar
- Ki sa a fridge in ya yi sanyi sai a sha.