Fitar Da Ruwa A Gaban Mace (VAGINAL DISCHARGE)

0
2465

VAGINAL DISCHARGE: a taƙaice ita ce fitar da ruwa a gaban mace shi ake kira vaginal discharge. Abin da ya kamata mu sani shi ne ba kowane irin fitar da ruwa a gaba ne infection ba.

LAUNUKAN RUWAN DA YAKE FITA  A GABAN MACE

Akwai launuka daban daban waɗanda a dalilinsu ne ma ake iya rarrabe nau’o’in ruwan da ke da matsala da kuma mara matsala, ga su kamar haka :

1- White discharge (Vaginal Lubrication) : Akan sami dan farin ruwa kaɗan yana fita a gaban mace, dab da fara al’ada wannan ba matsala ba ce.

– Tsinkakken farin ruwa mara ƙaiƙayi da yake fita a gaban mace yana da amfani na tsaftace gaban mance da tabbatar da lafiyar gabar mace a kowanne lokaci.

Yadda halittun gaban mace take kullum iya ƙoƙarin kawar da matattun ƙwayoyin jiki da sauran ƙwayoyin cuta da ke kwance a gabanta ko bakin mahaifa shi yasa ma cikin gaban mace ba buƙatar dole dole a an saka sabulu an wanke shi.

2- Thick White : Farin ruwa mai yauƙi da kauri kamar majina mafi yawa ana ganin wannan bayan Al’ada da kwana 6 zuwa 10  wannan yana nuni ne da cewa lokacin Ovulation ne (Lokocin da mace ta gama ƙyenkyashe ƙwai) shi ma ba wata matsala ba ce.

3- Blushed deep pink: a likitance mance idan tagama Al’ada , kamar yadda muka yi bayani a sama gaban mace tana tsaftace kanta , shi ne dalilin ganin wannan pink discharge bayan gama al’ada.

Kuma masu sabon ciki sukan yi wannan pink discharge alama ce ta ciki shi ma ba matsala ba ce.

Sannan yana da kyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

Kuma wani lokoci pink Vaginal discharge zai iya zama matsala idan ya zo da alamomi kamar haka :

1- Ƙarni

2- Ƙaiƙayi

3- Tsananin ciwon ciki.

4- Yellow – Green :  Wannan shi ma wani lokocin yakan faru ta dalilin matsalar abinci ko ƙarancin wassu daga cikin sinadaran vitamin.

Shima idan yazo da alamomi kamar :

ƘaiƘayi 

Ƙarni 

Ciwon ciki 

Ya kamata a ga likita kai tsaye domin matsala ce.

5- Gray or dark discharge: wannan kai tsaye matsala ce wanda ƙwayar cutar bakteria take haifarwa tana zuwa da alamomi kamar haka :

Ƙaiƙayi

Ciwon ciki

Ƙarni

Zafi 

Yana da kyau ku karanta Jan Hankali Ga Masu Cin Smoked Fish (Bandar Kifi)

ME YAKE KAWO INFECTION NA MATA

1- Bacteria Vaginosis : wannan wani ƙwayar cuta ce da ke rayuwa  cikin farji takan haddasa matsalar Sanyin mata.

2- Candidiasis : wannan wata ƙwayar cuta ce Wadda take haddasa Sanyin Gaba. Waɗannan ƙwayoyin cutar suna zama cikin farji kuma ba su cika cutarwa ba, waɗannan ƙwayoyin cutar suna son waje mai gumi domin su girma da kuma yaɗuwa.

3- Trichomonas Vaginalis: wannan ita ce wacce take yaɗuwa ta hanyar jima’i. Ita wannan ƙwayar cutar parasite ce take kawo shi .

4- Irritation Vaginitis : ita wannan ana kiranta da Allergic , wassu abubuwan da jikin mutun bai ɗauke su ba, ana samun sa wajen amfani da kamar su condom, sabulu , ko maganin shafawa.

YAYA MACE ZA TA KARE KANTA DAGA KAMUWA DA INFECTION NA MATA

1- Avoid Vaginal Douching : A cikin Farji akwai wassu ƙwayoyin bakteriya waɗanda ba sa cutarwa kuma suna da amfani, amfaninsu shi ne suna taimakawa wajen ba da kariya ga Farji , sai ka ga wassu matan sukan wanke Farji da Sabulu ko detol haka, waɗannan abubuwan da ake amfani wajen wanke farji yakan kashe bakteriya masu amfani na Farji .Sai masu cutarwa su samu damar shiga.  A kiyaye wanke Farji Da Sabulu da kuma waɗansu abubuwa Wanda ba mu san Kansu ba.

Domin karanta bayani a kan Ciwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure) Danna nan 

2- Uses of Underwear : Amfani da wandon pants, wassu matan sukan bar wandonsu ya yi datti, Barin datti ko amfani pant masu datti yakan ba wa ƙwayoyin cuta damar shiga Farji.

A Tsaftace wanduna.

3- Cleaning Faeces : wajen wanke bahaya mafi yawa mata sukan ɗauki ƙwayar cutar da take dubura zuwa Farji, wanda ba sa yi wa dubura illa amma sukan yi wa Farji illah.

 Shawara shi ne a fara wanke Farji kafin a wanke dubura.

4- Sharing of Underwear:  amfani da pants na wasu , ta yiwu wacce kuke amfani da pants ɗaya tana da cutar Sanyi idan kin yi amfani da nata ke ma za ki iya ɗauka.

5- Sexual intercourse : mutum yakan iya ɗaukar wannan cutar lokocin saduwa da namiji shawara ita ce a dinga amfani da Condom lokocin saduwa. Ga wanda suke da tambaya za su yi join Tambaya and answer sai su yi a ciki za a ba su answers A ciki.

Karanta Kadan Daga Cikin Cuttukan Da Ake Dauka Ta Hanyar Saduwa (Jima’i) (Sexually Transmitted Diseases

labarin da ya wuceKaɗan Daga Cikin Cuttukan Da Ake Ɗauka Ta Hanyar Saduwa (Jima’i) (Sexually Transmitted Diseases
Labarin na GabaBAYANI GA MAZA MASU MATSALAR HAIHUWA SANADIYYAR ƘARANCIN MANIYYI [LOW SPERM COUNT]