Tag: ilimin aure

  • Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki 02

    Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki 02

    A bayani na farko mun bayar da wasu bayanai a kan yadda ake jan hankalin miji; Ga sauran bayanan nan.

    4. Iya Taku

    Takunki a lokacin da kike gabansa da tsayuwarki da zamanki, dole ne ya zamo na musamman.Ya kasance daban kuma cikin salo na ɗaukar hankali. kar ki kasance mara kuzari ko kina nuƙu-nuƙu a yayin da kike tare da shi.

    5. Ku yi Siyayya Tare

    Yana da kyau kuna yin siyayya tare musamman ƙananun kaya masu ɗaukar hankali, wanda za ki yi masa kwalliya da shi, shi kaɗai. Kuma ki nemi zaɓinsa a kan irin wanda yake so, hakan zai saka shi ya kasance cikin zumuɗi.

    6. Ado Da Kwalliya

    Ba dole ba ne, sai kin caɓa kwalliya mai yawa sosai ba, a wasu lokutan canza yanayin gyaran gashinki ko gyaran fata yana jan hankalin mai gida. Ko Kuma canza launin jambaki ko ƙara wani sabon launi a kan fuskarki wanda bai saɓa gani ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Zaki Inganta Halayyarki Da Ɗabi’u Masu Kyau danna nan

  • Muhimmancin Aure a Ƙasar Hausa

    Muhimmancin Aure a Ƙasar Hausa

    Muhimmancin Aure – Aure abu ne mai matuƙar muhimmanci a wurin Bahaushen mutum; wannan ta sanya da zarar yaro ya tasa za ka ga an yi masa aure.

    Kuma ma har idan an ga wani ya aikata wani abin da bai dace ba; wanda cikakken mai hankali ba zai yi ba, sai ka ji an ce ‘Ai ba shi da aure’.

    Ko kuma idan saurayi ko yarinya kansu na rawa, sai ka ji an ce, ‘A yi musu aure ko sa nutsu’.

    Kenan aure sababi ne na nutsuwar mutum a wurin al’ummar Hausawa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Muhimmancin Aure A Rayuwa danna nan

  • Abin da ya Halatta Game da Mai Jinin Haila da na Biƙi Tare da Mazajensu

    Abin da ya Halatta Game da Mai Jinin Haila da na Biƙi Tare da Mazajensu

    Ya halatta ga mai jinin haila da na biƙi tare da mazajensu abin da zai zo:

    • Ci da sha da bacci tare
    • Wanke kan miji da taje shi

    Mene ne ake so game da mai jinin haila da na biƙi?

    Ana so ga mai jinin haila da kuma na biƙi fita don halartar idi tare da ƙaurace wa sallah.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Darasi Na Tara Game da Hukunce-Huncen Jinin Cuta danna nan

    Don karanta cikakken bayani a kan Yadda Za Ki Gyara Kanki danna nan.

  • Hukunce-hukuncen Jinin Haila Da Na Biƙi

    Hukunce-hukuncen Jinin Haila Da Na Biƙi

    Mene ne yake haramta saboda jinin haila da na biƙi?

    Salla tana haramta saboda jinin haila da na jinin biƙi da Azumi da Ɗawafi da saduwa da saki; a bisa haɗuwar Malamai.

    Kuma maganganun malamai sun saɓa game da zama a masallaci da taɓa Alƙur’ani da karanta shi; sai wasu daga cikinsu suka halatta haka, wasu kuma suka hana.

    Ko za ka ambata mana dalilan haramcin abubuwan da suka gabata?

    Amma haramcin salla, saboda jinin haila dana biƙi. Saboda faɗar Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa, ga Faɗima ‘yar Abi Hubaish. Idan haila ta zo, to ki bar sallah.

    Amma haramcin yin Azumi, saboda jinin haila da na biƙi; saboda faɗar Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa; shi ashe ba idan ɗayarku tana jinin haila ba ta Azumi ba ta salla ba? Suka ce haka abin yake.

