Yadda Ake Biskit Ɗin Gyaɗa (groundnut cookies)

0
1704

Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah.

A yau zamu koyar da yadda ake yin Biskit ɗin Gyaɗa (groundnut cookies); ku biyoni a sannu domin mu koya tare…

Ko kun san Gyaɗa na rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya wato cardiac disease.

Abubuwan Buƙata

 1. Fulawar gyaɗa ½ kofi
 2. Fulawa 1 cup
 3. Bota ½ cup
 4. Siga ½ rabin kofi
 5. Filebo flavor babban cokali daya
 6. Baƙin hoda Baking powder ½ tablespoon
 7. Bicarbonate soda ½ teaspoon ƙaramin chokali

Yadda Ake Haɗawa

 1. A buga siga da bota sai aukin ya ninku
 2. A saka sauran kayan (fulawa, filebo, baking powder, bicarbonate soda da sauransu). A juya har sai yayi tauri.
 3. A murza da rolling pin sai a saka cookies cutter a yayyanka zuwa shape kala-kala
 4. A gasa cikin abun gashi na minti 15 sai a fito dashi

Domin koyan Yadda Ake Kek Ɗin Gyaɗa (Groundnut Cake) danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Kuli-Kuli
Labarin na GabaYadda Ake Haɗa Lemon Gyaɗa, Shinkafa Da Dankalin Hausa (Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake)