Tag: ilimin aure

  • Yadda Za Ki Yi Mu’amala Da Uwar Mijinki

    Yadda Za Ki Yi Mu’amala Da Uwar Mijinki

    Mahaifiyar miji ita ce mace mafi ƙima da daraja a wajensa. Kuma ita ce mafi kusanci da shi.

    Ita ce ɗan mukullin arziƙinsa, ɗaukakarsa, da albarkarsa. Allah Ta’ala ya ba wa Annabinsa (S.A.W) labarin Uwaisul Ƙarni. Manzon Allah (S.A.W) ya ba da labarinsa a wajen sahabbansa. Duk da girman matsayi irin na Sayyadina Umar(R.A). Amma yai masa wasiyya da in ya gamu da shi Uwaisul Qarni. Ya nemi yai masa addu’a, hakan kuma aka yi.

    Halaka ce babba, ki bar mijinki yana saɓa wa iyayensa.

    Cikin suratu Baqara: 73.
    :”… Kuma ku kyautata wa iyayenku, ku zama masu biyayya a gare su”.

    A duk lokacin da Uwa ta sa wa ɗanta namiji albarka. Wannan albarka tana bibiyarsa da kuma’ya’yansa. Wato ɗaya daga cikin hanyar da ‘ya’yanki za su yi albarka. Shi ne ta wajen uwar mijinki.

    Ya zama dole ne ga kowacce mace. Ki san yadda za ki yi mu’amala da uwar mijinki.

    Mu'amala Da Uwar Mijinki

     

    HANYOYIN MU’AMALA DA UWAR MIJI

    1 HAƘURI: Yin haƙuri da ita, ko da ta faɗi baƙar magana . Ka da ki mayar mata. Yin haƙuri da yawan buƙatunta. Shi haƙuri dukkaninsa alkhairi ne.

    2 – KARANTAR TA: Akwai buƙatar ki karanci halin uwar mijinki sosai. Kuma ki koyi irin yadda ake wa mai irin halayenta. Domin kuwa ana samun wasu masu kaushin hali, da sa ido, da kishi, da rowa, da mita da dai sauransu.

    3 – GIRMAMA TA: Amsawa da yin abin da tai umarni. Yin waya ki gaishe ta. Ziyarar ta domin ku ɗan zanta. Aika mata da jikokinta su gaishe ta.

    4 – TAIMAKON TA : Duk sanda kika kai mata ziyara. Ki taya ta aikin da kika tarar tana yi. Shara , girki , ….

    5 – KYAUTA : Kyauta tana faranta rai. Kuma alama ce ta kana son wanda ka baiwa. Tana nuna kana tunawa da shi. Daga lokaci zuwa lokaci. Daidai ƙarfinki, ki dinga aikawa da Uwar mijinki. sabulu, turare, goro, lalle , da kuɗi.

    Da kuma yi mata kyauta a lokuta na musamman. Kamar da azumi , da sallah , da dai sauransu.

    6 – KUNYA : Ki dinga jin kunyar iyayen mijinki.

    A Duk lokacin da mijinki ya ga kina ba wa mahaifiyarsa kulawa. To zai fahimci irin ƙaunar da kike masa. Zai ƙara ƙaunar ki, ya ba ki matsayi na Musamman a Zuciyarsa. Ga wani labarin Wata Mata da Mijinta.

    Ma’aikaciya ce ni mai himma sosai, da bana son wasa da aikina. Sai muka wayi gari surukata ta rasu ( Uwar Mijina). Na roki a ba ni lokaci, domin a yi jana’izarta da zaman ta’aziyya. Amma fir Shugabana da nake ƙarƙashinsa ya ƙi amincewa. Sai dai ya ba ni awa biyu rak. Na ce masa gaskiya mijina na tsananin buƙata ta . Domin ba shi da tamkar mahaifiyarsa. Shugabana ya ce: Ni dai awa biyu na ce . Muddin ki kai zamanki kuwa to zai zama kin sallami kanki.

    Nai tafiyata kawai, cike da tsoron ma na rasa aikina. Domin gaskiya mijina ya fi min aikina. Nai zamana ina lallashi da tausayawa mijina, har akai uku. Ba shakka mijina yai farin ciki da irin kulawata. Na samu ƙarin soyayyarsa da daraja a wajensa. Yakan ce min:” Matata ba zan manta da irin abin da kika min ba. A lokacin da na rasa mahaifiyata”.

    Allah Mai iko, sai gashi ban rasa aikina ba. Shugabana ya bar wajen aikinmu. Ni kuma aka min shugabanci.

    A ƙarshe dai taimaka wa mijinki ya kula da iyayensa. Zai zame miki alkhairi cikin rayuwarki.
    Wani Bature ma ya ce ,ana iya gane irin son da mace ke ma. Idan aka ga yadda take son iyayenka.

    Domin karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki danna koren rubutun nan

    Litattafai da aka duba:

    1 – Qur’an
    2 – Riyadu Salihin.

    3 – 101 Amazing ways to say”I LOVE YOU !”. By Cucan Pemo.

  • Yadda Ake Wankan Soyayya

    Yadda Ake Wankan Soyayya

    Wankan soyayya ana yin sa ne a tsakanin ma’aurata. Kuma yana da tasiri sosai wajen sanya shaƙuwa. Abu ne mai matuƙar daɗi, da sanya farin ciki da nishaɗi.

    Sabbi ko tsofaffin ma’aurata duk na iya yi. Akwai buƙatar namiji ya gayyaci matarsa. Masoyiya ta taho mu yi wanka tare mana. Zan so a ce na wanke kyakkyawar surar jikinki”.

