Tsafi (Metaphysics)

0
20

Tsafi shi ne haɗa waɗansu ‘yan dabaru (siddabaru), domin cutar da wani mutum ko dabba ta haramtacciyar hanya. Karatun tsafi yana ɓangaren “Metaphysics” a Falsafa. Ya wuce ilimin kimiyya (Science), domin shi yana karatun bayan ɗabi’a ne (Beyond the nature), sannan ita kuma kimiyya na karantar halaye ne (nature). Saboda haka, ilimin kimiyya zai gaya maka ilimin halaye, sai shi kuma “Metaphysics”ya gaya maka dalilin da yasa ake iya haɗa siddabaru (tsafi).

Ita kuma kimiyya za ta gaya maka daga Baba sai Mama, amma shi “Metaphysics” yana binciken meye dalilin da yasa daga Baba sai Mama. Don haka kimiyya ba za ta iya karantar da tsafi ba, don haka ta gindaya shi a cikin “Pseudoscience”, domin tabbatar da ilimin tsafi sai a “Philosophy”.

Har ila yau, shi ilimin tsafi, daɗaɗɗen ilimi ne, wanda a tarihin Ɗan-dam da ya samu ci gaba a shekaru dubbai da suka wuce. Mutanen Syria, Egypt, Babylons, Nabataens da Chaldaens su ne suka samu ci gaba a ɓangaren wannan sana’a. Bayan zuwan musulunci an samu waɗansu daga malamai da suka karanci sihiri da tsafi, don su san haƙiƙarsa ta fannin kariya, don  sanin sharri ba don a aikata sharri ba.

Jabir bn Hayyan, wanda babba ne a cikin masana kimiyya (Alchemy), ya karanci tsafi har sai da aka riƙa kiransa da “Chief sorcerer of Islam”. Sannan a Spain an samu irinsu Maslama bn Ahmad Almajiristi da har littafi ya rubuta akan tsafi mai suna “Ghayah” wanda yake tattare da abubuwan mamaki ƙwarai da gaske!

Aikata tsafi haramun ne a addinin musulunci, saboda cutarwar da yake wa mutane kuma ilimi ne da ya  dogara ga wanin Allah a zahiri. Matsafa suna fara iya tasarrufi da ruhinsu kafin su aikata duk abin da suke so. Wanda zai yi tsafi, yana buƙatar ya zama mai iya juya ruhinsa (soul) ta yadda jikinsa ba zai yi tasiri ba a lokacin da yake aikata tsafin.

Tamkar mutumin da yake hawa dogayen gida ne (skyscrapers), idan yana so ya yi gudu ya tsallaka daga wannan gidan zuwa wancan mai tsawon gaske, to dole sai ya cire tsoron da yake ransa kafin ya tsallaka. Rashin haka zai iya sanyawa ya yi karkarwa ya faɗo. Kamar wanda yake tafiya a tsaye akan igiyar da aka ɗaure tsakanin dogayen gini biyu.

Idan mutum ya ji tsoro a lokacin da yake tafiya akan igiyar, to shi kenan sai ya yi karkarwa ya faɗo, amma idan bai ji tsoro ba, to zai iya tasarrufi da jikinsa ya ci gaba da tafiya bai faɗo ba. Irin wannan hanyar ita take sanyawa matsafa suna iya tasarrufi da jikinsu ta hanyar sarrafa ruhinsu gurin faruwar waɗansu abubuwan na ban mamaki. Idan mutum ya ƙware wajen iya tasarrufi da ruhinsa, to a nan zai iya tasarrufi da abubuwa da yawa a cikin halaye.

Masu aikata “sorcery” ba su fiye amfani da wani abu wajen yin tsafinsu ba. Ga wanda ya kalli film ɗin “Marlin” wanda yake iya tasarrufi da idonsa wajen tsafi, to wannan shi ne “sorcery”. Masu “witchcraft” su ne bokaye da suke amfani da waɗansu abubuwan na itatuwa ko dabbobi da suke ganin alaƙarsu wajen aikata wani lamari da ruhinsu a lokacin da suke tsafin.

Irin waɗannan su ne masu cewa a kawo itace kaza ko farar tsuntsuwa wajen aikata wani lamari. Akwai wani littafi, wanda wani mai tsafi, mai ban tsoro da ya ce a jiƙa gawar mutum da man riɗi har tsawon kwana 40 a riƙa yagar naman da ya ragargaje ana ci a lokacin da ake tasarrufi da ruhi, to ta nan mai tsafin duk abin da ya faɗa ya ce zai faru to a kaso 100 za a samu 80 ya faru! Irin waɗannan matsafan malaman musulunci suka ce a kashe su. Saboda hakan ya saɓa da shari’ar musulunci.

Bambancin mai tsafi da mai mu’ujiza ko karama shi ne, shi mai mu’ujiza ko mai karama an san shi da kyawawan halaye (ethics), kuma har lokacin da yake aikata mu’ujizar ko karamar bai daina aikata kyawawan halayen ba. Shi kuma mai tsafi an san shi da munanan ayyuka da kuma aikata waɗansu abubuwan da ake ganin nutsattsen mutum ba zai aikata ba, domin har kisa suna yi akan hanyar tsafinsu.

Abinda yasa waɗansu daga masana tsafi suke yarda da Annabawa shi ne gane cewar hanyar tsafi daban da ta Annabta. Wannan shi ne yasa matsafa suka yarda da Annabi Musa, saboda sun gane cewa hanyarsa daban da tasu. Abin da yasa ingantattun mu’ujizozin Annabi Muhammad (S.A.W) ba su zamo tsafi ba saboda larabawa sun riga sun san shi da kyawawan halaye har suka riƙa kiransa da sunan  “Amintacce”.

Domin karanta yunƙurin Hausantar da kimiyya danna nan

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceTarihin Marigayi Alaramma Suraj Yunus Kudan
Labarin na GabaWaƙar Baƙar Rama (Ta Haruna Uji)