Rayuwar Yahaya Tanko A Taƙaice
Wanda Aka Gabatar A Taron Walima Wanda Majalissar Mata Ta Shirya A Ɗakin Taro Na Tsangayar Kimiyya Ta Jami’ar Bayero Ranar Lahadi 27 Ga J/Sani=26 Ga Maris 2017
Ƙuruciya da Aure:
- An haife shi unguwar Bakinruwa ƙaramar hukumar Dala a 1951
- Yayi ƙuruciyarsa rabi a Bakinruwa rabi a unguwar kakanisa yakasai, bayan rasuwar mahaifinsa.
- Ya yi aure a shekarar 1974
Karatu Da Tarbiyya:
- Ya fara samun tarbiyya a hannun mahaifansa.
- Yana da kimanin shekar biyar mahaifinsa ya sa shi a makarantar allo ta Alhaji Malam Isa a unguwar ‘yar kasuwa kan titin kasuwar kurmi zuwa goron dutse.
- Karatun ƙawa’idi a wurin Malam Abdu na unguwar ‘yan muruci.
- Makarantar dare ta Islamiya ta Malam Baba Baƙinruwa.
- Makarantar Ulumiddini ta Alhaji Sunisi Ɗantata a shekarar 1960, a wannan lokacin yana da kimanin shekara takwas ko tara a duniya.
- Makarantar “Judicial School ta Shahunci 1964-1968. A sannan yana da shekara sha 12 a duniya.
- Yayi wta tafiya ta ziyarar ‘yar uwarshi a mina (Jihar Neja) a 1970.
Koyon Sana’a Da Kasuwanci:
- a sanda yake uruciya mahaifiyarsa takan dora masa tallan acma/acamo. A sanda yake “Judicial” mahaifinsa yana koya masa sana’ar gidansu, watau dinkin keke. Bayan rasuwarsa a shekarar 1967, daga shekarar 1968 zuwa shekarar 1970 kwunsa ya sa shi harkar kasuwanci. Ya yi kasuwanci a wani kanti cikin asibitin Murtala. Ya yi kasuwanci a wani kanti a Galadima Road Sabongaroi. Ya kuma yi ciniki a wani dan kanti na katako a cikin lungun kurna a unguwar yakasai. A sanda yake makarantar SAS, mahaifiyarsa takan dora masa dubulan/cincin mai nama daga Bakin ruwa ya kai kantin asibiti.
KARATU:
Ya fara karatun Alkur’ani a makarantar Alhaji Malam Isa, unguwar ‘yar Kasuwa.
Ya fara karatun Ilimin (Ahlari/Kawa’idi) a wurin M Abdu a Unguwar ‘Yan muruci.
Ya fara karatun Islamiyya a a unguwar Koki 1960.
An sa shi a makarantar K Shari’ah ta shahunci 1964-1968.
Yayi karatun Ilimi na a zure a hanin kakansa Malam Abdur Razak, alkalin Ringim.
Ya sauke AlQur’ani a makarantar malam Abdu mai ‘yan makaranta wadda take a Yakasdai.
Ya je Makarantar Nazarin Harshen Larabci (SAS) a 1971.
Yaje Abdullahi Bayero College (Diploma in Arabic Hausa and Islamic Studies) 1975-1978.
Digirin farkao a Bayero University (Hausa Islamic Studies) 1980-1983.
Digiri na biyu a Bayero University (Isalmic Sturdies) 1988-1981.
Kwas na horar da Limamai a jami’ar Al Azhar (Nov-jan) 1994-1995.
Digiri na uku a Bayero University ( Islamic Studies) 2011.
Koyarwa A Makarantun Gwamnati:
- ya fara koyarwa a makarantar firamare ta Dwanau,1974-1975.
- Koyarwa a makarantar koyon harshen Larabci (SAS) , 1978-9179.
- Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta bayar dashi aro domin koyar da IRK a “Federal Governent Coliege Kano” 1979-1980.(sai ya tafi kartu)
- Koyarwa a makarantar mata ta Arabiyya Ɗanbatta 1884-1985
- Koyarwa a Gumel A.T.C (Kano State Higher Institute of Education) 1985-1960
- Koyarwa a “College of Edukation Kumbotso”, wadda a yanzu ake kira “Sa’adatu Rimi College” 1987-1992.
- Koyarwa a “Aminu School Of Islamic Legal Studies” Kano State polytechnic 1999-Febuary 2015.
Koyarwa A Makarantun Islamiyyah:
- Ya koyar a makarantar Islamiyya ta Yola da yamma.