    Ko kuma ita ta gayyaci mijinta. “Rabin Raina, bari in zo in wanke ma bayanka mana. Son ka ya lulluɓe min zuciyata. Ya sa ina son a ce dai, yau ni zan ma wanka”. Kafin ya ba ki amsa, tuni kin ɗau sabulu da soso. Daman a shirye kike. Za ki iya sanya kyandir ko fitila mai kala (wato haske mai duhu).

    Yadda Ake Wankan Soyayya

    YADDA AKE YI

    1 – Gayyata cikin kalmomi soyayya tare da sakin jiki .

    2 – Ma’aurata za su saɓa junansu da sabulu. Sai su bar kumfa. Za su yi amfani da ita wajen shafe-shafe jikinsu na tsawon lokaci.

    3 – Ma’aurata masu  kwami na wanka. Za su cika shi da ruwa, su shiga ciki. Za su riƙe juna a ciki. Da yin dukkan wasanni da za su ji daɗi.

    4 – Shiga ruwan sama an lokacin damuna. Yin ‘yan guje-guje da wasanni a cikin ruwa.

    5 – Wasan ruwa musamman a lokacin zafi. Ta hanyar fesawa da mesa ( Ta ban-ruwan flower) . Ko kuma da wani mazubi.

    Wankan soyayya ya samo asali ne daga wajen Annabi ( SAW) .
    A’isha (R.A) ta ce “Mun kasance muna wanka ni da Manzon Allah ( S.A.W) daga mazubi guda ɗaya. Muna kanfata daga ruwan baki ɗaya”.
    (Bukhari da Muslim)

    A ƙarshe nake tambaya kin taɓa wanka tare da mai gidanki? Idan ba ki yi ba, to yam kamata ki shirya muku.

    karanta rubuce-rubuce na yadda ake shagwaba mai gida lokacin hutu ko yadda ake da mai gida lokacin al’ada domin karantawa danna koren rubutun

    Litattafai da aka duba

    Umdatul Ahkam
    Babul haidha

    Physical touch
    The 5 love languages
    Gary Chapman

    Aure A Musulunci
    Amina Yusuf Gwamna

  • Yadda Ake Faɗar Ina Ƙaunar ki/Ka A Soyayya.

    Yadda Ake Faɗar Ina Ƙaunar ki/Ka A Soyayya.

    Faɗa wa kogin soyayya abu ne mai sauƙi. Haka ma faɗa wa masoyi ko masoyiya, ina son ka/ki, bai da wahala. Sai dai yakan yi wa masoya wahala idan lokaci yai tsawo.

    Musamman a ce kalmar ta dinga tasiri tamkar farkon soyayyarku ne. Kuma lalle akwai buƙatar yawan fadar Ina ƙaunar ki/ka. Sai dai a tabbata da gaske ake. Kuma cikin hanyoyi daban-daban. Niyya da tasirin kalmomin shi ne muhimmi. Shi ke sanya bugawar zuciya. Ya sa shaƙuwa da Bege. Ya haɓaka soyayya ta dinga ƙaruwa.

    Muna so a ce dukkan sanda ka fadi “Ina kaunar ki/ka” Ta zama ta sanya farin ciki da harbawa zuciya ga masoyi dake sauraro saboda haka, sai an bi wasu hanyoyi daban-daban. cikin canja salo tare da ‘yan dabaru. Ayyukanka na magana ga masoyiyarka, ba ma tare da furta kalma ba.

    Misali:

    Wajen kwanaki huɗu (4) kenan, ina cikin ɓacin rai da damuwa. Ni kaina ba zan ce ga asalin matsalata ba. Ina zaune kan tabarma zuciyata cike da jin haushin mai gidana. Na ɗora ruwa zan yi tuwon masara kenan. Sai na ji waya: “kar ki ɗora tuwo yau, ki shirya bayan sallar isha’i za ki raka ni unguwa”. Sai ya kashe wayarsa.
    Duk da kasancewar sa talaka, amma yana da ƙoƙari akan gidansa. Sai dai kuma ba ya birge ni.

    Tunani na fada: unguwa kuma? To ina za mu? Wani abu ne ya faru a gidansu Goggo? Nan da nan na canja kaya. Ina idar da sallar isha’i kuwa ,sai ga shi. Yai mana shatar a-daidaita ( Opay ). Bayan mun zauna na ce lafiya kuwa ? Ya ce, “ƙalau”. Sai ya kamo hannuna ya ɗora a kan cinyarsa. Kawai sai na ji wani sanyi a raina. Yana riƙe da hannuna har muka isa Yahuza Suya. Ya biya a-daidaita ta cikin waya. Muka sauka ya ce zo mana.

    Ya nuna min kujerun waje na daidai shuke-shuke. Shi kuma ya wuce wajen siyayya. Sai ga shi da kaza da lemo ( ice cream ). Ya buɗe muna ci. Sai ya sa hannu a aljihunsa. Ya ce miƙo hannunki. Sai ga shi ya ɗora min wata guntuwar takarda .

    Cikinta ya rubuta da kansa : “INA KAUNARKI SOSAI, A MATA BABU IRINKI” Habawa sai na jawo hannunsa na dinga sumbata ba adadi! Na Ƙara ƙura wa takardar nan ido, ina riƙe da hannunsa gam. Har sai da na ji hawaye sun fara gangarowa a kumatuna. Kawai na miƙe na faɗa jikinsa. Sai ya ce ke: “Mutane na kallon mu”. Ni kuwa nai kamar ban ji ba. Bayan na gama juye-juyena a jikinsa. Na ɗago na ce: “Wallahi na ji daɗi sosai. Sai na ji nan da nan zuciyata ta cika makil da soyayyarka. Na gode ƙwarai. Muna gamawa kuwa, ya zaro waya ya ƙara mana shatar a-daidaita. Muna shiga na kwanta jikinsa, ya riƙo ni, har muka isa gida. Sai na killace takardata da kyau. A koda yaushe ganinta na tuno min da fitarmu. Kuma inji wani sabon farin ciki. Gaskiya da na ɗauka ma, mijina bai iya soyayya ba. Shi ya sa sam ba ya birge ni a can baya.To kun ga akwai ayyuka da dama da su ka wakilci “INA ƘAUNARKI SOSAI” A wannan labari. Wato yin furuci Aiki. Soyayya Ingantacciyya.

    HANYOYIN FADAR INA KAUNAR KI/KA:

    LOKUTA : Masoya su dinga fadar ina kaunarki a lokuta daban-daban.
    1 -Da safe za a rabu ( zai je aiki).
    2 – Lokacin haɗuwa ( yana shigowa gida).
    3- Lokacin da za a yi barci.

    YARE : Amfani da yare kala-kala wajen faɗar Ina sonki. Larabci , da fulatanci , da Barbanci , da Yarbanci , da dai sauransu.

    Larabci : Uhibbuki
    Fulatanci : Mi yidi ma
    Barbanci : Nya Raina
    Yarbanci : mo nife re
    Inyamuranci : a hurum gi n’anya .
    Turanci : I love you

    WURARE : Canja wurare daban-daban koyaushe, Ka fada a ɗaki, anjima ka same ta a madafa ( kitchen) . In za ka fita a bakin ƙofa. In ka ajiye ta a unguwa.

    RUBUTU : Rubuta kalmar ina kaunar ki/ka.
    1 – A rubuta da rubutun ka/ki a takarda ko wani kwali ( cardboard paper) a ba wa Masoyi ya/yi.
    2 – Tura ma masoya ta waya. A sakon kar-ta-kwana (text message) .
    3 – Katin soyayya ku siya ku ba wa Masoyanku.

    HOTUNA : Tura hoton filawa , zuciya , tsuntsaye mai jan hankali. Da mai haɗe da kalmomin soyayya. Ta cikin Hanyoyin yanar gizo ( email , Whatsapp, …).

    KYAUTA : Kyauta babbar alama ce ta soyayya. Ana son ba da kyauta daga lokaci zuwa lokaci. Misali : Turare , sutura, zobe , agogo , da dai sauransu.

    A ƙarshe dai dukkanin waɗannan da ma sauran irin su. Ayyuka ne dake fassara cewa :” Ina KAUNARKI / KA”. Kun ga ɗaukar su da muhimmanci. Da sabawa da yin su a cikin rayuwarmu zai dinga haɓaka soyayyarmu.

    Litattafai da aka duba:
    1 – Islamic Education.
    By Iqraa charitable society. Jeddah, Saudi Arabia.

    2 – 101 Amazing ways to say “I love you ! “.
    By Cucan Pemo.

  • Yadda Za Ki Ratsa Yatsunki Cikin Na Mai Gidanki

    Yadda Za Ki Ratsa Yatsunki Cikin Na Mai Gidanki

    Hannayenmu na da amfani wajen abubuwa da yawa

    Mace ta ɗabi’antu da rike hannu mijinta na maganin matsaloli da dama. Kuma na sawa soyayyarta ta ƙaru ta ƙara matsayi. ( misalin 50% higher .

    Ratsa Yatsunki Cikin Na Mai Gidanki
    Ratsa Yatsunki Cikin Na Mai Gidanki
    Ga wannan labarin Masoya. Domin ganin tasirin haɗa hannu.

    Uzuri ne mai ƙarfi ya kama ni zuwa gidanmu. Na san halin kayana, bai son a je a wuni cur a gida, Yana da kirki saboda haka duk da baya so, bai hana ba, Amma fa muna tafe yana ta mita.

    “Lalle fa ba za ki wuni cur ba” faɗa min awa nawa za ki yi? Awa 1 ko biyu? Sai ki hau adaidaita(napep) ki dawo gida.

    Ta ce “ba damuwa, ko juyowa ma mu yi tare. Ka girmamin iyayena hakama”. Su ga koda a gurguje ne na je a yau da su ke tsanani buƙatata. Sai ta sa hannunta a kan hannunsa da ke kai tana ta shafa hannunsa.  Sannan ta dinga ratsa yatsunta cikin nasa : Wallahi Na gode, na gode Rabin Raina.

    Sai ya ɗan sassauta faɗan. Ni dai faɗa min awa nawa za ki yi ?

    Rabin Raina da gaske nake, ka gama min komai. Faɗa min kawai yaushe zan dawo?. ( Alhali a zuciyata ina da tsananin buƙatar in wuni cur da su, Kuma tabbas haka nake so da zai bar ni. Amma fa na san hali.).

    Muka ci gaba da tafiya. Amma na lura yanayinsa ya saki fuskarsa sosai yanzu. Sai na ƙara tunani na dube shi cikin murmushi.

    Oh! Rabin raina ina mamakin irin ƙoƙarinka. Wai a safiyar nan har an samu mai ruwa. Bai ma yi ko rabi ba, amma aka sake cikata mana duro. Allah dai Ya ƙarama arziki. Gaskiya ina jin daɗi, na gode sosai.

    Gogan nawa sai ya yi murmushi. Da haka dai na dinga kalato zance muka ci gaba da hira.

    Bayan ya ajiye ni a kofar gidanmu cikin sakin fuska.: Idan kun kammala komai kawai ki min waya. Amma dai ki bi a hankali. Zan dawo in ɗauke ki.

    Farin ciki ya ishe ni alamun an ce in wuni cur kenan.

    Aikuwa ko da na masa waya na kammala sai ya ce : Yanzu na ɗan yi nisa, ki yi zamanki sai lokacin da na kammala zan zo, Sai da ya ƙara min wajan awa 4 bayan wayar mu da shi.

    Ga darussa cikin labarin.
    • Muhimmanci ɗada jiki:

    Duk da cewa iya hannunta ne ta ɗora wa hannunsa. Amma fa shi ne ya sa har temperature sa ta sakkowa cikin sauki.

    • Muhimmanci Godiya:

    Ta yi godiya. kan abin da ba shi take so ba. Kuma ta tuno da wani aikin daban (sayan ruwa) shi ma ta yi godiya, Sai wannan yasa shi canja ra’ayinsa

    • Muhimmanci Haƙuri :

    Shi yasa matar ta iya cin nasara, Da ta yi fushi cewa a kan me zai ta mita. Kuma alhali uzuri ne na iyayenta Da ba ta ci riba ba.

    • Muhimmanci Murmushi, Ba ɓata rai ta fito da damuwarta ba.

    A ƙarshe dai mu dinga kamanta haɗa yatsunmu mazanmu da mata. Domin kwantarwa da juna hankali .

    Domin maza karata yadda za ka riƙe hannun matarka na lallashi danna koren rubutun

  • Yadda Za Ka Burge Matarka Ta Zama Masoyiyarka

    Yadda Za Ka Burge Matarka Ta Zama Masoyiyarka

    Kowanne namiji yana tsananin son ya zama shi ne yake burge matarsa.

    Domin haka ne zai sa ya taka Babban Matsayi, Ta zama dukkan ƙoƙarinta da tunaninta shi ne faranta wa mijin nata, yi ma ka biyayya da yabawa hidimarka, Sai dai hakan zai kasance ne, Muddin ka dage kana ƙoƙari kan kulawa da ita.

    Burge Matarka Ta Zama Masoyiyarka
    Burge Matarka Ta Zama Masoyiyarka
    HANYOYIN DA ZA KA BIRGE MATARKA SU NE :

    1 – MATSAYI: Ka zama ka ba wa matarka matsayi mai girma. Ka dinga jaddada matsayin. Faɗa mata da nunawa a aikace mutuwa ce kaɗai za ta raba ku. Ko ka ce: komai yawan matana, Wallahi ba ni da tamkar ki. Duk abin da na samu , ke nake fara tunani.
    Kuma ba za ka bari wani ya wulaƙanta ta ba, ko da ƙannenka ne .

    2 – KALMOMI SOYAYYA:

    Ka shirya waɗansu Kalmomi na irin soyayya da kake mata. A koda yaushe Mace na buƙatar kulawa da soyayya.

    3 – GIRMAMAWA:

    Ka girmama dukkan mu’amalarka da ita. Ban da zaginta, wulaƙanta iyayenta , ko da ‘yan uwanta. Kar ka jefe ta da kaya: kana nufin ba ta kayan. Kar ka zage ta, komai yadda ta ɓata maka rai kuwa.

    4 – FITA:

    Ka fita tare da ita wajen cin abinci, gidan zoo , wajen wasanni . Domin ku ɗan ɗebe wa juna kewa. Ku ci wani abin, ku yi hira. Wannan irin fita na burge mata sosai. Ya zama ko da sau ɗaya ne a wata biyu.

    5 – MAGANCE MATSALARTA:

    Yin ƙoƙari ka magance matsalar da take ta kokawa. Wato ka lura sosai ka ga tai ta faɗar abu: Ba ka ga kwalliyata ba? Kai kullum ba za ka dawo ba sai can dare?
    Ina son in dinga ma kwalliya, amma ɗinkinka daga sallah sai wata sallah(Eid).

    6 – KULAWA DA HAƘƘOƘINTA: Ka zama ka tsaya sosai wajen abinci, lafiya, tarbiyya yara, kuɗin makarantarsu, gamsar da ita a shimfida, Kar ka dinga barinta da sha’awa.

    7 – SUMBA: Ka yawaita rungumarta da sumbatar matarka. Lokaci zuwa lokaci ba wai sai za ku haɗa shimfida ba.

    A takaice idan kana waɗannan abubuwa. Matarka za ta amince ta yarda da kai mijinta ne. Ta ji sonka ya lulluɓe ta, kana burge ta sosai. Sai kuma ka ga ita ma tana himma wajen sallama wa mijinta.

    LITATTAFAI Da aka duba:
    Fiqh of love
    Shaikh Yaser Birjas

  • Yadda Za Ka Riƙe Hannun Matarka Na Lallashi

    Yadda Za Ka Riƙe Hannun Matarka Na Lallashi

    Haɗa hannun Ma’aurata na da tasiri wajen sasanta rigima. Maza da yawa na jin nauyin bai wa matansu haƙuri.

    Hannu Matarka Na Lallashi
    Hannun Matarka Na Lallashi
    To ga wani salon rarrashi, Za ka kama hannunta, sai kuma ka haɗo da abin da yake faranta mata rai. Misali na yadda za ka yi a cikin wannan labari .

    Na kai ta gidansu ta yi kwanaki, tunda a wani garin daban muke zaune. Duk sanda za ta fita sai ta kira ta tambaye ni, sai in yi mata izini, Lokaci daban-daban koyaushe sai in ce A dawo lafiya. Sai wata rana ta tambayi zuwa unguwa, sai na ce yau ba na son ki fita.

    kar ki je, Ta ce: “Su wance ce fa wadda ta zo bikinmu, ta yi mana hidima sosai ka tuna? Shi ne fa zan je mu yi sallama, za su tafi gida, Su ma sun zo garin” Ni kuwa na ce : “Kawai ba na son yau ki fita. Can sai na je garin zan ɗauke ta mu dawo gida, Na tarar tana cikin fushi mai tsanani, na san laifin da na yi.

    Ni dai ba zan furta kalma ta yi haƙuri ba, Sai na fara tunani yadda zan ɓullo mata, Ta ɗauko jakar kayanta da zummar za mu tafi gida, kawai sai na riƙo hannunta mukai ɗan tattaki( tafiya mai ɗan tsayi zuwa wajen motata)

    Ina riƙe da hannunta na ce: Na fasa, ba yau za mu koma gida ba, kuma shiga mota kawai mu je ki yi siyayya .

    Aikuwa dai lalle wani farin ciki ne mara misaltuwa ya bayyana a wajenta, kafin na ankara ma ta rungume ni. Na ce “Au! ba fushi kike ba ?” Ta ce “Ai na huce”.

    Ga Darussa cikin labarin:

    1 – Riƙe hannunta na nuna mata: Yana son ta, kuma yana girmama ta, Sannan shi ne madadin kalmar ki yi haƙuri.

    2 – Yi mata kyauta na irin abin da ta fi ƙauna ne ya rikitata, Mijinta ya karance ta sosai, Ya san irin abun dake faranta mata.

    A ƙarshe maza su gane bin salon shawo kan matayensu. A daina barin matsala tai ta ɗaukar tsawon lokaci. Shi ne abin da zai inganta rayuwar ma’aurata. Ka da ka biye wa matarka ku dinga gaba.
    Duba yadda za ki ratsa yatsunki cikin na mai gidanki.

    Nazari/ Dubawa
    Lacca M. Bashir Abubakar Takai.

  • Yadda Ake Sai Da Safe A Shimfiɗa

    Yadda Ake Sai Da Safe A Shimfiɗa

    Shimfiɗar ma’aurata wuri ne da za su kwanta har gari ya waye, Saboda haka akwai buƙatar ya zama an gyara ta tsaf. Kuma ba hayaniya, ba haske Ya zama za a samu natsuwa sosai.

    sai da safe
    sai da safe

    Mai gida zai dinga taimaka wa matarsa, wato kawo turaren ɗaki, harma da wanda za ta sa a jikinta. Zai kuma yi wanka ya sa turare kafin ya kwanta da yin asiwaki.

    Matarsa kuma za ta tabbatar ta tsaftace duka ɗaki, ta gyara shimfiɗa, ta sa turare, ta yi ado da bargo, yadda zai ba da sha’awa

    Ta yi wanka da wanke baki, ta shafe jikinta da Humra mai daɗin ƙamshi, ta sa kaya masu jan hankali.

    HANYOYIN DA AKE SAI DA SAFE :

    1 – Ma’aurata za su kwanta ne manne da junansu, mai gida ya rungume ta Ko kuma ita ta kwanta kan ƙirjinsa, ko kan kafaɗarsa, Lalle ya zama jikinsu a haɗe yake.

    2 – Idan kawai barci za ku yi, sai ki ja mayafi ki lulluɓe ku duka, Ki sumbace shi. Ki ce : Allah Ya tashe mu lafiya, Ina son ka, Ku yi addu’o’inku na kwanciya barci.

    3 – Mai gida ya sumbace ta sau uku, idan yana nufin gayyatar ta…

    Ya sumbaci goshinta ya ce “Masoyiyata”, Ya sumbaci kumatunta ya ce, “kina cikin raina”, Ya sumbaci leɓenta ya ce, “Ina ƙaunarki sosai”, Shi kenan za ta miƙa wuya. Idan bai yi ba, ke sai ki yi gayyatar.

    A ƙarshe dai, duk Ma’aurata da su ke haka, in za su yi barci, za su kasance cikin ƙauna da begen juna.

    Duba rubutun yadda za ka Birge matarka ta zama masoyiyarka.

  • Yadda Ake Shagwaɓa Mai Gida A Lokacin Hutu

    Yadda Ake Shagwaɓa Mai Gida A Lokacin Hutu

    Akwai waɗansu keɓantattun ranaku da Mai gida ke hutu. Wani ya dauki hutun aiki na wata guda ko ya ɗebi sati . Ko kuma ranakun Asabar da Lahadi. Ya zama babu aiki kuma zaman shi a gidansa zai ƙaru.

    To sai ki yi ƙoƙari ki zamo wa maigidanki KARIYA daga kallace-kallace da yawon kawai.

    Tun da ga dama ta samu. Sai ki yi iya ƙoƙarinki Ki bi hanyoyin da za ki lulluɓe shi da ƙauna, da kyautatawa. Saboda babu wata rayuwa ta morewa, Irin ki samu ku manne da mijinki cikin soyayya.

    *Annabi (saw) ya ce ” Duniya wani ɗan (wuri) ne na jin daɗi ƙanƙani, amma mafi wannan jin daɗin mace ta gari.”.*

    Ko da ba waɗannan ranaku ba, mu yi amfani da ranakun da Maigida bai da aiki wajen samarwa mazaje hutu a cikin gidajemmu. Kasancewar mafi yawansu Litinin har Juma’a suna sintiri wajen aiki.

    ABUBUWA DA ZA KI YI:
    Ki yi Ƙoƙari ki dinga riga shi tashi daga barci. Ki yi wanka da caba kwalliya, ki sa riga mai shara-shara ko ɗamammiyya mai nuna sirrin jikinki.

    Duk ƙarshen Mako (weekend) ya zamo breakfast ya bambamta (inda hali) Ki kammala shi da wuri. Idan hutun na da tsayi. Ki tsara abincinki, in dai da hali.

    Ki nemi garwashi, ki turare gidanki. Ki sa turare jikinki wato humra. Kuma ki fesawa kayan da kika sa.

    Bayan ya dawo sallah, da kin jiyo takunsa, ki ƙarasa ki taryo shi. Ki gaishe shi cikin girmamawa. Ki ce Bismillah ga abincinka.

    Idan ya ce ba yanzu ba, zai dan kwanta ne. sai ki bi shi ki kwanta jikinsa ku huta* Idan ya nuna yana buƙatar ki, good. In kuma barcin ne da gaske, sai ki tafi ki shirya yaranki da gidanki. Kar ki bar su, su yi ta hayaniyar da za ta dame shi.

    Da azahar kuma

    ki kammala girki da wuri. Ki sake kwalliyya da ado, sai dai kamar atamfa, leshi, shadda ( waɗannan wanda suka fi kyau cikin kayanki da ki ke ɓoyewa ). kar ki manta da yawan aswaki.

    Idan ba a yi komai ba tun asubar nan. To, ki yi ƙoƙari ya kwanta ya huta, da azahar bayan ya ci abinci. Ki tabbata kin yi abin da zai kiɗima shi don ku huta tare. Ki ba da isashen lokaci kina sumbantarsa, da rungumarsa , da shafa shi. Shi ma ki bashi damarsa ya yi duk yadda yake so, don Ranar hutunsa ce .

    Ki gama abincin dare kafin magrib .

    Ki sake wanka kuma ki canja kwalliya. In kina haka zai dinga yawan shigowa gidansa.

    A ƙarshe dai, ki saki jikinki mijinki ne. Ku ci abinci tare, da wanka tare, da barci a kan kafaɗarsa. Hira ma kina jikinsa. Ki shagwaɓa shi sosai . Ki dinga jin ibada kike yi. Da yardar Allah za ki samu sakamako mai girma.

    Mai gida ya taimaka da sakin jikinsa. Da yaba wa matarsa dukkan ƙoƙari da take yi. Da kuma fita da ita wani waje domin samun hutawa irin ta Masoya. Domin karanta yadda ake tafiyar soyayya Danna koren rubutun nan.

    Litattafai da aka duba
    Hanyoyin mallakar miji

  • Yadda Ake Maraba Da Mai Gida

    Yadda Ake Maraba Da Mai Gida

    Maraba da mai gida da rakiya dai ‘yar kwarya-kwaryar karɓa ce, ko tattaki da ake wa mazaje domin samar da natsuwa, soyayya , shaƙuwa da girmamawa tsakanin ma’aurata . Da shi mai gida da matar gida, suna kasancewa cikin farin ciki. Sai dai yana da matuƙar muhimmacin gaske, mace ta yi ƙoƙari ta dinga kimtsawa.

    Annabi (S. A. W) yakan dawo gida daga tafiya lokacin walha (da hantsi) kuma yakan sanar da iyalansa cewa gashi nan tafe, tun kafin ya iso gida.

    Ashe sanar da iyali, dama ce ta su kimtsa, ga mai gida na isowa. Tabbas haka na nuna mana ba a so mai gida ya tarar da matarsa a wani yanayi mara kyau.

    Annabi (S. A. W) ya ce :”Idan ɗaya daga cikinku ya tsawaita tafiya, kada ya ƙwanƙwasa wa iyalinsa kofa da daddare. ( Bukhari).

    Zan yi bayani ne a kan waɗannan:

    1 – Hanyoyin da ake janyo hankali Mai gida.

    2 – Abubuwa da ake yi lokacin rakiyar mai gida.

    3 – Abubuwa da ake yi yayin maraba da mai gida.

    4 – Tambayoyi ga mazaje.

    5 – Ra’ayoyin mazaje .

    Da farko mu fahimci cewa mazaje na bambanta a yanayin ayyukansu. Wani aikinsa ba wahala, kuma yana da isasshen lokaci. Yana tashi aiki da wuri. Wani Kuma dole ya wuni cur, ga wahala, ga ba shi da lokacin kansa.

    Wani ɗan kasuwa ne, wani ma’aikacin gwamnati ne. Dole ne a samu bambanci a yadda waɗannan suke shiga da fita a gidajensu.

    Wasu kuma hali, ɗabi’a ko ince sabo da yadda suka taso tun kuruciya. Za ka ga wani na son zama a gida. Wani dama mai nacewa abokanai ne (zama a majalisa).

    Wasu kyakkyawar manufa ta kulawa da haƙƙoƙin iyalai ke sa su yawaita waiwayar iyalansu.

    Wasu domin irin kwalliyar mata, da yadda ake gyara gida ke kwaɗaitar da su juyowa gida.

    Wasu maza fa duk ba haka ba ne. Illa suna da sa ido. Son gani me ke gudana a gida, ke sa su yawan shiga gida.

    Wasu Kuma ƙazanta, masifa da yadda yara ke hayaniya ce sa ba sa iya waiwayar gidajensu.

    Koma dai mene ne dalili. Yana da muhimmanci mu yi nazari sosai. Mu gane bakin zaren da yi wa juna uzuri. Tare da kawo gyara domin inganta rayuwar aurenmu.

    Wato mu dinga bibiyar hanyoyi tarairaya, soyayya da hikima domin mai gida ya dinga waiwayowa gidansa.

    Idan mai gida aikinsa mai sauƙi ne . Ya tashi aiki da yamma. To, a samu ya leko gida kafin ya wuce majalisa hira. Ka da ya zama daga wajen aiki sai majalisa, sai kuma kwanciya barci. Ki tabbata kina gyara kanki da gidanki, domin jawo hankalinsa zuwa gidansa.

