Tarihi ana rubuta shi ne ba dan ka yarda ko kar da yarda ba, ana rubuta tarihi ne dan ka ɗau darasi daga abinda ya faru.
SHIMFIƊA:
Kalmar zanga zanga a harshen Hausa tana da m’anoni da dama a turance, amma kalmomin da suka fi dacewa da ita, ita ce Kalmar “protest” da kuma kalmar “Demonstration”. Kalmar “demonstration” ta fi dacewa da zanga zanga saboda a ma’anar “demonstration” shi ne Jama`a su nuna ra’ayinsu bisa tsari da doka dan gwamnati ta canza wani ƙudiri.
Zai iya zama ta hanyar lumana ko ta hanyar tarzoma da rigima, wanda ya ƙunshi tattaki, tarurruka da sauran hanyoyin nuna wata buƙata ko nuna damuwa”
Kalmar “Protest” ita kuma a dunƙule tana nufin zanga zangar lumana; wato nuna rashin amincewa ko rashin yarda ta hanyar yin tarurruka, tattaki da lacca- lacca, amma cikin lumana wanda ya ƙunshi rike alluna da waƙe-waƙe dan jawo hankalin gwamnati kan wani abu mai mahimmnaci.
Daga waɗannan ma`anoni guda biyu da suka gabata, za a iya fahimtar Kalmar zanaga zanga, ta iya zama ta lumana ko akasin haka. Shiyasa duk lokacin da aka ambaci kalmar sai an ɗora ta da wata kalmar dan nuna abinda ake nufi ya fito fili.
Tun ranar 29 ga watan 5 na shekarar 2023 da aka ranstar da shugaban ƙasa Mai girma Ahmed Bola Tinubu ya shelanta cire tallafin mai wanda ya janyo tashin farashin man fetir wanda hakan ya sabbaba tashin sauran kayayyakin masarufi.
Farashin mai ya ci gaba da hauhawa daga naira 300 zuwa naira 720 (a gidajen ƙananan yan kasuwar mai, a yanzu 820 zuwa 850). Daga nan farashin sauran kayan masarufi suka rinƙa hauhawa da tashin gwaron zabi, sakamakon hakan mutane sun faɗa halin ƙa-ƙa-ni -ka-yi da ƙarin wahalar rayuwa da tsanani na yau da kullun. Wannan halin da ake ciki kullum ƙaruwa yake yi babu alamar sauƙi ko sassauci.
Rayuwar talaka ta na ƙara shiga tsanani. A hanu guda kuma talakan wannan kasa yana ganin yadda shugabanni suke sharholiya da dukiyar ƙasa, da kuma taskance ta ga kansu da iyalansu. Alhali abinda ya kamata shi ne talaka ya sami sauƙin rayuwa saboda irin arziƙin da Allah ya yi wa ƙasarsa.
Ba shugaba Tinubu ne ya sabbaba wannan halin da ake ciki ba, ɗorawa ya yi daga inda aka tsaya. Tun daga dawowa mulkin dimokraɗiyya ake ƙara farashin man fetur, wanda yana ɗaya daga cikin abinda talakan wannan ƙasa ya dogara da shi dan gudnanar da akasarin rayuwarsa. Janar Abdussalam ya miƙa mulki ga shugaba Obasanjo farashin man fetir yana Naira 20 kacal a shekarar 1999. Amma bayan shekaru 25 yanzu farashin sa ya kai Naira 720 zuwa 800+ (NNPCL N620)
TARIHIN ZANGA ZANGA
A tsari irin na dimokraɗiyar ƙasashen yamma da muka ɗauko muka yafa, an amince mutane su nuna fushinsu, ko rashin amincewar su, ko nuna wata buƙata ta su ta hanyar fitowa kan tituna da wuraren tarurrukan jama`a dan yin haka. To amma tun da aro wa muka yi muka yafa, ba lallai bane mutanen mu su yi abinda ya dace ko kuma hukumomin mu su yi abinda ake buƙata. Saboda haka ne zamu duba yadda aka gudanar da wasu zanga zanga a wannnan kasar tamu dan ganin ina muka dosa game da abinda ya shafi zanga zangar da ake ta kira da a fito.
ZANGA ZANGAR MATAN ABA 1929
Wannan shi ne zanga zangar farko a tarihin wannan ƙasar. A ranar 6 ga watan 12 na shekarar 1929, mata sama da dubu goma (10,000) daga ƙabilu shida na kudu maso gabashin wannan ƙasar ne suka fito zanga zanga dan nuna fushinsu game da abubuwa uku.
Na farko yadda sarakunan da turawa suka nada suka taƙaita wa mata a dama da su a gwamnati, wanda a al’adar wannan yanki tun tale-tale mata suna da ta cewa a gudanarwa da alamuran jama`a na yau da kullum. Na biyu ƙin amincewa da karin haraji wanda wani mai riƙon ƙwarya na D.O na lardin Bende, mai suna Mr. Cook ya ɗauko hanyar ƙidaya mata da dabbobi da sake duba yadda ake biyan haraji.
Sai mata suka zaci ƙara musu haraji za a yi duk da wanda aka ƙara wa mazajensu a shekaran 1928. Sai na uku, yadda farashin kayan gona ya yi warwas saboda babbar masassarar tattalin arziƙi da duniya ta faɗa ciki a wannan lokacin. Waɗannan dalilai n suka sa mata suka fito dan nuna rashin amincewarsu game da waɗannan matakai, wadda ta fara da zanga zangar lumana daga wani gari mai suna Olokoa a garin Bende wadda ta yaɗu zuwa akasarin yankin kudu maso gasbashin wannan ƙasa.
A ƙarshe, wannan mummunar zanga zangar ta haifar da sace sace, da ƙona kayan gwamnati a wurare kamar Owerri da Kalaba. Mata sama da hamsin da biyar ne suka rasa rayukansu, wasu sama da hamsin suka jikkata. Sannan an sami ‘yar nasara na amince wa mata su shiga a dama da su a gudanar da gwamnati.
ZANGA ZANGAR MATAN ABEKUTA 1946
Sakamakon ƙarin haraji da aka kakabawa wa mata, kungiyar mata ta Abekuta (AWU) wanda ƙungiyace ta ma’aikata da `yankasuwa mata ƙarƙashin jagorancin Funmilayo Ramsone-kuti, a lokacin tana shugaban wata ƙaramar makaranta, da kuma sirikarta Grace Eniola Soyinka. Wannan ƙungiya ta gabatar da ƙorafe-ƙorafenta ga Turawa da kuma Sarkin Abekuta game da nauyin harajin da ka ɗora wa mata da kuma yadda ake gudanar da tsarin shugabanci na Sole Native Authority, duk da korafe korafen, ba abinda ya canza.
A ranar 5 ga watan Oktoba 1946 mata suka taru a fadar Sarkin Abekuta Ladipo Ademola dan nuna damuwarsu da rashin amincewa da waɗancan matakai. Gwamnati ta mayar da martani mai zafi ta hanyar kame, tare da ɗaukan matan da suka taru har da barkonon tsohuwa.
An ci gaba da sa-in-sa har zuwa ranar 10 ga watan Sha biyu, in da aka samu matsaya da ‘yar kwarya kwaryar nasara, kamar sakin matan da aka kame aka kulle, sannan Sarkin Abekuta ya sauka na ɗan wani lokaci cikin wani yanayi da aka yi na yaudara, saboda turawa suna ƙaunarsa. Sannan aka baiwa mata dama a dama da su a cikin harkar gwamnati. Shima harajin da aka dakatar zuwa wani lokaci aka dawo da shi ta wata hanyar.
ZANGA-ZANGAR ƊALIBAN JAMI’O’I 1978
A lokacin mulkin Janar Gawan cikin shekarar 1978 Majalisar ƙoli ta mulkin soji na wannan lokacin ne ta ƙara kudin gurin kwanan dalibai zuwa Naira 90 da kuma kuɗin tikitin cin abinci, aka ƙara kwabo hamsin N50k daga N1.50k zuwa N2.00k. kamar yadda shugaban hukumar kula da Jami`o`i ta Kasa na lokacin wato Parpesa Jibril Aminu da kuma Ministan Ilimi kanal Ahmadu Ali suka fada.
Wannan ƙarin ya janyo dalibai karkashin ƙungiyarsu ta NUNS a wancan lokacin, wanda Segun Okeowo ya jagoranci zama da sauran ɗalibai a Ilori, Maiduguri da Kalaba. Ƙarshe dai dalibai sun yanke su kaurace wa ɗakunan karatu daga ranar 17 ga watan Afrilu, 1978. Amma da ɗaliban suka fahimci gwamnati ta yi biris da buƙatunsu, sai shugaban ya shelanta da jagorantar zanga zanga a jami`ar Lagas wanda hakan ya janyo kashe ɗalibi ɗaya. A jami`ar Ahmadu Bello da ke Zaria kuwa, ɗalibai takwas ne sojoji suka kashe.
Bayan sati guda an gudanar da zanga zangar gama gari na ɗalibai wadda aka fi sani da “Ali Must Go” zanga zangar ta janyo ɓarna mai yawa da ta hada da sace-sace, lalata kayan gwanmati da sauransu, Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin rufe dukkan jami`o`in ƙasar, sannan aka rusa ƙungiyar ɗalibai ta NUNS. Ƙarshe dai gwamnati bata janye ƙarin da ta yi ba, sannan an sallami wasu malaman jami`o`i da kuma ɗalibai har da shugaban ƙungiyar ɗaliban Segun Okeowo wanda ɗalibi ne a jami`ar Lagos duk da a ƙarshe ya yi karatunsa a Jami`ar Awolowo. Amma dai babu dai wata kwakwarar nasara da aka cimma a wannan zanga zangar.
ZANGA ZANGAR RASHIN AMINCEWA DA SHIRIN TSUKE BAKIN ALJIHU 1986
Ɗaliban Jami`o’i, ma`ikata, da waɗanda ma ba ma`aikata ba har da zauna gari banza ne suka kwarara kan titunan kasar nan ranar 24 ga watan biyar na shekarar 1986 bayan da Bankin Duniya mai bada lamuni ya ƙaƙaba wa Najeriya shirin tsuke bakin aljihu (SAP) wanda ya ƙunshi karya darajar naira, ƙara farashin man fetur, ƙara kudin karatu a jami`o`i. Waɗannan abubuwa sun janyo tsadar kayan masarufi.
Kafin a fita wannan zanga zangar ƙungiyar ɗaliban kasar nan sun yi tarrurruka da miƙa wa gwamnati ƙorafe-ƙorafe guda 10 da suke so gwamnati ta aiwatar da su, a ciki har da soke shirin nan na tsuke bakin aljihun gwamnati, amma gwamnati tayi kunnen uwar shegu.
Wannan ya sanya daliban jami’ar Jos da ta Benin suka fita zanga zangar lumana, daga nan zanga zangar ta koma ɓarna, sace-sace da ƙona kadarorin gwamnati. Sakamakon wannan zanga-zangar mutane 2 sun rasa rayukansu a Jami`ar Benin, sannan wasu da yawa sun mutu a manyan birane irinsu Lagos. An kame shugaban ƙungiyar ɗaliban jami`o`i Ghani Fawenhimi da shugaban ƙungiyar ɗalibai ta kasa wato Lukman Salihu Mohammed, sannan aka rufe Jami`o`i goma sha uku. Kamar zanga-zangar da ta gabata Gwamnati bata janye wannan shiri na tsuke bakin aljihu ba.
Shugaban ƙasa na wannan lokacin wato Janar Babangida cewa ya yi babu wani shiri da zai maye gurbinsa. Haka dai aka ƙare ba wani abin a zo a gani bayan zanga zangar.
ZANGA ZANGAR RASHIN AMINCEWA DA SOKE ZAƁEN 1993
Musamman a kudu maso yammacin Najeriya an gudanar da mummunar zanga-zanga bayan rushe da soke zaben da aka gudanar a ranar 12 ga watan shida, na shekarar 1993 wanda ya gudana tsakanin Cif Abiola na Jami`iyyar SDP da Alhaji Bashir Tofa na Jam`iyyar NRC. Duk da ba a kai ga sanar da wanda ya lashe zaɓen ba a hukumance, amma dai an tattara ƙuri`un da ya nuna Cif Abiola na jam`iyayr SDP yana kan gaba da ƙuri`u 8,341,309 wato kashi 58.38 a cikin ɗari, abinda ya bashi damar zarce Bashir Tofa da ya sami ƙuri`a 5, 952,087 wato kaso 41.64 cikin dari.
Ranar 24 ga watan shida, Shugaban ƙasa na wannan lokacin ya sanar da soke zaɓen gaba daya, wanda hakan ya janyo mummunar zanga zanga da ya janyo mutuwar mutane sama da ɗari. `Yan ƙabilar Ibo da suke Legas sun yi ta gudun hijira dan barin ɓangren yarbawa.
An rurrufe gidajen jaridu da rediyo, sannan aka kame `yan jaridu. Gwamnati soji ta wannan lokacin ta hana duk wata kotu karɓan karar duk wani abinda ya shafi soke zaɓen. Duk da wannan zanga-zangar da kuma abinda ya faru, ba abinda ya canza. Ƙarshe ma dai aka damƙe Abiola bayan ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa, har Allah ya karɓi kayansa.
ZANGA ZANGAR RASHIN AMINCEWA DA CIRE TALLAFIN MAI 2012 (OCCUPAY NIGERIA)
A ranar 1 ga watan Janairun shekara 2012 ne shugaban ƙasa na wannan lokacin Jonathan ya shelanta cire tallafin mai da ƙarin farashin da ya kai kashi 120% bisa ɗari akan tsohon farashin na man fetir. Wannan ya janyo ranar 2 ga wannan wata na Janairu aka fito zanga-zanga a biranen Legas, Kano, Abuja, Minna, Gusau da kuma ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Landan, an gudanar da irinta a birnin New York da da sauran manyan biranen ƙasashen duniya.
Musamman a garin Minna ta jihar Neja, matasa sun fito tituna suna ƙone-ƙonen kadarorin gwamnati, motocin jama`a har ma kadarorin wasu manyan mutane a jihar. Wannan zanga-zangar kamar sauran na baya an yi ta`adi mai yawa na kayan al`umma, kadarorin gwamnati, an kuma yi hasarar rayuka goma sha shida (16) daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ita ma wannan zanga-zangar bata haifi wani ɗa mai ido ba, saboda duk buƙatun da aka fito nema ba wanda gwamnati ta aiwatar da shi, ƙarshe dai haka abin ya wuce ba tare da an cimma wani abin a zo a gani ba. Ministan kudi na lokacin Mrs. Ngozi Okonjo-Iweala cewa ta yi idan gwamnati ta janye tallafin mai za ta ajiye aiki.
ZANGA ZANGAR NUNA ƘYAMAR (SARS) ZARATAN (`YANSANDA) NA MUSAMMAN DAN DAƘILE FASHI DA MAKAMI DA SAURAN MUGGAN AYYUKAN LAIFI 2021
Wasu daga cikin jama`a musamman mutanen kudu sun yi ta ƙorafe-ƙorafe kan yadda jami`yan `yansada na musamman wanda aka samar da ita tun shekara 1992 dan daƙile fashi da makami da sauran muggan ayyukan `yan ta`adda da masu sace mutane.
Ana zargin waɗannan zaratan `yansanda da wuce gona da iri da cin zarafin ɗan adam fiye da kima wurin gudanar da ayukansu. Waɗannan zarge-zarge da ƙorafe-ƙorafe sun yi yawa tun daga 2017 har zuwa 2021 musamman ta kafar sadarwa ta tweeter wanda yake ɗauke da alamar #EndSARS.
Wannan kururuwar ya samu karɓuwar mutane sama da miliyan ashirin da takwas a wannan kafa ta sadarwa. Wanda ya janyo zanga-zangar goyon baya a ƙasashen waje da dama dan kawo ƙarshen ayyukan waɗannan `yansanda.
A cikin watan October, 2021 ne aka gudanar da munanan zanga-zanga a jihohi da dama na kudancin wannan ƙasa dan nuna ƙyamar ayyukan waɗannan zaratan `yansandan na musamman. Wasu daga cikin ire iren zargin da ake yi wa waɗannan jami`ai ya yi ta yawo a kafafen sadarwa kamar wanda aka gano wasu jami`an wannan sashe sun harbe wani matashi har lahira sannan suka yi awon gaba da motarsa ƙirar Lexus SUV.
A ranar 8 ga watan Goma 2021 zanga-zanga ta ɓarke a sassa daban daban na kudancin wannan ƙasar. ‘Yansanda sun yi ƙoƙarin tarwatsa wannan zanga-zanga amma abin bai yiwu ba. Ranar 20 ga watan Goma an zargi jami`an soji da kisan masu zanga zanga a Lekki na jihar Legas.
A ranar 11 ga watan 11, 2020 Gwamnati ta sanar da rushe wannan sashe na zaratan jami`an `yansanda. Wannan shi ne babbar nasarar da aka samu biyo bayan wannan zanga-zanga. Amma a gefe guda kuma zanga-zangar da ta janyo hasarar rayuka sama da hamsin (55+) na fararen hula, `Yansanda goma sha daya (11) da kuma jami`an soji bakwai (7).
RUFEWA
Idan muka dubi waɗannan jerin zanga-zangar da aka gudanar a wannan ƙasa tun tale-tale da kuma nasarorin da aka samu, za mu iya cewa daga abinda ya wuce na tarihin zanga-zanga, babu wata ƙwaƙƙwarar nasara da zamu iya cewa an samu sai ma dai hasara ta rayuwa da dukiyoyi da zanga zangar ke haifarwa. A taƙaice, kwalliya dai bata biyan kuɗin sabulu.
Daga abinda ya gabata, wannan zanga-zangar da ake ta kururuwa da kiran mutane su fito, shin tana da wani bambanci da wadda aka yi a baya? Da ga dukkan alamu babu wani bambanci saboda da dalilai masu yawa. Na farko dai shi ne, su waye waɗanda za su shirya wannan zanga-zangar ta yanzu? Misali a baya mun ga ƙungiyar mata da ƙungiyar ɗalibai ne suke kiran zanga-zangar, amma daga ƙarshe sai abin ya fi ƙarfinsu, ɓata-gari suka shiga suka yi aika-aika.
Toh wannan su waye suka shirya ta, kuma su waye jagororinta? Wannan tambaya ce da duk waɗanda suke kira da a fito zanga-zangar ba takamaimen wanda zai bada amsar ta. Rashin wannnan amsar shi zai nuna inda zanga-zangar ta dosa. Wato kowa sarkin kansa ne a zanga-zangar.
Abu na biyu, shin akwai tabbbacin ɓata-gari baza su yi amfani da wannan dama ba dan tada hargitsi da tarzoma? Wannan ma abu ne da babu wanda yake da tabbacin rashin faruwar hakan, musamman a irin wannan yanayi da muke ciki na ƙwarya-ƙwaryar tsaro a wannan yanki namu na Arewa da ma kasa baki ɗaya. Saboda haka akwai matsaloli da ba wanda zai iya tantance su kai tsaye, wanda hakan ya ke nuna rashin yinta zai fi yinta alheri.
A maganar gaskiya, mutanen wannan kasa suna cikin babbar matsala, wahala, takura da matsin rayuwa. Mutane ba sa iya samun abinci, ba sa iya gudanar da rayuwar su kamar yadda ya kamata. Alhali shugabannin siyasa su na cikin daula da walwala, wasu ma har da almubazzaranci. Toh wace hanya za a bi dan nusar da shugabanni halin da talaka ya ke ciki a wannan kasar?
Dole ne shugabannin addini da na al`umma su riƙe mastayinsu na `yan tsakiya tsakanin Shugannin siyasa da kuma al`umma. Talakawa ba su da damar ganin shugabanni kai tsaye, su fada musu halin da suke ciki a sauraresu, amma shugabannin addini da na al`umma musamman sarakuna su ne suke da wata dama ta musamman, ita ce suna da alaƙa da talakawa kai tsaye kuma suna da alaƙa da shugabanni kai tsaye, sun san halin da talakawa suke ciki sannan sun san yadda za su kai kukan talaka a sauresu kuma a dau mataki.
Saboda haka, ya kamata su san wannan sannan kuma su yi abinda ya kamata kafin lokaci ya ƙure musu. Talakwa su zama basa ganin girmansu da darajar su, balle su saurari maganarsu.
Edita: @rumasau-kallamu