    Dalilin haramcin yin Ɗawafi, saboda jinin haila da biƙi faɗar Manzon Allah; tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi;

    Ga A’isha lokacin da ta yi jinin haila tana mai harama da aikin Hajji; ki aikata duk abin da mai aikin Allah, har sai kin samu tsarki;

    Haramun ne saduwa da mai jini haila da na biƙi.

    Saboda faɗar Allah Maɗaukaki: “To ku ƙaurace wa mata a kwanakin jinin haila; kuma kada ku kusance su har sai sun samu tsarki”.

    Kuma saboda faɗar Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa, lokacin da ayar ta sauka; “Ku aikata komai da matanku, in ban da saduwar aure”.

    Abin da ake nufi da haka a sake su lokacin tsarkin da ba a sadu da su ba.

    Faɗakarwa:

    Jinin biƙi yana bambanta da na haila ne; da kasancewar idda ba ta afkuwa da shi; saboda iddar mai ciki tana ƙarewa ne da haifar ciki.

    Allah Maɗaukaki ya ce: “Mata masu ciki iddarsu shi ne su haife cikinsu”.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Tukunyar Mace Ta Musamman danna nan.

  • Bayanin Mafi Yawancin Kwanakin Jinin Biƙi

    Bayanin Mafi Yawancin Kwanakin Jinin Biƙi

    Shin nawa ne mafi yawancin kwanaki na jinin biƙi?

    Jinin Biƙi – An karɓo daga Ummu-Salama, Allah ya yarda ita, ta ce:

    “Mai jinin biƙin ta kasance tana zama a lokacin Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; tsawon kwanaki arba’in”.

    Kuma Imam Tirmizi, Allah ya jiƙan sa, ya ce: Haƙiƙa malamai da sahabbai da tabi’ai da waɗanda suka biyo bayansu, sun haɗu a kan cewa:

    “Haƙiƙa mai jinin biƙi tana barin salla tsawon kwana arba’in, sai dai, idan mai jinin biƙin ta ga tsarki kafin haka; to haƙiƙa za ta yi wanka ta yi salla”.

    “Idan ta ga jinin bayan kwana arba’in, haƙiƙa mafi yawancin malamai sun ce: “Ba za ta bar sallah ba bayan kwana arba’in”. Kuma shi ne maganar mafiya yawancin Malaman Fiƙihu.

    Sai iyakacin kwana arba’in ya kasance shi ne galibin yawancin kwanakin jinin biƙi.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Darasi Na Shida Game da Hukunce-Hukuncen Jinin Haila da na Biƙi danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Duhun Kan Mace Mai Gaba da Kisihiya. danna nan.

  • Abin da Bincike Ya Gano Game Da Matsalolin Aure A Ƙasar Hausa

    Abin da Bincike Ya Gano Game Da Matsalolin Aure A Ƙasar Hausa

    Wannan bincike dai ya yi ƙoƙarin binciko wasu muhimman al’amura; game da wasu matsaloli da suka addabi gidajen mafi yawan Hausawa; inda binciken ya gano musabbabinsu ta amfani da wasu waƙoƙin Hausa na Situdiyo.

    Matsalolin Aure -Daga cikin abin da binciken ya gano, ya bayyana lalle akwai matsaloli a tsakanin ma’aurata a Ƙasar Hausa, sannan ya fayyace matsalolin ta hanyar amfani da zantukan mawaƙan baka na Situdiyo.

    Binciken dai ya gano yadda mawaƙan baka na Situdiyo suke taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma ta hanyar lalubo matsalolin da suka addabe su, da kuma bayyana su cikin hikimar zance irin tasu.

    Har wa yau, binciken ya nuna waƙa yalwatacciyar hanya ce ta isar da saƙo ba jefa nishaɗi kurum a tsakanin al’umma; ta yadda da ita za a iya gano matsalolin da suka dabaibaye al’umma; har ma a yi kirdadon hanyoyin magance matsalolin.

    Binciken dai ya ƙara tabbatar da cewa aikin waƙa; aiki ne na fasaha da bincike ta yadda ba haka kawai da ka ake yin waƙa ba; har sai an yi bincike yayin da ake son isar da wani saƙo; ko kuma yin ishara ko hannunka mai sanda ko kuma faɗakarwa a cikin waƙoƙin baka na Situdiyo.