    HANYOYIN DA AKE JANYO HANKALIN MAI GIDA :

    Waɗansu daga cikin waɗannan abubuwa za ki Yawaita yin su. Har su zama ɗabi’arki a koda yaushe. Waɗansu za ki aiwatar da su tun kafin ya iso gida. Wasu kuma daidai lokacin shigowarsa.

    1 – Tabbatar da gidanki ya zama a kan tsafta. Babu wani abin da zai ɓata masa rai.

    2 – Kasancewa cikin tsafta, da sutura mai kyau, da kwalliya, da ƙamshi.

    3 – Tanadin abinci da aka kyautata shi da Lemo, da kayan marmari.

    4 – Tsaftace baki a koda yaushe.

    5 – Sakin fuska da yin haƙuri. Ban da riƙo ko mita.

    6 – Tura sako na soyayya, addu’a, (text message).

    7 – Sabar wa kanki da kalmomin soyayya da za ki dinga dukan kunnuwansa da su.

    8 – Sabar wa ‘ya’yanki natsuwa, Ka da ya zama koyaushe ba su da aiki sai guje-guje.

    9 – Kammala ayyuka na gida a kan lokaci kafin ya shigo. Katse kowanne aiki yayin da ya shigo.

    10 – Tattara hankalinki, tunaninki gare shi. Taƙaita hira a waya, kallo yayin da kuke zaune tare.

    ABUBUWAN DA AKE YI LOKACIN RAKIYAR MAI GIDA :

    1 – Za ki bi shi, ki tattaka masa, rakiya har soro ko bakin ƙofa.
    2 – Ki tabbata kin sa turare, ku rabu yana sheƙa ƙamshin turarenki.
    3 – Yayin rakiya haɗa jikinki da nashi ko rike hannunsa na da muhimmanci.
    4 – Yanayin kallonki ya zama cikin ƙauna da tarairaya.
    5 – Murmushi a fuskarki.
    6 – Addu’o’i kariya, da nasara, da fatan alkhairi. Addu’arki na da tasiri sosai ga mijinki.
    7 – Sumbaci Mijinki yayin rakiya.
    8 – Riƙe masa abin da zai fita da shi.
    9 – Ambato mijinki da suna na soyayya ko girmamawa lokacin rakiya.
    10 – Kula masa da adonsa da irin shigarsa. Gyara masa hula, kwalar riga da sauransu .
    11 – Yabawa tsabtarsa, irin ƙamshin turarensa, da yadda shigarsa tai kyau.

    Za ki haɗa wasu a Lokaci guda. Wasu abubuwa kuwa ki dinga caccanjawa.

    ABUBUWA DA AKE YI YAYIN MARABA DA MAI GIDA :

    1 – Ƙa’idar maraba da maigida sai ki zama wayayyiya ce ba bagidajiya ba. Kar ki kalli yawan shekarunki, ko yawan yara. A koyaushe mace a wajen mijinta, ba ta da wani iyaka na tarairayarsa.
    2 – Karantar lokacin da ya fi shigowa gida. Da irin sautin abin hawa na maigida .
    3 – Duk shigowarsa ki karɓi abin hannunsa. Leda ce, jarida, koma mene ne. Haka girmamawa ce.
    4- Babban abin da za ki mayar da hankalinki daga shigowarsa. Ya fahimci ya shigo wajen iyalinsa. Ki fara ba shi magani na natsuwa da kwanciyar hankali , ki haɗa jikinki da nashi , ki sumbace shi .
    5 – Dukkan miji na da tsananin buƙatar soyayya. Ba babba ba matashi a nan. Ki tarye shi da kalmomin soyayya.
    6 – A wani Lokaci ki shirya yadda tun daga maraba za ki shayar da shi bom na soyayya. Ki bugar da shi, Amma fa ba da kayan maye ba. Ki shayar da shi soyayya ta hanyar shagwaɓa.
    7 – Godiya da jinjina masa irin ƙoƙarinsa a lokacin taryar sa. Wato bayan karɓar abin da ya shigo da shi. Za ki yi ta godiya komai ƙanƙantar abin da ya kawo.
    8 – Haƙuri da yanayi da ya shigo a cikinsa. Cikin gumi, gajiya ko fushi.
    9 – Kaucewa tuhuma a yayin maraba. Daga Ina kake? Tuhuma ce. Amma Masoyina duk na shiga damuwa, na jika shiru ne, ina ta jimami ko lafiya kuwa? To wannan zai gane damuwa ce ta ƙauna, kewa, da Begensa.
    10 – Domin samun yi wa maigida maraba da daddare. Ki saba wa kanki shan shayi bayan sallar isha. Ki shagalta da nafilfili ko karatun Qur’ani. Shayi zai ba ki karsashi, ya hana ki barci. Maza da yawa sun fi ɗaukar maraba ta dare da muhimmaci. A dare ake gane zunzurutun ƙauna, da tausayi. Irin wanda uwa ce ta fi yinsa. Saboda uwa ce ba ta iya barci komai dare. Sai ta ga danta ya dawo gida lafiya. Kin ga yana da kyau ki sabawar wa kanki da jiranshi ya dawo kafin ki yi barci.

    11 – Nuna wa ‘ya’yanki muhimmaci maraba da mahaifinsu. Da iyaka daidai inda za su kauce su ba ku waje. Wato ku samu natsuwa da kula da juna.

    12 – Ki zama mai canja salon maraba. Da karance-karance domin ki goge da yadda za ki mu’amalanci mijinki.

    A taƙaice burinki kullum shi ne dirsa wa mijinki farin ciki ta masa maraba da rakiya ta musamman. Wannan zai ƙara miki ƙima da daraja . Mijinki ba zai dinga bari ki nesa da shi ba. Sai dai fa inda uzuri.

