Tag: ilimin aure
-

Inganta Rayuwar Ma’aurata Ta Hanyar Karin Magana
INGANTA RAYUWAR MA’AURATA TA HANYAR AMFANI DA KARIN MAGANA
2.YANZU YANZU SAI ALLAH.
3. BA A ƁARI A KWASHE DAIDAI.
4.HANA WANI, HANA KAI
5.ALLAH ƊAYA GARI BAMBAN
-

Yadda Za Ki Yi Wa Namiji Mai Shiru-shiru
Wani Namijin halitta ce shiru-shirunsa. Ba damar canja shi. Ba zai miki hira ba, kuma ba zai saurari hirarki ba.
Sai ki yi nazari ki fahimci ke kadaice ba yawa hira? Ko ke kaɗai ce bai damu da ya saurara ba?
Idan a ko’ina ma haka yake, ba ya son magana. Sai ki yi haƙuri. Rashin miki hira ba zai hana ki samun rahamar Allah ba.
Sai ki daina kallo da damun kanki a kan hirarsa.
Ki mayar da hankalinki a kan sauran halayensa na kirki. Abubuwa da yawa waɗanda wasu matan da yawa ba su samu ba. Ke kina samu , Kuma ki gode wa Allah .
IDAN MIJINKI MAI MAGANA NE.
Idan mai magana ne, ke ce kaɗai ba ya son yi da ke?
Na farko ki koma ga Allah wajen yawaita istigfari.
Na biyu ki yi ta nacin addu’a .Tashi ƙiyamul layl a kan Allah ya warware miki matsalarki.
Na uku: ki yi tunani daga wajenki za a samu gyaran ko kuma daga wajensa ne?
Wato ko ba ki fahimci irin hirar da ya fi so ba?
Ki yi nazarin rayuwarsa. Misali :
Mai son labarai: Kullum yana karanta jarida. sai ki rinƙa karanta jaridu, da sauraron labarai a radiyo.
Idan kun zauna, sai ki fara ba shi sabbin labaran wannan rana .Mai kiwon kaji ne, sai ki karanci ire-iren kaji da abincinsu, da magungunansu.
Ɗan Kwallo: Sai kin karanci ƙungiyoyin ball. Da labaran ‘yan ƙwallo da suke tashe a yanzu.
A ƙarshe dai yana da muhimmanci mace ta karanci irin sana’ar mijinta. Da mafi yawan abubuwa da suka shafi mijinta. Hatta labarin rayuwarsa . Zai taimaka sosai wajen rage yawaita matsaloli.
Wallahu A’alam .Domin karanta yadda ake da mai gida lokacin al’ada ko yadda ake shagwaɓa mai gida lokacin hutu
-

Yadda Za Ki Koya wa Mijinki Ko Matarka Wasanni
Yadda Za Ki Koya wa Mijinki Ko Matarka Wasanni Wasannin ma’aurata Iri-iri ne. Suna ƙara danƙon soyayya da samun biyan buƙata. Suna sa biyayya har ma da mallaka
Rashin su kuwa, na sa ɗaya daga cikin ma’aurata ya zauna cikin sha’awa, da ƙunci, da rashin natsuwa, har ma ya kai ga ƙiyayya. Ko ma rabuwar ma’aurata.
Ire-iren wasannin sun haɗa da shafa wasu sassan jiki a hankali. Yin sumba (Kiss) na laɓɓa, da runguma , da yin amfani da baki/harshe a wasu sassan jiki. Da hura iska a kunne. Da dai sauransu.
Amma fa runguma da sumbata ba za su yiwu ba. Sai dai da wanka, wanke baki da fesa turare. Idan miji/ ko mata ta ji kana wari. Za ka ga kawai tana ƙin kusantar ka, balle wasanni.
Idan aka jarrabe ki da mijin da bai iya wasa ba. Ko matar da ba ta iya wasa ba. To yakan sa a ji an gaji da juna.
HANYOYIN KOYAR DA WASANNI
1- Ban da ɓata rai, da ƙorafi , da nunawa wanda ba ya wasan shi/ ita ‘yar ƙauye ce.