    Wani babban abu kuma muhimmi da wannan binciken ya gano shi ne muhimmancin mawaƙa da kuma; ƙoƙarin taƙaituwa zuwa ga abin da suka faɗa a matsayin ita ce matsala ga wani rukuni na al’umma; ko wani abu da yake faruwa a tsakanin al’umma.

    To mawaƙa ma na iya tsinkayowa da kuma ayyana basirarsu wajen sanar da jama’a a waƙe.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Nazarin Matsalolin Aure A Ƙasar Hausa Daga Mahangar Zabiya Lawisa da Fatima Jalo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta bayani a kan Ma’anar Aure danna nan

    Domin karanta bayani akan Abin da Bincike Ya Gano Game Da Matsalolin Aure A Ƙasar Hausa danna nan

  • Haƙƙin Zaman Gidan Miji

    Haƙƙin Zaman Gidan Miji

    Tabbatar mace cikin gidan mijinta, doka ce tabbatacciya daga Allah Maɗaukaki, ga abin da Allah ya ce: “(ku mata) ku tabbata cikin gidajenku, kada ku bayyanar da adonku irin bayyanar da adon maguzancin farko”.

    Bisa dogaro da wannan ayar, haramun ne mace ta fita daga gidan mijinta ba tare da izininsa ba, ko da kuwa ta leƙa waje ne.

    Wannan ya sa wani ɗan uwa ya gargaɗi mata da cewa:
    Sai ta ukunsu gadangama kenan,
    Ba ta nufin gyara sai cuta.
    Ba ta nufin khairi ga mijinta,
    Ba ga kishiyoyi ba ga maƙotaba.
    Ba ta nufin gyara sai ɓarna,
    Sai duka safe ta cuci mijinta.
    Ya tafi ofis ko kuma kanti,
    Ba ta ƙara zama ɗakinta.
    In mai noma ne ko zage,
    Ka tafi gona zaure za ta.
    Tana neman ta ga masu wucewa,
    Wai ita dai suga kyan fuskarta.
    In taga sun ƙi shiga harkarta,
    Sai ka ji ta ce za ta maƙobta.

    Ayyukan Cikin Gida:

    Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas, Allah ya yarda da su, daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Dukkan ku makiyaya ne, kuma dukkan ku ababan tambaya ne game da abubuwan kiwonku,…. Mace ma makiyayiya ce a kan gidan mijinta da ‘ya’yansa, kuma ita ma abar tambaya ce game da abubuwan kiwonta”.
    Sannan an karɓo hadisi daga Asma’u ‘yar Abubakar Siddik, Allah ya yarda da su ta ce: “Na kasance ina yi yiwa zubairu (mijina) hidindimun gida baki ɗaya, kuma ya kasance yana da wani doki da nake wahala da shi, ina yi masa ciyawa kuma ina kula da shi”. Iman Ahmad ne ya rawaito shi.
    A wata ruwayar kuma (Asma’u) ta ƙara da cewa, tana ɗinke guga, da kwaɓa gari. Ahmad ne ya rawaito shi.
    Sannan kuma dai an karɓo hadisi daga Aliyu, Allah ya yarda da shi, ya ce, haƙiƙa matarsa Faɗima da ta sami labarin an kawo wa Annabi (Tsira da amincin Allah ya su tabbata a gare shi) bayi, sai ta je gida domin ta koka wa Annabi (tsiri da amincin Allah su tabbata a gare shi) game da kantar da hannunnta yake yi a sakamakon amfani da dutsen niƙa (ko ya agaje ta da baiwa), da ba ta sami Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a gida ba, sai ta gaya wa A’isha (R.A), da Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya dawo, sai A’isha ta faɗa masa saƙon Faɗima, sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tafi gidan ‘yarsa Faɗima; ko da ya isa sai ya tarar da ita da mijinta Aliyu (R.A) Sun riga sun kwanta bacci, da suka yunƙura za su ta shi domin taro shi, sai ya ce da su, “Ku yi zamanku a inda kuke’. Sannan sai ya zauna kuma ya ce da su: “Ashe ba na sanar daku abin da ya fi wanda kuka tambaya ba, idan za ku kwanta bacci ku yi tasbihi talatin da uku, hamdala talatin da uku, takbir kuma sau talatin da huɗu”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
    Duba da waɗannan dalilai da wasunsu ne wasu daga cikin malamai suka yanke hukuncin cewa: ɗaukar ɗawainiyar aikace-aikacen da suka shafi cikin gida nauyi ne da ya rataya a wuyan matar aure. Ko da yake ba laifi ba ne a shari’ance ga wanda yake da iko ya samo wa matarsa ‘yar aiki, sai dai fa ba ita ba samun ladan da ake ba wa waɗanda suka tsayu da kansu domin aiwatar da waɗannan ayyuka na cikin gidayaku ‘yan uwa mata!

    ku sani fa ba ƙasƙanci ba ne ku tsayu da:

     Ba wa dabbobin miji abinci da kuma share garkensu.
     Wanke banɗaki.
     Sharar tsakar gida.
     Dafa abinci.
     Gyara shimfiɗa.
    Da sauran su.
    Waɗannan abubuwa dukkan su share fagen shiga Aljanna ne, shi ya sa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da sahabbansa ba su goyi bayan ‘ya’yansu da matansu su yi watsi ko sakaci da su ba. Wannan kenan.

    Kula Da Abubuwa Mallakar Miji:

    Tabbas ne dukkan wasu abubuwa mallakar miji da suka haɗar da kuɗinsa, abincinsa, kadarorinsa, kayan aiwatar da sana’arsa da dai sauran su; kowanne yana ɗaya daga cikin abubuwan da Allah zai tambayi mace game da su a lahira. Don haka da mai kulawa, da mai banzatarwa, da mai sacewa, duk za su amsa tambayar Allah ba fasawa.

    Hana Wanin Miji Shiga Gidan Miji

    Ya inganta cikin bayanan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a hajjinsa ta ban-kwana ya ce: “Haƙiƙa maza kuna da haƙƙi a kan mata, na kada su kuskura su yi izinin shiga gidajenku ga wanda ba kwa so ya shigar muku gida, kuma kada su bar wani ya hau muku shimfiɗa alhali ba kwa so”. Muslim ne ya rawaito shi, kuma an karɓo shi ne daga sahabin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) wato Jabir, Allah ya yarda da shi.
    Kuma an karɓo daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi ya ce: “Haƙiƙa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya ce: “Ba ya halatta wata mace ta yi izinin shiga gidan mijinta, sai da izininsa”. Bukhari ne ya rawaito shi.

    Neman Izinin Miji Dan Yin Azumin Nafila:

    Bukhari,Muslim, Abu Dawud, Nasa’I da wasun su, sun rawaito hadisi da aka karɓo daga Abu Huraira (R.A) Ya ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Bai halatta ba mace ta yi azumi mijinta na nan a gari in ba Azumin Ramadan ba”.
    Sannan kuma ko azumin Ramadan ɗin, in dai na ramuwa ne, bai halatta mace ta yi shi ba har sai ta sanar da mijinta, ta nemi izininsa saboda yalwar kwanakin da take dasu game da ramuwar Azumin da ake bin ta ɗin.

    Neman Izinin Miji A Lokacin Buƙatar Fita:

    A zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da zazzaɓi ya tsananta ga matarsa A’isha (R.A) a dalilin ƙagen zina da aka yi mata, ta nemi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da ya yi mata izinin tafiya gidansu, domin ta sami tabbacin shin abin da ake faɗa game da ita ya isa kunnen iyayenta kuwa? Don kuma ta dace da samun lallashin mahaifanta da tausayawarsu. Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi mata izini ta tafi gida…”. Sahihul Bukhari, hadisi na (4750).

    Godiya Da Yaba wa Miji:

    Yana daga cikin kyawawan halayen Musulmi ƙwarai ya zama mai yin tukuici da godiya da yabawa kan abin kirkin da aka yi ma.
    Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda ya yi muku abin kirki, to ku yi masa tukuici, idan ba ku sami abin yi masa tukuici ba, to ku yi masa addu’a, har sai kun ga cewa kun saka masa (wato da yin addu’ar)”.
    A wata ruwayar kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) cewa ya yi: “Duk wanda aka yi masa abin kirki, sai ya ce da wanda ya yi masa kirkin, Allah ya saka maka da alheri, to haƙiƙa ya kai matuƙa wajen yabawa”. Tirmizi, Nisa’I da Ɗabarani ne suka rawaito shi.
    To ‘yar albarka yi da gaske ki yi aiki da wannan koyarwa ta Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ki yaba wa mijinki game da ɗumbin alherin da yake yi miki, sai ki rabauta da kyakkyawan sakamakon Allah (S.W.T), kuma ki ƙara kima da daraja a wajen mijinki, sannan kuma ki kubuta daga faɗawa cikin jerin mata butulai waɗanda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce da ire-iren su Allah baya duban matar da ba ta gode wa mijinta, alhali ba za ta iya wadatuwa daga shi ba”. Nasa’I ne ya rawaito.
    Kuma an karɓo shi ne daga Abdullahi ɗan Amr(R.A) wani ƙarin abin ban tsoro ita wannan ta’ada ta butulci ita ce sanadiyyar yawaitar mata a cikin wuta kamar yadda ya tabbata a hadisin da aka karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (R.A), daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Na hangi cikin wuta, ban taɓa ganin abin ban tsoro ba irin na yau, kuma na ga mafi yawaicin ‘yan cikinta mata ne. Sahabbai suka ce: “Me yasa ya Manzon Allah? Ya ce: “Saboda suna butulcewa”. Aka ce Allah suke butulcewa?ya ce: “Miji suke butulcewa, kuma suna da butulcewa kyautatawa, da za ka kyautatawa ɗayarsu tsawon shekara, sannan ta ga wani abin da bai mata daɗi ba daga gare ka, sai ka ji ta ce: “Tun da take ba ka taɓa ganin wani alheri ba daga gare ka ba”. Bukhari ya rawaice shi. Hadisi mai lamba (5197).
    To ‘yar uwa ki kiyayi cewa da mijinki me ya taɓa tsinana miki? kin dai ji irin abin da faɗar hakan ke jawowa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nauye-nauyen Rayuwar aure danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Cikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Da su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe

    Cikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Da su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe

    (1) Samuwar Amincewar Waɗanda za a Ɗaurawa Aure:

    A shari’ance, aure ba ya zama zartacce, abin la’akari da shi, sai idan an sami yardar ma’aurata da kuma amincewarsu.
    Dalili kuwa faɗar Allah Maɗaukakin sarki: “Ku auri abin da ya kwanta muku a rai daga matan (da suka halatta a gare ku), biyu-biyu ko uku-uku ko kuma hurhuɗu”.
    Da kuma hadisin da aka karɓo daga Ukbatu ɗan Amir (Allah ya yarda da shi) ya ce, “Haƙiƙa Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce: “Da wani mutum (da zai ɗaurawa aure ) ka yarda in aura maka wance? Sai ya ce: eh (na amince), sannan Annabi ya ce da matar: kin yarda in aura miki wane? Sai ta ce: eh (na yarda), Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ɗaura musu aure”. ( Baihaƙi da Hakim da wasun su ne suka rawaito shi ).
    Kuma Abdullahi ɗan Abbas ( Allah ya yarda da shi ) yace: “Haƙiƙa, wata budurwa ta zo wajen Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ta ce: Babanta ya ɗaura mata aure ( Da wani ) ba don sonta ba ( nan take) sai Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ba ta zaɓin idan ta amince da wanda aka aura mata, auren ya ɗauru, idan kuma ba ta son sa, to auren bai ɗauru ba”. ( Ahmad da Abu Dawud da wasun su ne suka rawaito shi).
    Sannan an karɓo daga khansa’u ‘yar Khidan ( Allah ya yarda da ita ) Cewa: Mahaifita ya ɗaura mata aure da wani tana bazawara ba don son ta ba, sai ta je ta shaida wa Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) sai ya ce : “Auren bai ɗauru ba”. ( Bukhari ne ya rawaito shi ).

    (2) Waliyyin Matar da za a Aura:

    Waliyyi shi ne mutumin da alhakin aurar da mace yake wuyansa, kamar uba, ko madadinsa, ko shugaban Musulmai.
    Waliyyi ma sharadi ne daga sharuɗɗan da sai da su aure yake ɗauruwa a Musulunce.
    Saboda haka, bai halatta mace ta aurar da mace ba, kamar yadda bai halatta mace ta yi gaban kanta ta aurar da kanta ga wani ba.
    An karbo daga Abu Huraira ( Allah ya yarda da shi ) ya ce: “Manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce : “Mace ba ta aurar da mace, haka kuma mace ba ta aurar da kanta”. ( Ibn Majah ne ya rawaito shi ).
    Kuma an karbo daga Ikrima da Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya yarda da su) sun ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Babu aure sai da waliyyi”.
    Sannan kuma an karbo daga A’isha ( Allah ya yarda da ita ) ta ce: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce: “Duk matar da ta yi aure ba da izinin waliyyinta ba, auren ɓatacce ne,. Idan kuma wanda ya aure ta a kan hakan, har ya sadu da ita to, ya ba ta sadakinta, saboda saduwar da ya yi da ita. Idan kuwa mace da waliyyinta suka saɓa, to, shugaban musulmai shi ne waliyyin duk wacce ba ta da waliyyi”. ( Abu Dawuda da Ibn Majah ne suka rawaito shi).

    (3) Shaidu:

    Su kuwa shaidu su ne, adalan mutanen da suke halartar gurin ɗaurin aure, su kuma kasance a gurin a lokacin da za a ɗaura auren.
    A Musulunce, mutane biyu su ne mafi ƙarancin shaidu game da ɗaurin aure. Saboda hadisin da aka karɓo daga Imran ɗan Husaini, da A’isha ( Allah ya yarda dasu ) cewa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ” Babu aure sai da waliyyi da kuma shaidu biyu adalai”. ( Imam Ahmad ne ya rawaito shi ).

    Amfanin Samar da Shaidu a Aure:

    Yana daga cikin amfanin da samar da shaidu yake da shi:
    1. Kawar da zargin zina, ko daduro tsakanin ma’aurata.
    2. Hana a kira ‘ya’yan da mutum ya haifa ‘ya’yan zina (shegu).

    (4) Sadaki:

    Sadaki shi ne dukiyar aure, wacce mace take cancantarsa daga wajen miji ta dalilin aure. Saboda faɗar Allah Maɗaukaki:
    “kubawa mata sadakinsu cikin daɗin rai, idan kuma suka sayar muku da wani abu daga cikinsa da sonsu (don kansu), to, ku ci shi (halak malak ) rai kwance”.
    Da kuma faɗar Allah maɗaukaki:” To, waɗanda ku ka ji daɗi da su daga cikinsu (mata) ku ba su sadakinsu (cikakke) tilas”.
    Sannan kuma Allah cikin hikimarsa ya yi bayinsa bai yi su bai ɗaya ba, don haka ma, da ya wajabta musu bayar da sadaki, sai bai iyakance musu shi ba. Saboda ya dace da mai hali da kuma mai ƙaramin ƙarfi. Kowanne gwargwadon halinsa.
    Don haka, a Musulunce ya halatta mutumin da yake da hali ya dunƙule wasu maƙudan kuɗi ya bayar a matsayin sadakin matar da zai aura. Allah Maɗaukaki ya ce : ” Idan ku ka yi nufin musanya wata mace a maimakon wata (da kuka saka) alhali kuwa da kun ba wa dayarsu ( ta farkon ) dukiya mai ɗimbin yawa (a matsayin sadakinta ), to , kada ku karbi komai daga cikinsa, shin kwa karbe shi don zalunci da saɓo mabayyani”.
    Sai dai kuma mafi falalar sadaki shi ne wanda bayaninsa ya zo kamar haka:
    An karɓo daga Ukbatu ɗan Amir (Allah ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) “Ya aura wa wani mutum mace a kan sadakin zobe na ƙarfe”. (Hakim ne yarawaito shi).
    Bayan haka kuma, shi sadaki haƙƙi ne na matar da aka aura, kamar dai yadda bayani ya gabata. Saboda haka, bai halatta ba ga waninta ya ci wani abu daga cikinsa, sai dai inda izininta.
    To bayan kammalar bayanin waɗannan abubuwa da muka ji, ana so a lokacin da za a gudanar da ɗaurin aure a kwaikwayi Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) a rigayi ɗaurin auren da gabatar da wannan addu’ar kamar haka:
    An karbo daga Abdullahi ɗan Mas’ud ( Allah yayarda dashi ) Yace: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya koya mana yin ” Huɗubar Haja ” a lokacin ɗauren aure. Wato:
    “Innal hamdulillahi ta’ala, nahmadhu wanastagiynuhu, wanastagfiruhu, wa na’u’zu billahi min shuruwri anfusina wa min sayyi’a’ti a’a’malina, man yahdihil-llahu fala mudilla-lahu, waman yudlil fala hadiyaya lahu, wa’ashadu an lailahaillallahu wahdahu la shariyka lahu, wa’ashadu anna muhammadan abduhuwarasuluhu”.
    “Ya ayyuhal lazina a’manuttaƙuwllaha haƙƙa tuƙatuhi wala tamutunna illa wa antum muslimun (Al-i-mran, aya ta (102)
    Ya ayyuhannasu-ttaƙuw rabbakumullazhiy kalaƙakum min nafsin wahida wakalaƙa minha zaujaha wabassa minhuma rajalan kasiran wa nisa’a’wattaƙuwllahal lazhiy tasa’a’luna bihi wal’arhama innallaha kana alaikum raƙiyba” (An nisa’i aya (1)
    “Ya ayyuhal-lazhina ‘a’manuttaƙuw-llaha wa ƙulu ƙaulan sadhidhan yuslih lakum a’a’malakum wa yagfir lakum zhunubakum waman yuɗi’illaha wa rasuluhu faƙad faza fauzan a’zhima (Al Ahzab aya,
    Abu Dawud, da Nisa’i da wasunsu ne suka rawaito shi.
    Sannan kuma ya halatta bayan gama ɗaura aure, ranar a kai amarya gidan miji, a buga dundufa domin sanar da aure da kuma faranta ran ango. Amma bai halatta ayi dauraba.

    Ranar Haɗuwar Ango Da Amarya:

    A Musulunce ana so ranar da ango ya fara haɗuwa da amaryarsa ko kuma ranar da aka kawo wa ango matarsa gidansa, ya yi ƙoƙarin yin waɗannan abubuwa masu zuwa kamar haka:
    (1) Ango ya jagoranci matarsa su yi sallah raka’a biyu- nafila don miƙa godiyarsa ga Allah da ya cika musu burinsu kamar yadda Ibn Abi Shaiba ya rawaito.

    (2) Ya ɗora hannunsa a kan goshin matarsa, wato ya karanta ya riƙe, sannan kuma ya karanta wannan addu’a kamar haka:” Ya Allah ina roƙon ka alherin wannan mata da alherin da ka halicceta a kansa, kuma ina neman tsarin ka daga sharrinta da sharrin abin da ka halicce ta a kansa”. ( Bukhari a cikin littafinsa da Abu Dawuda da Ibn Majah da wasunsu ne suka rawaito shi ).

    (3) Gabatarwa da amarya wani ɗan abin kusa da baka, kamar yadda Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) ya yi wa matarsa A’isha (Allah ya yarda da ita ).

    (4) Goge baki kafin kwantawa da amarya, domin kawar da wani hamami, ko wari da ka iya tashi daga cikin baki. Kamar yadda aka samu Muslim da Abu Awana sun rawaito Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya yi haka.

    (5) Yin addu’ar saduwa da mace, kafin fara saduwa da ita. Addu’ar kuwa ita ce: “Ya Allah ka nesan ta ni daga shaiɗan ka kuma nesan ta shidan daga abin da ka azurta ni da shi”.
    Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce: Idan Allah ya hukunta wa miji da matarsa samun ɗa a saduwar da suka karanta wannan addu’ar, to, shaiɗan ba zai cutar da ɗan da suka samu ba har abada”. (Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ).

    (6) Yin walima da abin da Allah ya hore, bayan tarewa da saduwa da amarya. Saboda aiwatarwar Annabi da kuma umarnin da ya yi na ayi walima.
    Sannan kuma idan za a kira jama’a walima, to a yi kokarin ganin an tara waɗanda suke mabuƙata, saboda Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) yana cewa: “Mafi sharrin abinci walima, wanda ake kiran (ko gayyatar) mawadata a ƙyale mabuƙata “. ( wato a ki gayyatarsu ). ( Malik da Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ).
    Daga lokacin da Allah ya hukunta wa Musulmi aurar wata mace, ko kuma ya hukunta wa Musulma auren wani Musulmi, to ya zamar musu lallai su san cewa, a musulunce akwai wasu nauye-nauye da suke tattare da rayuwar da zasu fuskanta ta zaman aure, wadanda suka sha bamban dana irin rayuwar da suka faro a baya ta zaman kaɗaici.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nauye- Nauyen Rayuwar Aure danna koren rubutun nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.

  • Haƙƙin Wanda Mutuwa Ta Raba Shi Da Abokin Zamansa Daga Cikin Ma’aurata

    Haƙƙin Wanda Mutuwa Ta Raba Shi Da Abokin Zamansa Daga Cikin Ma’aurata

    A Musulunce idan mutuwa ta raba tsakanin ma’aurata, to wanda yake raye cikinsu yana da haƙƙi daga cikin abin da wanda ya mutu ya bari.

    Idan mace ce ta mutu, ta bar mijinta, to mijin zai gaji rabin abin da matarsa ta mutu ta bari na abubuwan mallakarta, idan ba ta da ɗa a raye. Idan kuma tana da ɗa a raye, to mijin nata zai gaji ɗaya bisa huɗun abin da ta mutu ta bari ne. Allah (S.W.T) ya ce:
    “Kuma kuna da rabin abin matanku suka bari idan ba su da ɗa, amma idan suna da ɗa, to kuna da ɗaya bisa huɗu daga abin da suka bari, bayan (an zartar da) wasiyya da suka yi, ko kuma bashin dake kansu…”.
    Idan kuwa miji mutuwa ta ɗauke shi ta bar mata, to ita matar za ta yi wa mijin takaba, sannan kuma za ta gaji ɗaya bisa huɗun abin da ya bari idan ba shi da ɗa a raye, idan kuma yana da ɗa a raye, to za ta gaji ɗaya bisa takwas daga abin da mijinta ya mutu ya bari, wannan shi ne abin da mace ke gada daga miji ko da kuwa su nawa ya mutu ya bari a matsayin matansa.
    Allah (S.W.T) ya ce: “…su kuma (matan aure) suna da rabo ɗaya bisa huɗu na abin da kuka bari idan ba su da ɗa. Amma idan kuna da ɗa, to suna da ɗaya bisa takwas daga abin da kuka bari bayan (an zartar da wasiyya da kuka yi, ko wani bashi dake kanku…”.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Ma’anar Aure

    Ma’anar Aure

    Aure wani haɗi ne da ake yin sa tsakanin namiji da matar da ta halatta da aure a gare shi, bayan amincewar su da juna, domin tabbatar da halaccin gudanar da cuɗanya a tsakaninsu, da kuma biya wa junansu buƙatar sha’awa, ba tare da an sami wani zargi ba.

    Abubuwan Da Sai da Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe:

    A musulunce aure na tabbata ne da tabbatar waɗannan abubuwa masu zuwa kamar haka:
    1. Samuwar amincewar waɗanda za a ɗaurawa aure.
    2. Waliyyin matar da za a aura.
    3. Shaidu.
    4. Sadaki.
    5. Siga. (wato maganganun da aure yake ɗauruwa da su), kamar mai neman ya ce da waliyyin mace: ‘Ina neman auren wance’. Sai shi kuma waliyyin ya ce: ‘Na aura maka ita.

    Domin karanta cikakken bayanin abubuwan da sai da su aure yake zama karɓaɓɓe danna koren rubutun nan.

    Wannan bayani an ciro ne da littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi. domin karanta cikakken littafin danna wannan koren rubutun.