    TAMBAYOYI GA MAZAJE
    1 – Me maza suka fi buƙata, Matar mutum ta gabatar yayin da zai fita gida?

    2 – Mene ne suka fi buƙata yayin isowar su gida.

    3 – Mene ne yasa wasu mazaje ke ƙoƙarin waiwayowa gidajensu?

    4 – Mene ne yasa wasu mazaje ba sa son komawa gida?

    5 – Mene ne abin da ake maka da ya fi burge ka idan za ka fita gida?

    6 – Wane abu ya fi burgeka idan ka dawo gida?

    7 – Kana ga rakiyar maigida da taryarsa na da muhimmanci?

    8 – Kana iya yabawa rakiya da tarya da ake maka? Ta wacce hanya kake ganin haka?

    RA’AYOYIN MAZAJE :
    Na harhaɗe wadanda amsoshinsu ya zo iri ɗaya.

    RUKUNI SABBIN AURE
    Mu gaskiya mun fi buƙatar a ce sumbata tai yawa a cikin mu’amalarmu ta aure. Shi muka fi sha’awar samu a duk lokacin da za mu fita gida bayan an rako mu.

    Kuma lalle Muna son rakiya har soro. A ganinmu haka na daga cikin kulawa, da nuna damuwa aƙalla.

    RUKUNIN MATASA MASU AURE
    1 – Yayin fita gida lalle a yi mana addu’ar neman halak, a je lafiya a dawo lafiya. Ta tabbata ka fita cikin tsafta da natsuwa.
    2 – Yayin dawowarmu tarba mai kyau. A barka ka huta. A kaima ruwa ka yi wanka. A ba ka abinci.
    3 – Muna ƙoƙari dawowa gida saboda kulawar da ake ba mu.
    4 – Wasu maza ba sa son dawowa gida ne, saboda rashin zaman Lafiya da iyalinsu.
    5 – Abin da ya fi burge mu yayin fita gida, addu’a da ake mana.
    6 – Yayin dawowa fuskantar halin da muke ciki da tausaya mana.
    7 – Tabbas rakiya da maraba na da muhimmanci domin tsantsar soyayya ce a ciki.
    8 – Muna yaba wa matayenmu:Muna amsa gaisuwa , da yabon kwalliya.

    RUKUNI MATASA MARASA AURE

    Na farko duk da cewa ba mu da aure. Abin da mutum zai fi buƙata Idan zai fita gida. Matarsa ta duba shi tsaf. Duk wani abu da zai gyara shi ya zama fes. Ta shirya masa jikinsa ya kamata a ce, ta riga ta masa. Domin fa matar mutum tabbas ita ce mudubinsa.

    Sai kuma ya zama in zai fita ƙarshen abin da zai kalla (last memory), ya zama ita ce a cikin siffa ta soyayya. In dai tai haka ma Shi kenan , yin haka zai taimaka sosai.

    A taƙaice, har ma da bayanai sosai daga shugabanni da dattijai masu matuƙar amfani. Tare da nuni da yadda maza ke tsanani buƙata rakiya da maraba.

    Litattafai da aka duba
    Aure A Musulunci

    Lacca Aure a Garin Katsina . Satimba 2019.

    Men are from Mars Women are from Venus . John Gray, Ph.D.

  • Yadda Ake Amfani Da Na’urar Gwajin Ciki (Juna Biyu)

    Yadda Ake Amfani Da Na’urar Gwajin Ciki (Juna Biyu)

    Za a iya gwajin ciki da na’ura a kowane lokaci na rana; amma dai da sassafe shi ne mafi dacewa. (fitsarin farko).

    Ki yi fitsari a cikin roba ko kwano mai tsabta ko kofi ko duk abin da kike ganin fitsari zai iya zama a ciki.

    1. Sai ki yi fitsari a ciki, daidai gwargwado, wanda na’urar ba za ta lume duka a ciki ba
    2. Sai ki saka na’urar a cikin fitsarin; iya wajan tsinin ake so ya taɓa fitsarin.

    Kar ki taɓa wajen nuna sakamakon ko wajan tsinin da hannunki

    1. Sai a tsaida na’urar a tsaye kada fitsarin ya wuce alamar (MAX)
    2. Sai ki bar shi ya ɗan jima a ciki kada ya yi ƙasa da sakon biyar (5)
    3. Bayan ya ɗan jima a ciki, sai ki ciro nau’rar daga cikin fitsarin.
    4. Sai ki sa na’urar ta kalli sama wajan ɓangaran da aka rubuta (MAX).

    Idan ba za ki iya riƙe ta a hannu ba, za ki iya ajiye na’urar a waje mai tsafta domin jiran sakamako, ta yadda wajen alamar rubutun MAX din yana kallon sama.

    Sakamako

    • Idan ki ka ga layi mai launi wanda ya turu sosai guda biyu; to kina da ciki kamar yadda aka nuna a hoton nan.
    • Idan kuma ki ka ga layuka guda biyu masu launi, amma ba turarru ba, kina da ciki.
    • Idan kuma ki kaga layi ɗaya, to ba ki da ciki.
    • Idan kuma ki ka ga layi ɗaya mai launi turarre ɗayan kuma ba turarre ba shi ma ba ki da ciki.

    Karin bayani

    • Yayin da ki ke jiran sakamako, za ki iya lura da layi mai launi yana motsawa a cikin wajen nuna sakamakon, wannan ba matsala.
    • Kina buƙatar jira minti 10 don tabbatar da sakamakon.
    • Ba a amfani da sakamakon da gwajin ya bayar bayan minti 30.
    • Sakamako yakan iya canzawa ya danganta da irin na’urar da ki kai amfani da ita, amma wannan shi ne wanda aka fi amfani da shi.