Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.
A yau za mu koyar da yadda ake yin gyaɗa marau-marau. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.
Ko kun san gyaɗa mai ɓawo ta fi bayar da kariya daga sinadarin (Aflotoxin), mai sanya cutar daji wato (cancer) a jikin ɗan Adam.
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Gyaɗa mai ɓawo
- Gishiri
- Toka
- Ruwa
- Ƙasar yashi ko toka
Yadda Ake Haɗawa
- A tsince dattin da gyaɗa ko mara kyau sannan a wanke ta fita.
- A zuba gyaɗa da gishiri cikin ruwa a dafa, kamar na munti 5-6. Sai a tace.
- A ɗora tukunya mai zurfi, idan toka ta ɗau zafi sai a saka wannan dafaffiyar gyaɗar a yi ta juyawa har sai ta yi.
- Idan ta yi, sai a juye domin shan iska.
Domin koyar Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri danna koren rubutun nan.