- Ya koyar a makarantar Islamiyya ta dare a unguwar Mai Aduwa.
- Ya buɗe makarantar Iasamiya ta dare a idansa B/R
- Ya koyar a makarantar koyar da matan aure ta dare ta Gumel
- Ya koyar a makarantar koyar da matan aure ta ƙungiyar Da’awa da yamma.
- Ya koyar a makarantar koyar da matan are ta Ƙungiyar Huɗaibiyya
Limanci
- Ya fara yin na’ibin limanci Juma’a tsohuwar Jami’ar Bayero tun 1991,
- An naɗa shi na’ibin limanci Juma’a a masallacin Umar bin Khaɗɗab a shekarar 1998
- Yayi limacnci a masallacin Muntada, wanda aka fi sani da Masallacin VC na sabuwar Jami’atun 1998.
- Yana limanci a masallacin Nana A’ishah FCE
Gudanar Da Gwamnati:
- A sanda yake koyarwa a BYK ya nemi hutu daga Jami’a ya yi aiki a Hukumar Zakka ta Jihar Kano, a matsayin kwamishina, ya kuma yi aiki a Hukumar Shari’a a matsayin babban darakta 2004-2011.
Darussa A Masallatai:
- Masallacin Juma’a na Jami’ar Bayero tsohuwa.
- Masallacin Jami’ar bayero sabuwa.
- Masallacin Juma’a na Umar bin Khaɗɗab.
- Masallacin Nana A’isha na kan titin FCE Ƙofar Ɗakawuya.
- Masallacin Khalid BIN Alwalid na cikin Unguwar Ɗakawuya
Littafai Da Maƙaloli:
A. Liittafai:
- Kayyaɗe Iyali Da Matsayinsu A Musulunci 1988
- Matsayin Kuɗin Ruwa Da Bashin Banki A Msulunci 1993
- Zaman Aure A Musulunci 1992
- Tarbiyar Yara A Musulunci 1994
- Matan Annabi “Wives of the Prophet 1994
- Bankin Musulinci Wanda Babu Ruwa 1994
- Addu’o’in Annabi A Wni Da Dare 1995
- Shin Bankin Yan Kasuwa Ne? 1995
- NASIHA Ga Musulmai A Kan Gardamar Watan Azumi 1997
- Matan Sahabbai Na Ɗaya 1997
- Kasuwanci A Musulunci 1997
- Tsaraba Ga Mawadata Da Mabuƙata 2004
- Muhimmacin Lokaci Ga Musulmi 2005
- Siyasa A Musulinci “Politics In Islam”
- A Brief abaut Busuness in Islamic Banking, on the Basic of Shari’ah and Jurisprodence. 2011
- Darul Umma For Publishing, Kano.
- (in Arabic) 2012
- Matrimonial Liife in Islam 2016
- 2016
- 2017
- 2017
- Ladaban Zama Da Kishiya A Musuluci 2019
- Kamanin Annabi Siffofinsa da Ɗabi’unsa Domin Koyi da shi 2020
B. Maƙaloli:
1- “Zakatul As’humi Was Sanadat, Wat ta’amulu Biha Fis Shari’atil Islamiyyah”
Journal of Islamic Studies vo1: 1 NO:1, 2007.
2- Murabaha to the Purchase Order in the Juristic Perspective
“Bai’ul Murabahati Li Amirin Bis Shira’i.
Jornal of Islamic Sturdies
Department of Islamic Studies, BUK.
A paper presented at a conference organized y Al Muntada Nigerian Office 1998
- Islami Foundation of Nngeria, Kano.
- Concil of Ulama, Kano.
- Hudabiyya Fondation Kano.
- Council for Adult Islamic Education in Rural Areas, Kano State.
- Wakili a kwamatin masallacin Jami’ar Bayaro.
- Gamayyar Ƙungiyar Haɗakar Bankin Ruwa.
- Haɗakan Zuriyyar Malam Isma’ila Yakasai.
Alhamdu lillah. A yanzu Yahaya Tanko Yana Bayar da darasai na littafai huɗu a mako, a masallacin Umar bin Khaɗɗab da da littafan Sahihul Bukhari da Fathul Majid a masallatan Nana A’isha da na Khalid binil Walid a unguwar Dukawuya FCE.
A yanzu Allah ya azurta Yahaya Tanko da zuryya mai yawa, ‘ya’ya da jikoki.
Ya yi ritaya a watan Febreru na shekara 2015 daga Jami’ar Bayero ta kano. Amma ya kama aikin kwantiragi da jami’ar Yusuf Maitama sule ta Kano.