Tarihin Afirka Kashi Na Ɗaya

0
17

Afirka na da mutane biliyan ɗaya da miliyan ɗari huɗu da saba’in da huɗu da dubu ɗari biyar da uku da ɗari bakwai da saba’in (1,474,503,770). Idan aka kasa yawan mutane a duniya tana da kashi goma sha bakwai da ɗigo tara (17.9%) na mutanen duniya. Faɗin ƙasar Afirka ya kai 30.37mlsq/km. Wanda su kan su yammacin Turai (Western Europe) France, Germany, Spain da sauran su kawai 2.2mlsq/km.

Wannan ƙasashe ba su kai ma Jamhuriyyar Congo (Democratic Republic of Congo) ba, idan ka haɗa waɗancan ƙasashen guda goma saboda faɗin ƙasarta ya fi 2.345 million km2. Algeria ita ce ƙasar da ta fi kowacce a Afirka. 

Harsunan Afirka sun fi dubu biyu, akwai ƙasashe guda hamsin da huɗu (54), ana taƙaddama a kan ƙasashe guda biyu; Yammacin Sahara (Western Sahara) da Somali (Somali Land). Sauran ƙasashe hamsin da huɗu ɗin nan duk ƙasashen kansu ne, yawancin ƙasashen nan duka in banda Habasha (Ethiopia) da inda ya zama Eritiriya (Eretria) yanzu duk sun taɓa zama a ƙarƙashin mulkin mallaka, ko dai na France ko na Ingila ko na Jamus ko na Belgium ko Portugal.

Misali ma dai ita Jamhuriyya Dimokaraɗiyyar Congo (Democratic Republic of Congo) ta na cikin ƙasashen duniya da suke da arzikin ƙasa kamar irin su Russia da China da Amurka. Belgium ce ta mallake ta. Kusan duk ƙasashen Afirka sun zo ƙarƙashin Turai, kuma su na da bambanci da yawa a tsakaninsu.

Afrika ta Arewa sama da Sahara ke nan ƙasashen Larabawa ne waɗanda suka haɗa da Morocco da Algeria da Libiya da Tunisia da Misra, idan ka yo ƙasa da Sudan da Murtaniya da Yammacin Sahara (Western Sahara) ɗin nan ƙasashen Larabawa ne, sun daɗe su na da alaƙa da Turai tun kafin mulkin mallaka, tun da kamar ƙasar Tunusia, nan ne asalin ƙasar Cartage, wacce ta yi yaƙi da Rum. Shugaban wannan ƙasa Hanibal ya kai mu su mummunan hari sun yi gwagwarmaya sosai.

A ƙasar kuma an taɓa samun Emperor na Rum daga Nubiya, saboda haka waɗannan ƙasashe su na da kyakkyawar alaƙa da Turawa ta shekaru ɗaruruwa ko dubunnai tun kafin zuwan Annabi Isah (A.S). Ƙasar Misra (Egypt) kowa ya san tarihinta, suna daga cikin tushen wayewar ɗan Adam. Marocco kuma idan aka bibiyi alaƙarta da Andalus da sauransu, ita ma tana da dogon tarihi. Waɗannan ƙasashe su na da alaƙa da Turawa, mutanensu su ma fararen fata ne. 

Idan aka yi ƙasa daga arewa (Maghrib) za a zo Afrika ta Yamma an yi dauloli masu tarihi masu martaba, irin su; Ghana, Mali, Songhai, Borno, Benin, Sokoto da sauransu, an yi su kafin zuwan Turawa. Haka har Turawan suka gama abin da za su yi dai, suka tafi suka dawo wa da ‘yan Afrika mulki. 

To amma me ya sa Afrika ta fi kowacce nahiya a duniya koma baya, kuma mai ya sa demokuraɗiyya ta ƙi kankama a Afrika, ko kuma menene ma ainahin shi wannan dimokuraɗiyya? Shin zai yiwu a Afirka?

Shin samun ci gaba sai lallai ta Gwamnatin dimokuraɗiyya irin yadda Turawa suka fassara ta? Idan haka ne me ya sa aka zo aka kawowa mutanen Afirka wannan dimokuraɗiyya kuma ta ƙi ta yi mu su aiki?

Wannan suna daga cikin dalilan da za a duba a tarihance, menene bambancin mutanen Afirka da sauran mutanen duniya da waɗannan abubuwan suka faru? Domin a fahimci wannan dole ne a duba tarihin ita kanta Afirka, kasancewarta da yadda ta zo ta zama har su Turawan nan suka mallake ta, kuma har yanzu ba su sakar mata mara ba (yadda ake ce wa).

Har yanzu ƙasashen Afirka su na ta bilinbituwa sun kasa kama hanyar da za su samu ‘yanci da tattalin arziki. Kowacce ƙasa a cikin Afirka ta na da matsala, waɗanda ba su da matsalar wata ƙila za ka ga abu kaɗan idan ya same su sai su rushe. Kamar Libya lokacin da suka kori Gaddafi.

Ƙasar Libiya Allah Ya yi mata albarka, mutanen ƙasar suna cikin jin daɗi, aka dinga zuga su da haɗin bakin shugaban ƙasar Amerika Barak Obama, wanda  shi ne baƙar fata na farko da ya shugabanci ƙasar da Hillary Clinton sakatariyar harkokin waje ta Amerika.

Ruguza Libiya kuma ya yi tasiri a cikin Afirka, fitintinu da yawa suka damu mutanen Afirka tun daga maƙotanta irin su Nijar, Mali, Najeriya da Burkinafaso. Rushewar Libiya ta sa kayan yaƙi sun bazu kuma an shiga wani bala’i.  Gaddafin nan duk abin da ya yi wa mutanen ƙasarsa suka zo suka saurari Turawa suka bijire, yanzu ga shi ƙasar gaba ɗayanta ta rushe. 

Wannan nazari da bayani an yi su ne don a fahimci, menene ya sa Afrika take cikin wannan matsala, a dalilin haka, shuwagabanni suke cewa ya kamata Afrika ta ɓullo da irin tata dimokaraɗiyyar.

Ba za a iya ba da amsar duk tambayoyin da suka shafi matsalar Afirka a wannan nazarin ba, amma za mu kalli abin ta mahanga da za mu qyarawa kanmu fahimta na waɗannan abubuwa da suka faru a Afrika suka janyo Afrika ta zama yadda take, kuma an kasa samun bakin zaren a siyasance har yanzu.

A siyasance babu cigaba a Afirka, wannan ya haifar da rashin cigaba na tattalin arziki. Idan aka kwatanta ƙasashen Afrika da sauran ƙasashen duniya irin su; South Korea, Singapore da Malaysia har ka zo kan ƙasa irin su Indonesia, ƙasashen Afrika su ne koma baya. 

Saboda haka za mu bi abubuwan nan daki-daki mu duba mu ga me ya samu Afrika kafin ma mulkin mallaka, da kuma yadda aka cutar da mutane aka dinga cinikin bayi. Bayan su Turawa sun hana cinikin bayi sai kuma suka zo da ƙarfin soja su mallaki ƙasashen nan na Afirka.

Ya aka yi aka ba su ‘yanci, waɗanne irin shugabanni ne suka ɓullo a waɗannan ƙasashen, da irin kisan gilalr da aka yi mu su.  Sai mu duba yadda ƙasashen da suke yin demokuraɗyiya, shin mutanen ƙasashen musamman masana a cikinsu suna alfahari da wannan tsarin demokuraɗiyya da ake son a tilasta ƙasashen Afrika lallai su yi shi.

Kuma menene asalin demokuradiyya, rana ɗaya ko lokaci guda aka kafa shi, ko kuma an gina shi ne a tsahon lokaci. Kuma a wacce ƙasa aka fara shi saɓanin yadda Turawa suke nunawa.

Domin karanta tarihin ranar demokuraɗiyya a Najeriya danna nan 

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceNeman Aure Bisa Koyarwar Musulunci
Labarin na GabaYadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su
Dr. Ibrahim Ado Kurawa
An haife ni, a ranar 10 ga Agusta, 1963, a Kano. Na yi karatu a fannoni daban-daban, tun daga kimiyyar halittu har zuwa karatun Larabci da ilimin addinin Musulunci. Na wallafa littattafai da takardu masu yawa kan tarihi, siyasa, da al'adu, wanda hakan ya ba ni damar samun kima a duniya, har ma na zama ɗaya daga cikin masu zama a Rockefeller Villa Serbelloni a Italiya.