Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Gima Macaroni Jallof su ne:
- Niƙaƙƙen nama/mai
- Kayan miya
- Tafarnuwa
- Masoro
- Girfa
- Shammar
- Abin ɗanɗano
Kayan Aiki
- Murhu/Risho/Gas
- Tukunya
- Kasko
- Mazubi (mai tsafta)
- Ludayi
- Abin daka
- Wuƙa
Yadda Ake Haɗa Macaroni Jallof
Za a samu tukunya a zuba mai daidai yawan girkin, a sa naman a ciki, a soya sama-sama a zuba mai kaɗan a daka garlic da sauran kayan ƙamshi, a zuba abi ɗanɗano a jefa girfa. Idan ya soyu, a ƙara ruwa kaɗan a ciki.
A gefe kuma a dafa farar macaroni daban, kar ta dafe. Idan ta dahu sama-sama, a tace a wanke ta da ruwan sanyi sai a zuba a cikin tukunyar kayan miya, a sa ludayi a juya a hankali, har ta haɗe jikinta
a rufe ta, ta turara kamar minti 3, a sauke
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Macaroni 2 danna nan.
[…] karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Gima Macaroni Jallof danna […]