YADDA AKE GYARA FARCEN TURAREN WUTA
Farce ɗaya ne daga cikin kayan haɗi ne da ake amfani da shi wajen haɗa turaren wuta da humra da sauran nau’ikan turare.
Dabbace a cikin ruwa ake samu, kuma sai an masa gyara sosai inba haka ba sai ya ɓata ma turare ba, zai ƙamshi mai daɗi ba.
YADDA AKE WANKE FARCEN TURARE
1. Za a zuba farce a tukunya a zuba masa ruwa da omo a ɗora a wuta, sai a bar shi ya tafasa .
Sai a sakko da shi ya huce sarai .
2- Za ka sa hannu a dinga wanke shi za ka ji wani abu a jikinsa kamar nama, har sai ya fice fes.
3- Sai a zubar da ruwan, a zuba sabon ruwa a ci gaba da wankewa. In yai datti a ƙara sake ruwan har sai an ga yai fes.
4- Sai a baza shi a tire(faranti) har ya kwana domin ya bushe sarai.
YADDA AKE SOYA FARCEN TURARE
Za ki samu ƙasa, ki zuba ta a cikin kasko. Ki juye busasshen farcen da kika wanke shi fes.
Ki ɗora a kan wuta ki yi ta soyawa kamar dai suyar gyaɗa.
Idan na turaren wuta ne, in ya yi ja sosai sai ki kwashe shi. In kuma na baƙar humra ce in ya yi ba ki sai ki sauke shi .