2- Kai/ke mai koyar da wasan zai fara ne da maganganu masu gayyato sha’awar mijinki. Da yaba masa yana burge ki a shimfiɗa ko da ba hakan ba ne kuwa.
3 – Mai koyarwar ya dinga ɗauko hannun miji/ mata yana sa wa a inda yake so a jikinsa. Domin shafa…
4 – Ki kai abin da kike so ga bakin mijinki. Kai ma ka kai abin da kake so ga bakinta..
5 – Ba da labarin irin daɗin da ake ji idan akai miki/maka abu kaza.
6 – Bayar da umarni, amma fa cikin lumshe ido da sigar buguwa/maye na kalar wasan da ake so ga mijinki ko matarka. Kallon wannan yanayin naka, zai sa nan da nan a yi abin da aka umarta.
Zai fi kyau ga ma’aurata ma a kowanne lokaci za ku rabu, ko ku ka haɗu. To a fara da sumbatar juna.
Nana Aisha ta ce: “Manzon Allah (S.A.W) yana sumbatar matarsa idan zai fita. (Abu-Dawud).A ƙarshe ya zama tilas ga ma’aurata, su kula da gabatar da wasanni kafin shimfiɗa. Domin da yawa ma’aurata ba sa samun gamsuwa in babu wasanni. Hakan na haifar da matsaloli da yawa ga su Ma’aurata.
Wallahu A’alamDomin karanta yadda ake maraba da maigida ko yadda ake da maigida lokacin al’ada
-

Ladubba Zaman Ma’aurata
RAYUWA A KAN MANUFA
Rayuwa ba manufa, rayuwa ce marar ɗanɗano. Matuƙar ma’aurata sun haɗu a kan manufa ɗaya, za su rayu ne a kan wannan manufar, amma in aka yi rashin dace, yadda miji yake kallon al’amura da bambanci da nahiyar da ita take kallo, toh! a nan tushen saɓani yake.
In dai manufa kuwa za ta bambanta, hanyoyin isa ga manufar ma za su bambanta. A wannan yanayi saɓani da cin karo zai dabaibaye zamantakewar aure, saboda ba a kan manufa ɗaya ake tafiya ba.
Duk kammalallen mutum yana samun nasara ne saboda ɗabi’ar tsayuwa a kan manufa. A cikin manufar samar da ɗan Adam za mu iya fahimtar gamammiyar manufar aure.
Hajiya amarya manufarku ta farko ta kasance zaman ibada da neman yardar Allah, ba al’ada ba.
Akwai keɓantacciyar manufar aure nau’ika biyu; Asliyyah; Kiyaye wanzuwar jinsin ɗan Adam. Sai kuma Taba’iyya sauran manufofi da mutum ya ƙudura a ransa, a matsayin manufar da ta motsa shi ya yi aure; haihuwa, kamewa daga sha’awa, biyan buƙatar ɗabi’a, godewa ni’imar Allah da sauransu.
Ma’auratan da suka gina zamantakewar aurensu a kan manufa ingantacciya, sun fi kusa da jin tsoron Allah wajen kulawa da haƙƙoƙin junansu, kuma aure ya fi albarka.
SOYAYYA, AMANA DA KULAWA
Soyayya, amana da kulawa su ne manyan sirrukan ɗorewar zamantakewar ma’aurata, cikin aminci da amintarwa. Alƙur’ani mai girma ya ba mu wasu ƙa’idoji guda uku, assakan, al-mawadda, ar-rahma domin samun ingantacciyar zamantakewar aure mai haifar da kyakkyawar makoma.
Yaren soyayya guda biyar su ne; kyauta, bada lokaci (kulawa), hidimtawa juna, yabawa juna da kuma haɗuwar gangan jiki.
Ummul Mu’uminina Radiyallahu anha tana bayanin yadda fiyayyen halitta salawaatu Rabbiy wa salaamuhu alaihi yake rayuwar soyayya da iyalansa, hatta fita sallah in zai yi, yakan sumbace su domin rayar da ruhin ƙauna.
Tsarkakakkiyar soyayya mai asali tana ƙunshe da kulawa ta musamman, binciken zamani ya tabbatar da cewa kulawa ta musamman da fahimtar juna, su ne mafi girman abin da yake gaggawar mallake zuciyar abokin zama. Akwai mabambantan hanyoyi na nunawa juna soyayya a zamanance
KYAKKYAWAR MU’AMALA
Ma’aurata za su mu’amalanci junansu da mafi kyawun mu’amala “Wa ashiruuhunna bil Ma’aruf “, “Wa lahunna misthlul Laziy alaihinna bil Ma’aruf” su taimaka wa junansu wajen biyayya ga Allah Jalla wa alaa da Manzonsa.
Akwai fuskoki masu yawa da zasu bamu misalai na yadda shugabanmu abin koyinmu sallallahu alaihi wa sallam yake kyakkyawar mu’amala ta ƙoli da iyalansa, ya ba su yalwataccen lokaci, ya nuna musu ƙauna da soyayya, su yi raha, wanka, hira duk tare, ya taya su aikin gida, yana musu gyara cikin sauƙi, hikima da azanci ya kuma nuna kishinsa gare su.
Hajiya amarya ki faranta masa ta kowace fuska, ki girmama shi, ki gabatar da buƙatunsa a kan kowa, ki girmama ra’ayi da karɓar shawararsa a muhallin da ya dace, ki kasance mai nutsuwa da bin komai a tsanaki, tuna masa tsare-tsarensa na rayuwa, ki nemo dubarun kwantar da hankalin his excellency yayin fushi, ɓacin rai ko wata musiba.
Masu hikima sun tattare sirrin samun sa’adar zamantakewar aure a Khamsah Taa’aat da ya kamata a samu zaman tare; at-Tafaahum, at-Tasaamuh, at-Tafaa’ul, at-Tazayyun, at-Tajaddud
TAUSAYI, RAHMA, SAUƘI DA SAUƘAƘAWA
Waɗannan dunƙulallun halaye jigo ne mai ƙarfi da yake rike zaman tare, wanda ake buƙatarsa ga dukkan ɓangarorin biyu, domin wannan jigo yana biyo bayan tsaftatacciyar ƙauna da take zukatan ma’aurata. Annabin rahma sallallahu alaihi wa sallam ya yi gamammiyar wasiyya a kan a riƙe mata da alkhairi cikin kyautatawa a kowanne yanayi na mu’amala da su, kuma a aikace za mu ga gaba ɗayan rayuwarsa tana fassara ludufi da bin zamantakewarsa da su sannu-sannu.
“Istausuu bin nisaa’I khairan fa’innal mar’ata khuliqna min dwala’in a’awaj. Wa inna a’awaju ma fid dala’i a’alaahu”
Imam an-Nawawiy (Allah ya masa rahma) ya ce: “A cikin wannan akwai kira ga laɗɗafawa mata da kyautata musu, haƙuri a kan karkatar ɗabi’arsu da haƙurin juriya a kan raunin hankulansu”
Shaykh AbdulAziz Ibnu Baaz (Allah ya masa rahma) yana cewa: “Wannan umarni ne ga mazaje, iyaye, ‘yan uwa da wasunsu a kan su kyautata mu’amala ga jinsin mata, kada su zalunce su, su ba su haƙƙoƙinsu, sannan su fuskantar da su zuwa alkhairi”19
Ku sani saɓani ɗabi’a ce ta ɗan Adam, duk cikar mutum yana kuskure, duk kamalarsa ta ilmi, addini, wayewa ko fahimtar rayuwa ta mutum ɗan adamtaka tana gitta masa. Idan yadda saɓani ya gitta, al’amura sun rikice, ki gayyato nutsuwa zuciyarki, kar ki zartar da hukunci yayin fushi, ki tuno 90/10 rules kada ki nemi saki, ba fita yaji, kar ki fasa yi masa ɗa’a, domin daman don Allah kike, kada kuma ki kai ƙararsa wajen iyaye, ki koma ga Allah, ki yi alwalla ki yi sallah raka’a biyu, kiyi addu’o’i a ciki. Sannan daga baya, ki bi matakan da suka dace, Allah ya taimaka ya kuma rufa asiri-
RUFEWA
Kiyaye ladubban zamantakewar aure shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti da ci gaba wanda akasin haka zai jefa al’umma cikin mummunar makoma. Allah Jalla wa alaa ya kiyaye. Dr. Muhammad Sani Umar yana cewa:“Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida.
Idan miji da mata suka samu haɗa kansu bisa turba ta Musulunci, to sai ka samu ‘ya’yansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba a kan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.
Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.
Subhanakallahumma wa bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.
karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautar ki ko ladubban tarewa a gidan miji ko Muhimmancin Aure a rayuwa domin sauki cekakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu
-

Wannan Shi Ne Miji Nagari
Duk wani miji a duniya yana so da neman mace tagari wacce a idonta akwai tausayawa, a wajenta akwai hutu da nutsuwa, a zuciyarta akwai so da ƙauna, kamar yadda shi ma yake siffantuwa da siffofin nagarta.
- Miji nagari shi ne mai tsoron Allah a cikin maganganunsa da ayyukansa, yana taimaka wa iyalansa wajen samar da asalin tushen ƙauna, nutsuwa da girmamawa, wanda a kansu Musulunci ya gina zamantakewar aure.
- Miji nagari shi ne wanda ya ɗauki Annabin Rahma sallallahu alaihi wa sallam abin koyin sa wajen kyautata mu’amala da iyalai, taya su aikin gida, ɗebe musu kewa, sanya farin ciki da annashuwa a zuciyarsu tare da kauda kai daga rauni da rangwamen tunaninsu.
- Miji nagari yana sauraron matarsa, ya fahimci damuwa da buƙatunta ya kuma baza tunani da ƙwarewarsa wajen magance matsaloli da damuwar farin cikin ransa.
- Miji nagari yana riƙon matarsa a matsayin abokiyar rayuwarsa, rabin addininsa, mahaifiyar ‘ya’yansa, yana nuna mata ƙauna, kulawa da girmamawa, tare da ƙarfafa mata gwuiwa wajen ayyukan alkhairi.
- Miji nagari yana bai wa matarsa lokaci, tare da tantance tsakanin haƙƙoƙin mahaifiya da na matarsa. Mahaifiya: ƙauna, girmamawa da biyayya. Mata: ƙauna, girmamawa da tausayawa.
- Matuƙar an samu mace tagari a gidan miji nagari, hakan zai ba su damar zama da rayuwa tagari, tare da samar da zuri’a tagari wacce Annabin Rahma sallallahu alaihi wa sallam zai yi alfahari da ita. Allah Jalla wa Alaa yana cewa:
“Wal baladud dayyibu yakhruju nabaatuhu bi izni Rabbihi wallazi khabutha laa yakhruju illa nakida…” 6
RUFEWA
Kiyaye ladubban zamantakewar aure shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon, shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti, da ci gaba wanda akasin haka, zai jefa al’umma cikin mummunar makoma, Allah Jalla wa Alaa ya kiyaye. Dr. Muhammad Sani Umar yana cewa:“Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana, domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida.
Idan miji da mata suka sami haɗa kansu bisa turba ta Musulunci, to sai ka samu ‘ya’yansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya. To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba a kan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.
Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.
Subhanakallahumma wa bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.
karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki ko ladubban tarewa a gidan miji ko Muhimmancin Aure a rayuwa domin sauke cikakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutun nan
-

Wannan Ita Ce Mace Tagari
Gidan miji masarauta ce ga mace, shi yasa mace tagari ke sarrafa dukkan abin da ta mallaka na ilmi, hankali, wayewa da ƙwarewar rayuwa, ba domin komai ba, sai don ganin ta mayar da masarautarta aljannar duniya wajen kwanciyar hankali, more rayuwa da cikakkiyar nutsuwa ga uban ‘ya’yanta.
- Mace tagari ita ce wacce ta yi fice da ƙwarewa tare da yauƙaƙa soyayyarta wajen inganta bangorori 15 kamar haka:
- Iya kwalliya
- Girki, tarba
- Murmushi
- Magana
- Kallo
- Rakiya
- Kwanciya
- Hira
- Tafiya
- Raha
- Rarrashi
- Da kwantar da hankali.
2. Mace tagari a matakin farko tana kusantar mijinta ne domin ta fahimci ɗabi’u, halaye da buƙatunsa, domin ta san yadda za ta zauna da abinta.
3. Mace tagari babban burinta cika siffofin da Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam ya siffanta mace tagari da su. “Khairu nisaa’ikum allatiy izaa nazara ilaiha zaujaha sarrathu, wa in amaraha adaa’athu, wa izaa ghaaba anha hafizathu fi nafsiha wa maalihi’’4
4. Mace tagari tana zaman aure ne domin samun yardar Allah Jalla wa Alaa, lazimtar addu’o’i da kyautata ladubban tarbiyya ta addinin Musulunci a gidanta da ‘ya’yanta, ta na kiyaye ibadu da kamanta tsoron Allah jalla wa Alaa a dukkan al’amuranta.
5. Mace tagari tana fifita ilmi fiye da komai na rayuwarta, tana mayar da hankali a kan kyakkyawar rayuwar ilmi a cikin gidanta da yaranta domin samun albarka da hasken rayuwa.
RUFEWA
Kiyaye ladubban zamantakewar aure shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti da ci gaba wanda akasin haka zai jefa al’umma cikin mummunar makoma. Allah Jalla wa Alaa ya kiyaye. Dr. Muhammad Sani Umar yana cewa:
“Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana, domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida.
Idan miji da mata suka sami haɗa kansu bisa turba ta Musulunci, to sai ka samu ‘ya’yansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba a kan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.
Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.
Subhanakallahumma wa bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.
karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki ko ladubban tarewa a gidan miji ko Muhimmancin Aure a rayuwa domin sauke cikakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu
-

Muhimmancin Aure A Rayuwa
Aure shi ne ƙashin bayan dauwamar jinsin halittar ɗan Adam, dabbobi da tsirrai a bayan ƙasa, aure sutura ce ta aminci, nutsuwa, ci gaba, buɗi da kwanciyar hankali.
Aure garkuwa ne mai kare mutuncin mutum da rufa masa asiri, kuma hanya ce ta samun sa’ada a duniya. A taƙaice muhimmanci, fa’idoji da hikimomin da suke cikin rayuwar aure za mu iya kallonsu ta ɓangarori biyar;Ahmiyyatuz zawaaj al-Fardiyyah war ruhiyyah, ahmiyyatuz zawaaj al-Ijtima’iyyah, ahmiyyatuz zawaaj assihhiyyah, ahmiyyatuz zawaaj al-Iqtisadiyyah, ahmiyyatuz zawaaj as-siyasiyyah.
Wato muhimmancin aure a kan ruhi, zamantakewa, lafiyar jiki, tattalin arziƙi da siyasar shugabanci.
Shaykh Salih Fauzan (Allah ya masa rahma) ya ce: “Aure yana da fa’idoji masu yawa; kiyaye mutum daga laifukan jinsi
- Taƙaita musu kallon haram
- Samun zuri’a da kiyaye nasaba
- Samun nutsuwar ma’aurata da tabbatuwar amincin zuciya
- Taimakekeniyar ma’aurata ga junansu
- Gina nagartaccen iyali domin samun al’umma Musulmi tagari
- Samun sakamakon ibadar tsayuwa da al’amuran gida da sauransu.
RUFEWA
Kiyaye ladubban zamantakewar aure, shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti da ci gaba, wanda akasin haka zai jefa al’umma cikin mummunar makoma. Allah Jalla wa Alaa ya kiyaye. Dr. Muhammad Sani Umar yana cewa: “Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida. Idan miji da mata suka sami haɗa kansu bisa turba ta Musulunci, to sai ka samu ‘ya’yansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba a kan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.
Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.
Subhanakallahumma wa bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.
karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki ko ladubban tarewa a gidan miji domin sauki cikakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu
-

Ladubban Tarewa A Gidan Miji
A daren tarewa abubuwa guda goma sha ɗaya (11) ya kamata ma’aurata masu addini da wayewa su aikata:
- Addu’ar shiga gida
- Sallama
- Shigowa da abincin da ya dace
- Sallatar nafila raka’a biyu tare
- Karanta wannan addu’o’in
“Allahumma baarik liy fiy ahliy wa baarik lahum fiyya. Allahummaj ma’a bainana ma jama’ata bi khairin wa farriq bainana iza farraqta ila khairin” ko kuma “Allahumma baarik liy fiy ahliy wa baarik li ahli fiyya, Allahummar zuqhum minni warzuqni minhum, Allahummaj ma’a bainana ma jama’ata fi khairin wa farriq bainana iza farraqta fi khairin’’
6. Sannan ango ya kama goshin amaryarsa ya karanta
“Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi wa a’azu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi’’
7. Taƙaitacciyar hirar ɗebe kewa da soyayya
8. Su yi wanka da brush
9. Idan ba ta jinin al’ada a yi mu’amalar aure su karanta ‘Bismillahi, Allahumma jannabinas shaidan wa jannaibis shaidana ma razaqtana’’
10. Kiyaye ladubban mu’amalar aure
11. Bayan an gama a yi wanka ko alwalla kafin kwanciya.
Washegarin tarewa, ma’aurata suna zaunawa dogon lokaci domin meeting, su tattauna a kan yadda za su rayu har ƙarshen rayuwa cikin ƙauna da haɗin kai, a tsara gida da yadda zamantakewa za ta kasance, domin rayuwa ta ilmi, ƙauna da tausayawa, su fahimci manufofin juna da tsare-tsaren juna, tafiya a kan tsari shi ne asasin saurin isa ga manufa. Masu hikima na cewa “Zo mu zauna zo mu tsara”
RUFEWA
Kiyaye ladubban zamantakewar aure shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon, shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti da ci gaba, wanda akasin haka zai jefa al’umma cikin mummunar makoma. Allah jalla wa Alaa ya kiyaye. Dr. Muhammad Sani Umar ya na cewa: “Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida. Idan miji da mata suka sami hada kansu bisa turba ta musulunci to sai ka samu yayansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba akan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.
Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.
Subhanakallahumma wa bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.
karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki ko domin sauki cikakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu
-

Yadda Ake Shafa Jiki Na Musamman Ga Ma’aurata.
Shafa jiki yana inganta rayuwar ma’aurata. Domin abu ne dake isar da soyayya. Rashin sa kuma na kawo ƙiyayya da nesanta ma’aurata.
Kowanne mutum yana da abin da ya fi so. Ka so mafi yawa na mutane suna son a shafi jikinsu. Haɗa jiki na nuna ƙauna sosai.
Duba abin da Nana A’isha ( R.A) ke faɗa mana a ƙarshen hadisin nan.
A’isha (R.A) ta kasance tana cewa: “Ya mutu yana tsakanin saman kirjina da haɓata”.
(Bukhari da Muslim).Masana sun gano cewa: Jarirai da ake yawan ɗaukar su, da rungume su, da sumbatarsu. Sun fi koshin lafiya da walwala a rayuwarsu.
Shafa jiki ko ince haɗa jiki na sanya soyayya ta dinga tasiri. Ma’aurata mu saki jikinmu mu dinga hutawa tare. Ko za ka iya tuna sau nawa kake haɗa jikinka da na matarka? To in ba ka yi , sai ka fara. Ga wani kyakkyawan misali.
A’isha ta ce:” Annabi (SAW) ya na kishingiɗa a kan cinyata, Alhali ina haila, sai ya karanta Qur’ani“.
(Bukhari ).Ma’aurata da yawa kan ji sun shiga damuwa. Ba sa jin karsashi na soyayya. Ko auren ma ya zama kawai lallabawa ake yi. To yawan shafa hannu, runguma , sumba , kwanciya a jiki. Na farfado da soyayya ya rage damuwa.
Mata da yawa kan yi girke-girke, da kwalliyya, da gyara gida . Domin sanya farin ciki da jin daɗi ga miji. Amma sai ka ga duk ba ta burge mijinta ba. Wasu kaso na Mazaje sun fi ƙaunar a dinga tarairaya jikinsu sama da komai.
In kika haɗa waɗancan ayyuka da shafa jikinsu. To sai su ji ƙaunarki ta cika musu zuciya.
Haka ma wasu mata suke. Shafa jikinsu shi ne ya fi tabbatar musu da soyayya.
Ka tabbata matarka ta zama matashinka. Ka zama mai koyi da Annabi SAW.
