Rubutu
Sumerians su ne suka fara rubutu. Kafin lokacinsu zane kawai mutane suke yi kuma ba ya ba da ma’ana. Saboda haka suka ƙirƙiro rubutu mai haɗe da zane. Sun ƙirƙiro alamomi wanda ake haɗa su da rubutu don ya ba da ma’ana.
Shekara 5500 da suka shige sun assasa wannan tsarin rubutun nasu ana kiransa Cuneiform saboda ana rubutun ne akan ɓangori mai kamar tafin hannun ɗan Adam. An samu dubunnan ɓangori da aka yi rubutun lissafin ‘yan kasuwa, wasu kuma na addu’oi, wasu na dokoki haka nan kuma wasu wasiƙu da sauransu. Harsunan Semitics sun daɗe suna amfani da rubutun Cuneiform har shekaru wurin 4000 sannan suka koma na Phonetics.
Rubutu ya bayyana a lokuta daban ba tare da wata ƙasar ta san abin da wata ta ke yi ba a ƙasashen da suka waye wato Mesopatamia, da Egypt, da China da kuma America (ta tsakiya) (McGregor p.94). Rubutu shi ne ya fara tabbatar da tarihi a dalilin haka wasu masana suke ganin babu tarihi (wato sai pre-history) kafin a fara rubutu (Haugen 2009: 44). Kuma yawanci abubuwan da aka samu a tarihin wannan ƙasashe da suka waye an samo su ne daga rubutun mutanen ƙasar ko na maƙwabtansu.
Masana suna ganin cewa babu abun da ya kai rubutu muhimmanci a Wayewar Ɗan Adam in ji Professor John Searle, (Professor na falsafa a University of California). Dalili kuwa shi ne rubutu ya fi magana, yana nuna zurfin tunanin ɗan Adam, misali ba za a iya bayanin zurfin lissafi (complex mathematics) ko falsafa da baki ba dole sai an rubuta. Kuma rubutu ba kawai don ajiya (documentation) yake da amfani ba,har ma a sha’anin ƙirƙira, idan mutum ya yi rubutu ba kawai labari yake tabbatarwa ba har ƙirƙiro kuɗi, ma’ikatu, hukuma duk ana ƙirƙiro su ne da rubutu.
Ƙasa tana girma da mutane masu yawa, ba kamar zaman ƙauye ba dole ne a yi rubutu saboda tafiyar da mulki. Mahukunta sun fahimci ba ƙarfin soja ne kaɗai zai tabbatar da mulki ba, idan ana buƙatar mallakar mutane dole ne a rubuta abubuwa ba a yi mulki da ka ba. Rubutu ba labari ba ne ko waƙa ko tarihi wannan shi ake cewa Literature. Kuma ita Literature ba za a yi riƙe ta a ka ba sai an rubuta za a iya waƙe ta. Saboda haka rubutun farko a Mesopotamia ya shafi ƙididdiga (record keeping), ƙirgar wake, da kuma giya (McGregor 91-94).
Rubutu yana ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa ake ganin cewa a Mesopotamia (Sumeria) ɗan Adam ya fara wayewa. An samu ɓangorin da aka yi rubutu a jikinsa wanda ya fi kowanne daɗewa, a kudancin Iraqi, an yi rubutu a kansa sama da shekara 5000 kuma girmansa ya kasance centimeter tara a tsaho da kuma centimeter bakwai a faɗi. Wannan shahararren ɓangori na ƙididdigar giya wadda a wannan lokaci ita ce kamar kuɗin ƙasar. Akwai irin wannan ɓangorai 130,000 a gidan ajiye kayan tarihi na Britaniya (British Museum) (McGregor 91).
Lokaci
Mutanen Mesopotamia sun fi kowa shahara akan ƙirƙiro lokaci wanda lokacin Babylonians aka ƙirƙiro kwanaki bakwai da ake amfani da su yanzu a yawancin duniya. Shuwagabannin addininsu lokacin Sumerians suka ƙirƙiro wannan ilmin na lissafin lokuta da shi suke amfani don sanar da manoma lokacin yin shuka. Sumerians su ne suka fara dogon gini da ake kira Ziggurat a chan sama, a wannan gini suna duba taurari kuma suna bautar wata.
Shuwagabannin addininsu su ne suke kula da Ziggurat a chan sama suke yi wa mabuƙata addu’oi. Mutanen ƙasar sun ci gaba ta kulawa da waɗannan wuraren ibada da kuma duba taurari. Kuma har yanzu ana ganin ɓurɓushin ginin a wasu wuraren.
Lokacin da Babylonians suke mulki Saboda ilminsu na taurari suka fara binciken yanayin sararin samaniya suka gano wasu taurari (Planets) da suka fita daban da sauran a tsarin yadda suke. Taurarin da suka gano guda biyar ne, sannan kuma ga rana ga wata sai suka yi amfani da wannan ilmi suka ƙirƙiro kwanakin mako guda bakwai.
Ranar farko ta wata ce wato Litinin kuma su a wurinsu ita ce Monday ranar “Moon” kenan. Sauran ranakun duk sunayen taurarin suka ba su sai ranar ta ƙarshe suka ba ta sunan Rana wato “Sun” ita ce Sunday da turanci. Mutanen duniya da yawa yanzu suna amfanin da wannan sunaye ranakun da harshensu misali a Italia da Faransa. Amma a ƙasashen Musulmi an canja musu suna amma dai har yanzu kwana bakwai ake amfani da su.
ASTROLOGY MAGIC Annabi Ibrahim (alaihi salam) an haife shi a ƙasar Ur ta Chaldea wadda ita ma ƙasar Babylonian ce. Kuma an kawo ƙissarsa a cikin Alkur’ani inda ya yi muhawara da masu ilmin turari.
Danna nan don karanta Wayewa Da cigaba A Mesopotamia
Edita; Rumasa’u M. Kallamu