Waƙar Bikin Ƙaddamar Da Manhajar WikiHausa

0
38

TAKARDA WADDA AKA GABATAR A WAJEN BIKIN ƘADDAMAR DA MANHAJAR WIKIHAUSA, RANAR ASABAR 19 GA OKTOBA, 2024, A ƊAKIN TARO NA GIDAN TARIHI NA MALLAM AMINU KANO (MAMBAYYA HOUSE) DA KE GWAMMAJA, KANO

Assalamu alai gare ku,
Amsuwar ku da bakunanku,
Don ku samu abin riƙewa.

Ya Ilahu ka ƙara tsira,
Gun Rasulu da bai da kyara,
Har da alu jini na baiwa.

Sa sahabbai ‘yan aminci,
Bin su ne fa cika ta ‘yanci,
Har mazowa ran tuƙewa.

‘Yan’uwa na tsara waƙa,
Don maraba a wanga harka,
Gun bikin haɓakar ga nawa.

WikiHausa ta kikkira mu,
Yau da safe ta ce mu zo mu,
Ga mu mun zo ba musawa.

Manhaja kundin bayani,
Ko ka ce rumbun tunani,
Don a yaɗa ilim ga kowa.

Har na Hausa da Dini namu,
Ko kwa al’adar gidanmu,
Wadda ba ta faɗa da kowa.

In kana son gane harshe,
Tun a tsini har da tushe,
Ga fa Wiki tai sanarwa.

Har a Indiya an jiyo mu,
Ko Amurka da Chana, Jamu,
Har garin Manzo na kowa.

Je ka Ingila ko kwa Chadi,
Kun sani ba ma fasadi,
Mu nufin mu a ceci kowa.

Ga saraki gida na girma,
Sun halarto babu ƙyama,
Gaisuwar ku nake taɓawa.

Ga furofesas da dama,
Har da daktoci na girma,
Sun halarci bikin yabawa.

Ga fa Imam har da ɗalib,
Har da yaran ‘J’ fa ɗalib,
Ga marubbuta na kowa.

Yau fa murna ce a raina,
Ga mutan Zazzau gaba na,
Har na Barno suna jiyowa.

Hausa ce kundi na hairi,
Ce tsare tsara da tsari,
Tsattsakin tsaka ba tsirarwa.

In kana son gane harshe,
Babu wasa zo ka lasa,
Yau fa Hausa nake taɓawa.

Godiya gun malamaina,
Ambaton ku yana a raina,
Ga tsironku ana jiyowa.

In kuna neman bayani,
Mai karatun nan ku ji ni,
Ce Nayaya maso ga kowa.

Can fa Yobe Jiha mahaifa,
Nan Kano girma da tsufa,
Ran kushewa ban sanarwa.

Baituka ashirin na tsara,
Layuka uku duk na jera,
Wassalamu nake wa kowa.

Ibrahim Baba Ibn Garba Nayaya
Shugaban Sashen Hausa, WikiHausa
Nguru Writers’ Association of Nigeria (NWAN)
National Teachers Institute, Kaduna.
+2347066366586, +2348125351695
ibrahimba182@gmail.com

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceRayuwar ‘Ƴa Mace A Ƙasashen Turai Da Kuma A Musulunci
Labarin na GabaAzumi