Ga ta nan ga ta nan ku
Gizo ne dai yana son ya ci nama, amma ba shi da shi. Ya rasa yadda zai yi. Sannan ya ce a ransa, “Bari dai in yi wata dabara”. Sai ya sayo goro ya rarraba wa namun daji da tsuntsayen gida. Sai ya fara kai wa kaza, ya ce, “Ga shi, goron wasa ne wanda za a yi a cikin daji, naki ne wannan” .
Sai kaza ta ce, “To. Amma fa kada ka kai wa muzuru”. Sai ya ce, “Haba, me zai sa in kai masa?” Da gizo ya fita, sai ya shiga gidan muzuru, ya kai masa goro. Sai shi ma muzurun ya ce, “To, amma kada ka kai wa kare”. Sai gizo ya ce, “Haba me zai sa in kai masa?”
Da dai gizo ya fita, sai ya shiga gidan kare ya ba shi nasa goron. Kare ya ce, “To, amma fa kada ka kai wa kura”. ‘Gizo ya ce, “Haba me zai sa in kai mata?” Da ya fita, sai ya kai wa kura nata goron. Kura ta ce, “To, amma fa kada ka kai wa Zaki”.
Ya ce, ‘Haba kura, me zai sa in kai wa Zaki?’
Shi ke nan, sai ya kai wa Zaki nasa goron, ya ce, “Ranka ya daɗe. Wani ɗan wasa za a yi na kawo maka goro”. Da Zaki ya karɓa, sai ya ce, “To, Allah ya kai mu”. Shi ke nan. Da ya fita, sai ya shiga ya kai wa damisa. Damisa ta ce, “In ce ko dai ba ka kai wa Sarki Zaki ba?”
Sai Gizo ya ce, ‘Haba, haba. Wane ni da gayyatar Sarki?’ Sai damisa ta ce, ‘To, Allah ya kai mu”.
Da ya fito sai kuma ya shiga gidan giwa ya kai mata nata goron. Sai giwa ta ce, “To, in ce ko baka kai wa manyan dawa ba?’ Ya ce, “Mhm! Yaya zan kai?” Ko kai masa ne ma ai ke zan bai wa ki kai masa “. Shi ke nan. Ana nan ana nan, sai ranar wasa ta zo. Gizo ya bayyana musu wurin da za su haɗu a yi wasan. Ya ce musu, “To, ku tafi zan same ku. Ni daga baya zan taho tare da makaɗa’. Shi ke nan. Sai kaza ta fara tafiya. Ashe ba su sani ba, gizo ya riga su isa can. Sai kaza ta isa can. Gizo ya yi mata maraba. Ya ce,
“Shiga wannan bukkar kafin su zo”.
Shi ke nan. Kaza ta shiga, ta zauna. Daga can sai ga muzuru ya taho. Sai Gizo ya gaya wa muzuru cikin raɗa, ‘Maraba’. Shiga tana nan a ciki’. Shi ke nan sai muzuru ya shiga ya tasar wa kaza zai cinye ta. Ya cinye ta. Can kuma sai ga kare ya taho. Shi ma dai Gizo ya gaya masa kamar yadda ya gaya wa muzuru. Sai shi ma karen ya cinye muzuru.
Daga nan kuma sai ga kura. Ita ma ya gaya mata kamar yadda ya gaya wa kare da muzuru. Sai kura ta shiga ta cinye kare. Kura kuma tana zaune a cikin rumfa. Sai ga Zaki ya taho. shi ma Gizo ya gaya masa haka. Ya shiga ya cinye kura. Daga nan sai ga giwa da damisa sun jero sun taho. Sai Gizo ya ce, “To, ku shiga nan bukkar mana”. Daga shigar su, sai suka kaure da faɗa tun daga cikin rumfar har suka yiwo waje. Idonsu duk ya rufe, suna ta faɗa. Sai Gizo ya samo ganga, ya soma kiɗa yana waƙa:
Zaki bari, damisa bari.
Giwa bari.
Faɗanku na manya,
Wa yake shiga?
Sai wawa, sai mahaukaci.
Sai ko ni da ba ni da hankali.
Suna ta faɗa, can da giwa ta ga abin ba dama, sai ta fito ta yi tafiyarta gida, ta bar zaki da damisa suna karawa. Sai Gizo ya ci gaba da yi musu waƙa. Ya yi ta yi, su kuma suna ta faɗa. Ashe Gizo da ma ya zo da yaji a ƙunshe. Sai ya ɗauko yajin nan ya barbaɗa musu a idanunsu. Sai fa faɗa ya rincaɓe, idanunsu suka rufe ruf. Daga can sai Gizo ya ɗauko wuƙa ya ce, “Yan banza. Ana so a ci nama an rasa yadda za a yi”. Sai ya kama yankan naman jikinsu yana tarawa, har ya kashe su duka. Sai ya jide naman ya kai gida aka soya masa, ya ci ya ƙoshi, ya ajiye sauran, yana ci lokaci-lokaci.
Ƙurunƙus.
Domin karanta Tatsuniyar Ɗankaɗafi danna nan.
Domin karanta Tatsuniyar Gizo Da Giwa danna nan.
Edita:@rumasau-kallamu