KAYAN HAƊI
- Niƙaƙƙen nama
- mai
- Kayan miya
- Tafarnuwa
- Masoro
- Girfa
- Shammar
- Sinadarin ɗanɗano
Yadda za a haɗa
Za a samu tukunya a zuba mai daidai yawan girkin, a sa naman a ciki a soya sama-sama, a zuba mai kaɗan a daka garlic da sauran kayan ƙamshi, a zuba abin ɗanɗano a jefa girfa. Idan ya soyu a ƙara ruwa kaɗan a ciki.
Domin karanta yadda ake Fish – Cakes Danna nan
A gefe kuma a dafa farar macaroni daban, kar ta dafe. Idan ta dahu sama-sama a tace a wanke ta da ruwan sanyi, sai a zuba a cikin tukunyar kayan miya, a sa ludayi a juya a hankali har ta haɗe jikinta, a rufe ta, ta turara kamar minti 3, a sauke.