Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, A yau za mu koyi yadda ake chips da sauce na ƙundun kaza. Tare da ni Hafsat Shettimah.
chips na ƙundun kaza na mutune 2-3
Abubuwan haɗawa:
- Dankalin Turawa (peeled and sliced)
- Black pepper (masoro) pinch -optional
- Gizzard (kundun kaza) ½ kg
- Karas manya 2 (sliced)
- Yankakken Koran Tattasai babba 1
- Man gyaɗa
- Albasa jajjagaggiya babba 1
- Attaruhu 5 medium (to taste)
- Maggi (3)
- Garlic tafarnuwa medium Bari 1
- Curry ½ chokali (teaspoon)
- Thyme ½ (teaspoon)
Yadda ake haɗawa
- Ki ɗora kaskonki a wuta, ki sa manki ya yi zafi, sai ki ɗauko dankali kisa ɗan gishiri da black pepper ki juya ki sa a man. Kar ki yawaita juya shi zai fashe.
Idan ya yi, sai ki tsame a matsami. Yayin da man jikin dankalin ya ɗige, sai ki sa a kwano mai kyau, ki ajiye a gefe.
- A tabbatar ƙundun kazar ya wanku da kyau, sai a saka cikin tukunya a zuba maggi guda biyu, curry, thyme, tafarnuwa da rabin albasa a bar ruwan jikin ƙundun ya dafa shi.
- A cikin tukunya mai zurfi za a zuba mai chokali 3-4 a saka tafarnuwa da albasa idan ya soyu, sai a zuba ƙundun kaza shi ma, a soya shi, sai ya yi golden brown, sannan sai a ɗauko attaruhu da maggi 1 da karas, da romon ƙundu (in ƙwai) in kuma babu sai a zuba ruwa ¾ kofi a bar shi na minti 2, sai a zuba Koran Tattasai a sauke.