HANYOYIN SHAFA JIKI
1 – Kwanciya a jikin Miji/ Mata. A kan ƙirjinsa, da cinyarsa , da kafadarsa.
Hadisi ne a babin taimama: … Wata rana A’isha (R.A) ta ɗora kan Annabi SAW a kan cinyarta, har ma Annabi ya yi barci. Sayyadina Abubakar ya zo yana zungurin ta. Amma sai ta ƙi motsi , Don gudun ka da ta katsewa Annabi ( SAW) barcinsa.2 – Zama a tare waje ɗaya. A tabarma ko a kujera. Jikinka na manne da jikin matarka.
3 -Riƙe hannuwa tare ana tafiya. Ko yayin da ake rakiya.
4 – Rungumar juna akai-akai ya zama ɗabi’ar Miji da Mata. Daga A’isha (R.A) ta ce:” AbdurRahman dan Abi bakarin Sidiq (R.A) ya shigo, a lokacin ina rungume da Annabi a ƙirjina, ….
5 – Sumbatar juna da yawa.
6 – Tausa nasa warwarewa ta gajiya. Kuma tana sanya jin daɗi .
7- Ana hira ana wasa da yatsun hannu.
8 – Wajen gyara wa mutum kayan da yasa. Ko goge masa datti.
9 – Shafa fuskar matarka tare da faɗin: Allah Ya miki kyau Matata.
1O – Shafa kitson matarka , ko shafa mata mai a kitso : Masha Allah kitso ya miki kyau.
Mace kuma ta dinga tajewa mijinta Gashinsa.Hadisi ne: Annabi SAW yana itikafi yana zuro kanshi. A’isha (R.A) tana wanke masa, ta taje masa shi.
11- Yi wa miji aski, da shafa Mai, da wankin kafa da dai sauransu.
A karshe dai Ma’aurata su karanci ɓangarorin jiki. Su gano wanda ya fi jin sako. Kuma ba lalle in da miji ya fi so. Ya zama shi ne matarsa ke jin sako ba. Sai ka tambayi matarka ɓangaren jikinta da ta fi so.
Shafa jiki na da muhimmanci sosai. Ya kamata ya zama mun saba da shi sosai. Domin tabbatar da ƙauna a tsakani Ma’aurata.
Dannan koren rubutu domin karanta yadda ake wankan soyayya ko yadda ake shagwaɓa maigida lokacin hutu
Litattafai da aka duba
Kitabu Tayammumi
Kitabul haidha
Babus swak
Mukhtasar Sahihul Bukhari.Physical touch
The 5 love languages
Gary ChapmanTasirin Soyayya
Amina Yusuf Gwamna -

Yadda Ake Ayyukan Gida Domin Taimakon Juna
Akwai wata sananniyar hanya da ma’aurata ke bi domin ƙara donƙon soyayyar aurensu. Ita ce taimaka wa juna a wajen ayyukan gida. Yadda gidansu zai kasance cikin tsafta da tsari a koda yaushe.
A wajen maza da yawa, kula musu da gida ya fi komai muhimmanci a gare su. Yin shara, da wanke-wanke , da girki da dai sauransu.
Aikata wannan shi ne mafi muhimmanci a wajensa. Kuma da shi ne zai zama kin mallake shi.
Shi yasa idan namiji mai ɗabi’ar son a yi masa hidima ne, yake son wacce duk kika ajiye ta a mai aiki. ƙanwarki ce ko mai aikatau ce.
Shi yasa komai gatan ki. To ki bambance irin ayyuka da za a yi miki. Da irin wanda ke da kanki za ki dinga yi wa mai gidanki.
Burge irin wannan miji shi ne ta hanyar aiki.
Wato shi ne yi wa mijinki hidima da kanki. Har ma ki ƙara da kyautatawa.Misali: Wanke masa ƙananan kayansa. Jallabiyya, da safa , da rigunan bacci.
Namiji na da kyakkyawan zato a kan matar da za ta kula masa da hidimar gidansa. Shi yasa namiji ba ya gamsuwa idan matarsa mai kasala ce. Sai yai ta ƙorafi , duk da irin kyawunta da kwalliyarta kuwa.
Yin hidimarta gare shi soyayya ce. Da kuma son kyautata masa.
