Wa Ya Kashe Husaini (Radiyallahu Anhu)?

0
38

Shin Ahlussunna ne suka kashe Husaini (Radiyallahu Anhu)? Ko Mu’awiyya ne? Ko Yazidu ne?

Amsar wannan tambayar ba ta buƙatar dogon bayani, saboda shi da kansa Husaini (Radiyallahu Anhu) ya ba da amsar wannan tambaya; haka nan ma Aliyu ɗan Husaini (Radiyallahu Anhu) wato Zainul Abidina da Ummukulsum ‘yar sayyidina Au (Radiyallahu Anhu) wato ƙanwar Husaini waɗanda a gabansu komai ya faru; sannan kuma akwai waɗansu manyan malaman shi’a cikinsu har da masu muƙaman ayoyi duk sun ba da amsar wannan tambaya.

Dukkansu bakinsu ya zo ɗaya a kan cewa ‘yan shi’a ne suka kashe Husaini! Ga maganganunsu daga amintattun littatafansu babu ƙari babu ragi.

1-Maganar Husaini (Radiyallahu Anhu)

Imam Husaini (Radiyallahu Anhu) ya tabbatar da cewa waɗannan ‘yan shi’ar da suka gayyato shi sun yaudare shi sun warware mubaya’ar da suka yi masa, sun koma bayan rundunar da suka zo domin yaƙarsa sai ya ce: “Idan kuma kun ƙi (mara baya, kun saɓa alƙawari, kun warware mubaya’a da kuka yi min, na rantse ba wannan ne farau ba a cikin mugwayen ayyukanku.

Irin haka kuka yi wa baba na da ɗan uwana, da dan Baffa na Muslim, haƙiƙa duk wanda ya yarda da ku ya yaudari kansa”. Kuma tun da farko shi da kansa ya ɗan yi tababa dangane da yawan wasiƙun da suka aiko masa ya sha jinin jikinsa inda ya ce: “Haƙiƙa waɗannan suna tsorata ni, ga kuma wasiƙun mutanen Kufa, kuma ina jin kashe ni za su yi”.

Kuma ya yi addu’a ya ce:

“ya Allah ka shiga tsakanin mu da mutanen da suka gayyato mu domin su taimake mu, amma suka zo suka karkashe mu”. A ƙarshe dai Imam Husaini (Radiyallahu Anhu) ya yi musu baki, ya yi musu baƙar addu’a inda ya ce: “Ya Allah in ka raya su ka rarraba kawunan su, ka tarwatsa su ƙungiya-ƙungiya, kada ka sa shugabanni su yarda da su har abada, saboda sun gayyato mu domin su taimake mu, amma kuma sai suka afka mana da kisa”. Waɗannan kaɗan ne daga ikrari da Imam Husaini ya yi kan bayanin waɗanda suka kashe shi.

2-Maganar Zainul Abidin (Radiyallahu Anhu)

Shi Aliyu ɗan Husaini (Radiyallahu Anhu) ne, yana daga cikin waɗanda suka kuɓuta daga cikin iyalan Husaini (Radiyallahu Anhuma) a Karbala saboda shi ganau ne ba jiyau ba, ga abinda ya faɗa:

“Ya ku mutane (Mutanen Kufa) ina haɗa ku da Allah shin ba ku ne kuka rubutawa mahaifi na wasiƙu ba, amma kuka yaudare shi, kuka yi alƙawarin yi masa mubaya’a da biyayya amma kuka yaƙe shi kuka tozarta shi, Allah wadaranku, tur da tunaninku, shin da wane ido za ku yi tozali da ma’aikin Allah ranar lahira idan ya ce da ku shi ne kuka kashe iyalansa, kuka keta alfarma ta?”

Sai mata suka ɓarke da kuka, su kuwa mazajen suka rinƙa zagin junansu suke cewa: “kun halaka ba ku sani ba”.

Shi kuma (Zainul Abidin) sai ya ce: “Allah ya yi rahama ga duk wanda zai karɓi nasiha ta, ya yi aiki da wasiyya ta akan Allah da manzonsa da iyalansa saboda mu masu koyi ne da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam).

Gaba ɗayansu sai suka ce:

“Mun yi alƙawari za mu bi duk umarnin da ka ba mu, za mu tsare ka, za mu bi duk umarnin da ka faɗa Za mu yaƙi wanda ka yaƙa, mu yi shiri da wanda ka yi shiri da shi. Sai mun kamo Yazidu, mun yi bara’a da waɗanda suka zalunce ka, suka zalunce mu”. Sai ya ce da su:

“Haba mayaudara, makirai, ai wannan ihu ne bayan hari, son zuciyarku ba zai bar ku ku iya aikata hakan ba. Wato so kuke ku yi min irin yadda kuka yi wa babana? Wallahi ba za ta yiwu ba jiya jiya kuka kashe mahaifina a cikin iyalansa, alhali zuciya ta ba ta rabu da baƙin cikin rabuwa da shi ba, da rabuwa da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da ‘yan uwa na ba.

A lokacin da Zainul Abidin (Radiyallahu Anhu) yake wucewa sai ya ga ‘yan shi’ar Kufa suna ta kururuwa da koke-koke sai ya dube su cikin murya rarrauna ya daka musu tsawa ya ce: “Kuna wani koke-koke wai saboda mu, to su wane ne suka kashe mu in ba ku ba?”

