khairatu.shehu
Akwai wasu alamomi da ake iya gane masu shan ƙwayoyi. Wasu daga cikinsu sun haɗa da:
- Yawan tara kwalaben maganin mura da tari ko sirinji
- Allura ko kuma yankakkun takardu
- Yawan kunna turaren (ƙamshi) wuta a cikin ɗakin matasa
- Ƙin shiga cikin mutane, musamman a gida
- Yawan ƙamshin turare iri daban-daban don kawar da warin da yake tare da su
- Rashin ƙoƙari a makaranta (amma wata sa’a kuma an ce wai ƙoƙari suke sa wa)
- Yawan ladabi da gaishe da mutane (wanda ba a saba gani a da ba, ko kuma ana yi amma lokaci ɗaya a ga abin ya ƙaru)
- Lokaci ɗaya yarinya ta sauya ƙawaye, ba ta kuma damu da ƙawayenta na da ba, sannan yanayin harkokinta su sauya
- Rashin dawowa gida da wuri da daddare (don shaye- shayen miyagun ƙwayoyin an fi yin su daga yamma zuwa dare)
- Sauyin halaye da ɗabi’un yarinya waɗanda ba a saba da ganin ta tana yi ba
- Yawan sa baƙin tabarau
- Yawan son tafiya wajen biki, a je kuma a daɗe ba a dawo ba
- Sauyawar yanayin bakin matashiya, a dinga ganin ta tana nuna wani launi daban a leɓe ko kan harshe
- Sauyawar ƙwayar ido ta koma ja, idon yana iya ɗaukar fiye awa biyar bai koma daidai yadda yake kafin a sha ƙwayar ba, ko kuma idon ya dinga rawa, kamar ƙwalla ko kuma ana rufe shi ana buɗewa
- Karkatar da kai ko kaɗa kai, musamman ga masu shan hodar Iblis (cocaine)
- Lokacin da ake magana da matashi ko matashiya a ji suna sambatu marasa kan gado
- Yawan yin tamɓele a maganganunsu
- Zazzare idanuwa haka kawai, wanda suke kira ‘cin magani’
- Yawan fushi ko ɗacin rai
- Neman faɗa babu dalili
- Yawan barci.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.
Danna nan don karanta Matsalolin Da ‘Yan Maye Suke Cin Karo Da Su
Edita@rumasau-kallamu