Yadda Ake Dafaffiyar Gyaɗa

0
1328

Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

A yau za mu koyar da yadda ake yin dafaffiyar gyaɗa. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

Ko kun san dafaffiyar gyaɗa tana da sinadarai masu gina jiki, sannan kuma tana da ƙarancin calories wato kitse fiye da soyayyiyar gyada.

Abubuwan Da Ake Buƙata:

  1. Gyaɗa mai ɓawo
  2. Ruwa

Yadda Ake Haɗawa

  1. A tsince gyaɗa, a gyara ta tsaf.
  2. Sai a zuba ruwa da gyaɗa cikin tukunya mai zurfi a rufe.
  3. A dafa shi na kimanin awa uku (3) sai a tace.

Domin karanta Yadda Ake Gyaɗa Marau-marau ko Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Gyaɗa Marau-marau
Labarin na GabaYadda Ake Hada Grilled Apple Peanut Butter Sandwich