3-Maganar Ummu Kulsum ‘Yar Ali (Radiyallahu Anha)

Ƙanwa ce ga Husaini (Radiyallahu Anhuma) ita ma ganau ce ba jiyau ba, ga huɗubar da ta yi ga ‘yan shi’ar Kufa:

“Bayan haka, ya ku mutanen Kufa ya ku maha’inta mayaudara, makirai, kada Allah ya tsayar da hawayenku, kada Allah ya kawar da kukanku. Ku dai kun yi kama da mahaukaciyar nan da take yini tana saƙa, sai kuma ta zo ta tsittsinka abinda ta saƙa gutsun-gutsun.

Kuma rantsuwa don kawai biyan buƙatunku. Babu abinda kuka iya sai girman kai da jiji-da-kai da gaba, da mugunta da ƙarya, ga kwaɗayi irin na kuyangi, da tsanin riƙo da gaba, aikinku ya munana Allah ya yi fushi da ku, kuma za ku dawwama a cikin wuta.

Kuna wani kuka saboda an kashe ɗan uwa na? Za ku yi kuka mai yawa, za ku yi dariya kaɗan, kun yi abin faɗar da ba zai rabu da ku ba, ba kuma za ku ga sauƙinsa ba har abada, shi ne kuka kashe ɗan cikamakon annabawa, wanda ya fito daga tsantson tushen manzanci, shugaban samarin Aljanna, wanda kuke fakewa da shi in ana yaƙi, wanda shi ne gatanku, tir da aikinku, zunubin ku ya munana ranar ƙiyama, kun shiga uku kun lalace kun yi asara kun gamu da fushin Allah, za ku gamu da ƙasƙanci da wulaƙanci.

Ko kun san yadda kuka ɓatawa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) rai?
Ko kun san girman alƙawarin da kuka karya?
Ko kun san matsayin alfamar da kuka keta?
Ko kun san darajar jinin da kuka zubar?
Haƙiƙa kun yi taɓargazar da ta kusa sanya sammai su kece, ƙasa ta tsage, duwatsu su rumurmushe”

4-Maganar Zainab ‘Yar Ali (Radiyallahu Anha)

Ita ma ‘ya ce ga sayyaydi Ali (Radiyallahu Anhu) kuma tana cikin ‘yan kaɗan da suka tsira daga kisa ranar Karbala. A lokacin da suke wucewa a kan raƙuma sai ta ji mata suna ta karuruwa sai ta leƙo daga darbuka (rumfar da ake yi akan raƙumi) ta yi tsaki tace:

“ku mutanen Kufa, mazajenku suna kashe mu, matanku suna yi mana kuka, sai ranar sakamako Allah zai yi hukunci tsakanin mu da ku”

Ya ɗan uwa mai karatu, ka ji maganganun waɗanda abin ya faru akan su, yanzu kuma ga maganganun manya-manyan malaman shi’a da kuma sunayen litattafan da suka yi bayani ƙarara cewa ‘yan shi’a su ne suka kashe Husaini.

Wani abin lura shi ne waɗannan malamai ‘yan zamani ne waɗansu suna nan da ransu, Waɗansu kuma ba wani daɗe wa suka yi da mutuwa ba.

Kazim Al-Ihsa’i Annajfi

Ya ce: “waɗanda suka yaƙi Husaini su dubu ɗari uku ne, dukkaninsu ‘yan Kufa ne, babu mutumin Sham a cikinsu, babu mutumin Hijaz, babu mutumin Indiya ko Fakistan ko Sudan ko Misra ko Afrika, ƙabilu ne daban-daban daga Kufa”

Ayatullahil Uzma Muhsinul Amin

Ya ce: “Sai kuma mutane dubu ashirin daga Iraki suka yi wa Husaini (Radiyallahu Anhu) mubaya’a, amma suka yaudare shi suka kashe shi”

Husaini Karani

Ya ce: “Su mutanen Kufa, ba wai tarwatsewa kawai suka yi daga bayan Husaini ba, a a saboda tsabar munafurcinsu sai suka rinƙa gaggawar zuwa Karbala suna ba da sunayensu domin a sa a cikin sojoji masu yaƙar Husaini don kawai su farantawa shaiɗan rai.

Misali akwai wani mai suna Amr binul Hajjaj wanda ya rinƙa nuna goyon bayansa ga Husaini da kare alfarmar Ahlul Baiti har ma ya haɗa runduna domin ya kare Hani ɗan Urwah, amma sai ga shi ya canja yana kiran Husaini da sunan ɗan tawaye yana ma cewa da jama’arsa: “Ku yaƙi wanda ya fice daga addini ya rabu da jama’a”!

Wani misali na irin wannan munafurci shi ne Abdullahi Ibn Hauzah Attamimi wanda mutumin Kufa ne, ɗan shi’a ne tun zamanin sayyidina Ali, ta yiwu ma yana daga cikin waɗanda suka rubutawa Husaini wasiƙar gayyata, amma sai ga shi ya tsaya a gaban rundunar Husaini (Radiyallahu Anhu) yana cewa: “Ya Husaini ina yi maka bushara da wuta” Subhanallah! Wa iyazubillah!

To ɗan uwa ka ji yadda gaskiyar magana take, amma kuma daga baya su waɗannan mutane sai suka dawo suna koke-koke suna zage-zage da tsine-tsine suna jifan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba da laifinsu.

Domin karanta cikakken bayani akan Allah Ta’Ala Ya Yi Maganin Makasa Husaini (Radiyallahu Anhu) danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceIƙirarin Simpanci
Labarin na GabaGudunmawar Mawadata Da Ɗaiɗaikun Jama’a Ga Tsangayu