KAYAN HAƊI
- Nama (niƙaƙƙe) (250g)
- Albasa manya 5
- Attaruhun 2
- Ƙwai 1
- Kayan ƙamshi (ƙarami cokali)
- Tafarnuwa ƙwallo 2
- Tumatur manya 2
- Ganyen lettuce
- Sinadarin ɗanɗano
- Cocumber/ cheese slices (yankakke)
- Roll bread yadda zai ishe ka
A zuba nama a mazubi mai tsafta, a zuba kayan ƙamshi da attaruhu da albasa niƙaƙƙiya da ƙwai da abin ɗanɗano, sai a haɗa a cakuɗa. Sai a dunƙula da ɗan girma, sai a danna shi ya koma ƙasa ya ɗan yi faɗi.
Sai a sa mai a kasko mara kamu, a ɗan shafa mai kaɗan sai a ɗan sa naman a cikin kaskon in wannan ɓarin ya soyu sai a maida ɗaya ɓarin har shi ma ya gasu, sai sauke a ajiye a gefe.
Domin karanta yadda ake Fish – Cakes Danna nan
Sai a ɗauko tumatur 2, albasa 2, cocumber babba guda ɗaya sai a wanke da gishiri a tsane a gefe, a yanka su fale-fale, sai a ɗauko salak a ciccire shi a wanke da gishiri in ya tsane, sai a ɗauki biredi biyu a kifa shi a kaskon da aka gasa naman a gasa shi.
Sama-sama sai a ɗauko biredi a shafa masa man salak, sai a ɗaura salak tumatur ɗaya a sa nama a tsakiya, sai a ɗauko cocumba a sa da albasa, da (cheese slice) guda ɗaya, a ɗora a kan naman a rufe da biredin, haka za a yi wa sauran har a gama da kayan haɗin da sauran biredin har a gama.