Yadda Ake Alwala

0
49

Alwala asalin ta ibada ce kuma anciro kalmar ne daga asalin sunan ta na harshen larabci (Alwudu’u) wato haske kenan a ma’ana ta harshe,idan kuma ka yiwa harafin (waawun) wasalin fataha (Alwadu’u) ya zama ruwan alwalar kenan,kalmar a larabce an ciro ta ne daga (Addau’u)wato haske. Kamar yadda kalmar tazo cikin Alqur’ani Allah”

Shine wanda ya hore rana ta zamo (Diyaa’i) wato mai haskakawa halitta a cikin yini”,haka kuma kalmar tazo inda Allah yake cewa”adaa at maa haula hum” kalmar (Adaa at) dinnan itama ma’anar ta haskawa ne,duk da cewa kalmar (Addau’u)tana nufin haske mai zafi tamkar hasken rana saboda kalmar tazo tare da rana haka kuma tazo acikin hadisi”assabaru diyaa’un” wato hakuri haske ne ga mai yin sa, duba da hakuri ba kowa ke iya yin sa ba shi yasa hasken sa yazo a kalmar (Diyaa’i)wato haske mai zafi duba da cewa duk lokacin da kake yin hakuri akwai radadi a cikin sa da wahala kafin daga ƙarshe kaci anfanin sa.

Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Raka’atil Fajr danna nan.

A ma’ana ta shari’ah kuma kalmar alwala tana nufin tsarki na ruhi da na jiki daga ƙazantar zunubai kanana da tsaftace jiki domin ganawa da mahalicci,wanda hakan shine shiri na biyu ga duk mai son ganawa da maliccin sa bayan yayi shiri na farko wato tsarkin najasa. Yazo cikin hadisi”masu yin alwala zasu tashi ranar ƙiyama suna masu hasken gabobi saboda alwala”. 


Yadda ake alwala, mutum zai samu ruwa mai tsarki ya wanke hanun sa na dama sau 1 ko sau 2 ko sau 3,haka kuma hanun hagu sannan zai ɗebo ruwa atafin hannun sa na dama ko na hagu idan yana da nakasa ya kurkure bakin sa sau 1ko sau 2 ko sau 3 tare da cuɗawa gwargwadon iko, sannan ya ɗebo ruwa atafin hannun sa ya shaƙa ya face sau 1ko sau 2 ko sau 3, waɗannan sune sunnoni a alwala haka kuma wankewa sau 2 ko sau 3 sunna ce, amma wankewa sau 1wannan farilla ce.

Nan mun samu sunnonin alwala guda 3 ajire yanzu kuma zamu tafi farillai guda 3 ajire,sune kamar haka wanke fuska daga matsirar gashi na goshi zuwa gefen kunnuwa na kumatu zuwa kasan haɗa daf da maƙogoro sau 2 ko sau 2 ko sau 3 sannan wanke tsirtsiyar hannun dama sannan na hagu kowanne sau 1 ko sau 2 ko sau 3.

Domin karanta cikakken bayani akan Nafilolin Sallah danna nan.

Sannan shafar kai da ruwa daga goshi zuwa ƙeya ko daga ƙeya zuwa goshi sau 1 kacal idan daga goshi ne aka faro ana iya dawowa da shafar zuwa goshin haka kuma idan daga ƙeya aka faro ana iya mayar da shafar ƙeyar.waɗannan ukun ajere su ake kira farillai kamar yadda bayani ya gabata.sannan shafar kunne idan mai alwala bai haɗe kunnuwa a cikin shafar kai ba sai ya shafe su dabam, sannan wanke ƙafafu za afara wanke ƙafar dama daga idon sawu dunduniya tafin ƙafa har zuwa yatsun ƙafar tare da cuɗa su,ga wanda bai saka safa ba ko hufi ko sau ciki irin na masu ɗamara.

Idan ya saka ɗaya daga cikin waɗannan kuma yayi alwala kafin ya saka sai ya shafi saman hufin ko safar ko takalmin matsawar bai kwaɓe ba.akwai ƙarin bayani akai idan munzo abubuwan dake warware alwala.sannan ya kalli sama ba tare da ya ɗaga ɗan yatsa ba yacce”na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad manzo sa ne na Allah.

Allah ka sanya ni daga cikin masu yawan tuba ka sanya ni daga cikin masu yawan tsarki”iya nan ma ya isa idan yaso ba sai ya ƙarasa ragowar ba kamar”kasanya ni daga cikin bayin ka masu nagarta”.akowacce gaɓa da ya wanke ƙananan zunubai na fita lokacin da yake wankewan ko kuma tare da ɗigon ruwan ƙarshe, sannan kuma ita wannan addu’ar da yayi ana buɗe masa ƙofofin Aljanna guda takwas da zai mutu a lokacin sai ta wacce yaga dama zai shiga.

Domin karanta Jan Hankali Game Da Sallar Asuba Danna nan 

labarin da ya wuceYadda ‘Yan Mata Ya Kamata Su Kula Da Jikinsu Daga Lokacin Balaga
Labarin na GabaYadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da BismillAh A Cikin Sallah
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.