Addu’ar Bushewar Zuciya – Wannan addu’ar ma akan karanta ta domin Ubangiji ya ba ka kariya daga dukkan cututtukan zamani da kuma bushewar zuciya.
Muddin za ka yi wannan addu’ar Bushewar Zuciya; Allah (Subahanahu Wata’ala) ba zai bari ka shiga cikin wani hali na ƙunci a cikin rayuwarka ba, kuma zai tsare ka daga dukkan cututtuka na zamani wanda aka sani da kuma wanda ba a sani ba.
Ga addu’ar kamar haka:
“Allahumma inni a’uzhubika minal ajzi, wal kasali wal jubni, wal bukhli, wal harami; wal gaflati, wal qaswati, wal ilati, waz zillati, wal maskanati; wa a’uzhubika minal faqari, wal kufri; wal fusuqa, wash shiqaq, wan nifaq, was sum’ati, war riya’a, wa a’uzhubika minas sumami; wal bukami, wal jununi, wal jazami, wal barasi wa sayyi’il asqaam”.
Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Aure danna koren rubutu.
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za ki San Kanki Kafin Ki yi Aure danna koren rubutu.