An haifi mai girma Ishaƙ Muhammad Ashiru a garin Kudan a ranar 15/03/1944, shi ne ɗa na farko ga sarkin Kudan Muhammad Ashiru, Alhaji Ishaƙ ya yi makarantar allo tun yana ƙarami a garin Kudan. Tun yana ƙarami ne kuma aka kai shi makarantar elementare a shekara ta 1954-1958.
Da ya gama ya wuce babbar makarantar firamare da ke Giwa a shekara ta 1958-1960. Daga nan sai ya zarce kwalejin gwamnati ta fasaha da ke Kano (Govt Tech Training School Kano) a 1964-1967. Ya wuce Kwalejin Horon Sojojin sama da ke Ingila (School of Tech Training Royal Airforce Newto England) a 1970. A inda ya samu takardar shaidar Diploma a kan gyaran injin jirgin sama.
Bayan ya dawo gida, sai ya shiga aikin sojan sama, inda ya kai har W.O II (warrant officer II) a 1968. Ya yi ritaya a shekara ta 1977, bayan rasuwar mahaifin sa, Sarkin Kudan Ashiru. A shekara ta 1977, ya samu aikin ƙaramar hukumar Ikara. A shekara ta 1991 ya zama Sarkin Nassarawa, A shekara ta 2001 (30/06/2001) ya zama Sarkin Kudan a sakamakon zamowa Hakimi da ƙanin mahaifinsa Alhaji Haladu Yakubu ya yi, haka kuma Alhaji Ishaƙ Ashiru ya zama Hakimin Kudan Ciritawan Zazzau.
Abubuwan ci gaba da aka samu a zamaninsa
1. Shimfiɗa kwalta da ta ratsa garin Kudan gabas da yamma, kudu da arewa.
2. Shimfiɗa kwalta daga Kudan zuwa Sundu.
3. Kafa Asibitin ƙorama.
4. Kafa makarantar firamare guda biyu a kudu da arewacin Kudan.
5. Ƙarin fanfunan burtsatsai a garin Kudan.
6. Ƙarin rumfunan kwano a kasuwar Kudan.
7. Kafa barikin ‘yan Sanda.
8. Kafa kamfanin buga bulo na farko.
9. Kafa makaranta mai zaman kanta (Private School).
Bugu da ƙari kuma, yana ɗaya daga cikin manya-manyan sarakunan Kudan waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya haɗi da kula da tarbiyar mutanan da yake shugabanta a lokacin sa. Sannan kuma yana sasanta ma’aurata haɗi da ba su shawara akan zamantakewar auratayya, sannan kuma mutum ne mara girman kai, saboda idan wani abu ya faru na addinin wanda mas’alar ta zo gaban sa, to yana ɗaukar wayar sa ya tuntuɓi masana na wannan ɓangaran, kamar yadda marigayi malam Surajo Yunusa Kudan ya shaida mana a lokacin da yake raye.
“Mai girma hakimin Kudan yana kiran sa a waya idan wani abu ya taso na addinin domin neman fatawa”, bugu da ƙari kuma ni ma kai na shaida ne, saboda a shekarata 2014 akwai wata mas’ala da ta taso wanda wani ya auri wata mace watan su biyar dai-dai sai ta haihu. Wanda aka kawo wannan mas’alar gaban sa, kuma ya yi hukunci akan haka, ni kuma ina gefe ɗaya a zaune, sai ya tambaye ni akan hukuncin da ya yanke, yaya addini ya tsara, nan take na duba abinda na ga hakan ya yi daidai.
Sannan sai ya yi wa mutanan wajen jawabi cewa “kada ku ga na tambayi wannan yaron wani abu akan wannan mas’alar, saboda akwai wani littafi ne wanda ya rubuta akan irin wannan mas’alar, ya kuma turawa mai martaba sarkin Zazzau Dr. Shehu Idris har ma ya ɗauki nauyin buga littafin”.
Sanna kuma dukkanin wanda ya ga ya yi shigar banza ko kuma ya yi askin banza ko kuma ya zo ya wuce ta gabansa ba tare da ya yi musu sallama ba ko gaisuwa ba, sai ya kira shi ya yi masa faɗa akan haka.
Sannan kuma a shekara ta dubu biyu da ɗaya ne (2001) aka naɗa shi a matsayin sarkin Kudan, bayan sarkin Haladu Yaƙubu ya tafi, wanda ya yi mulki na tsawon shekara ashirin da shida, wato daga 1975-2001, Sannan kuma a shekara ta 2008 ne a sake naɗa shi a matsayin Ciritawan Zazzau kuma Hakimin Kudan.
Mai girma Ishaƙ Muhammad Ashir ya samar da ci gaba a garin Kudan sosai tare da nuna ƙaunarsa ga mutanan garin, saboda haka tun daga rasuwar Mahaifin sa da kuma sarkin Kudan Haladu Yakubu da mutanan Kudan, mutanan Kudan suke raɗaɗin rabuwa da mai kishin su, har sai da Allah ya kawo musu mai girma Ishaƙ Muhammad Ashir, wanda ko yanzu mutum ya shiga garin zai tabbatar haka, wanda waɗan su suke ganin tunda aka mai da shi Ciritawan Zazzau kuma Hakimin Kudan, suka rasa sarkin mai kishin su haɗi da kula da al’amuran su tare da zama da su haɗi da zuwa gidan rasuwa ko suna.
Mutanan garin Kudan ba su taɓa mantawa da irin alherin da mai girma Ishaƙ Muhammad Ashir ya yi musu ba, saboda an samu cigaba da yawa a garin, wanda furtawa a yanzu ƙauyanci ne, kawai mutum ya shiga garin zai gani ko kuma ya tambayi mutanan garin manyan zai ji ruwan amsoshi. Sannan kuma ya yi aure yana da mataye guda uku kamar haka;
1. Halima
2. Mariya
3. Hindatu
Sai kuma sunayen ‘ya’yan sa kamar haka;
1. Usman (Ɗanladi). 10. Nafi’u
2. Balarabe. 11. Isma’il
3. Mas’ud 12. Gaddafi
4. Nasiru 13. Imrana
5. Abdulshahid 14. Umar
6. Abubakar 15. Yunusa
7. Muzammil 16. Sha’awanatu
8. Furaira(Hajiyayye) 17. Karimatu
9. Aisha 18. Shamsiyya
10. Raliya 19. Aliyu (Ɗan Asabe)
Ana yi masa kirari da;
Dattijo a gai Na Mariya, Hakimin mu mutun mai gaskiya
Is’haƙ na Hindatu Jarumi, Na Halimatu Baban Nasiru,
Hoɓɓasa Soja mazan ƙwarai.
(Mun samu wannan jawabin ne daga bakin mai girma Ishaƙ Muhammad Ashir Kudan a ranar 29/12/2020 a ɗakin sa wanda yake cikin gidan wanda muka tattauna da shi). Allah ya yi masa rasuwa a ranar Lahadi 02 ga watan Juni, 2024 da misalin ƙarfe biyu na rana, an yi masa sutura da misalin ƙarfe 5:00 na Yamma, wanda aka rufe shi a cikin gidansa.
Don karanta tarihin Fati Nijar danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu