Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na Girke-Girken WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah.
A yau zamu koyar da yadda ake yin Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread); ku biyoni a sannu domin mu koya tare……
Ko kun san Gyada na ɗauke da sinadarin protein wanda ke taimako wurin gina jikin mu.
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Fulawa kofi 3
- Bota ¼ kofi
- Fulawar gyaɗa (Groundnut flour) kofi ɗaya
- Yis (Yeast) ƙaramin cokali 1
- Bakin hoda I (Baking powder)1 rabin ƙaramin cokali
- Ƙwai guda 1
- ½ rabin kofin siga
- ½ rabin ƙaramin cokali na gishiri
Yadda Ake Haɗawa
- A zuba ruwa a kofi, sai a zuba yeast da sugar a juya abarshi kamar minti 3-4.
- A haɗa sauran kayan haɗi (flour, butter, ƙwai, fulawar gyaɗa, gishiri). Kar a manta a chakuɗa sosai.
- A zuba ruwan yis sai a ɗan ƙara ruwan ɗumi a cakuɗa har sai ya haɗe jikinshi. Note:- ya ɗan fi kwaɓin cincin amma karya kai na fanke tsaka-tsaki.
- A sami film ko tsumma mai kyau a rufe a kai shi rana ya tashi sai ayi punching tsakiyar iska ya fita sai abarshi ya ƙara tashina minti uku zuwa huɗu.
- A yayyanka a sakashi a cikin gwangwanin gashi da aka shafa bota da flour. A ƙara barin shi ya tashi.
A saka biredin cikin abun gashi sai yayi golden colour. Temperature 1800c.
Domin sanin yadda ake kek ɗin gyada danna nan