To amma mene ne yake sanya wasu mata ƙyuiya. Ko kuma ince jin ganda. Har ma da masu jin ƙyashi. Wai don me zan ta aiki a cikin gidan nan ne?
Wata Matar ta taso cikin sakaci saboda dukiya. Ba ta komai a gidansu, ba ta iya aiki ba. Wata kuma ganin wadatar mijinta ne, ke sawa ta ƙi komai. Wata kuma mijin bai sayan ruwa, da omo, da sauransu. Dole ce ke sa ta bar gida da ƙazanta. Wata kuwa sai ta ce ma yadda mijinta ke tilastawa a yi ayyuka gida ba tausayi. Ta kan ji ya ɗauke ta tamkar baiwa. Wannan ke kashe mata karsashin ayyuka.
Mene ne kesa wasu yin aiki a gidan mijinsu, har ka ga tamkar ba sa gajiya?
Wata tana da ilmin addini, ta ɗauki dukkan hidimar gidanta a matsayin ibada. Tana duba irin matsayin Assayida Fadima (R.A) da yadda ta dinga hidima a gidanta, har hannunta na nunawa. Kuma Annabi (SAW) bai ba ta baiwa ba ,ya rarrashe ta da ta je ta cigaba da yi. Idan mace ta tuna wannan sai ta himmatu.
Yabawa ƙoƙarinta na ayyuka ne ke sa mata kwarin gwuiwa. Tai ta aiki ta ji kamar batirinta ya samu caji 60%.
Idan kuma ka shigo tana girki. Sai ɗanku ya tsala kuka. Sai ka ɗauke shi, ka sa shi a kafaɗa kana jijjigashi. Tana lekowa ka ce je ki ƙarasa aikinki. Sai ta ji batirinta ya samu cikakken caji 100%. Saboda a ɗabi’arta taimakonta ya fi komai muhimmanci.
Ka zama mai sauƙin kai, da kyautatawa matarka. Domin bin wasiyya da Annabi ( SAW) ya yi a kan Mata.
Annabi ( SAW) ya ce : Mafi cikar masu imani daga muminai, waɗanda suka fi kyawun ɗabi’a, sannan mafi alherinsu, su ne, waɗanda suka fi alheri ga matansu“.
(Tirmizi).A wani gida za ka tarar da mata, ta yi ma yara wanka (2/3) . Miji ne zai shafa musu mai da sa kaya. Ita kuma ta wuce madafa ( kitchen) tana shara da girka abin karyawa.
Kafin rufe wannan batu na taimakon juna da ayyuka na gida. Akwai wani taimako daban. Shi ne taimakon juna a kan ayyuka na ibada. Mace ta dinga amfani da hikima wajen zaburar da mijinta ibada.
Mace kuwa dama renonta ake da cigaba da tarbiyyarta. Ya zama wajibi ga miji ya jajirce domin ganin matarsa na yin duk abin da Allah Ya ɗora mata.
Yana ƙara wa namiji daraja. Kuma cika umarni Allah ne.
Allah Ya ce: Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku Kare wa kanku da iyalanku wata wuta makamashinta mutane da duwatsu ne. A kanta akwai waɗansu mala’iku masu kauri, masu ƙarfi. Ba su saɓa wa Allah ga Abin da Ya umarce su, kuma suna aikata abin da ake umarninsu”.
( Tahreem: 6)Annabi SAW ya ce: Allah ya jiƙan namijin da zai tashi cikin dare, ya tayar da matarsa don su yi sallah, ta ƙi tashi saboda barci sai ya shafa ma ta ruwa a fuska, har ta tashi, su ka yi sallah”.
( Abu Dawud)A ƙarshen yin ayyuka na gida domin taimako juna na dasa soyayya. Ta zama ƙatuwar bishiya har ta yi rassa. Ta ba da ‘ya’yan farin ciki da girmama juna.
Tausayi da taimakekeniya a aure na zaburar da Ma’aurata sosai.
domin kara fahimta zaman aure dannna koren rubutu yadda ake shafa jiki na Musamman ga Ma’aurata ko yadda ake shagwaɓa maigida lokacin hutu ko yadda zaki mayar da gidaki masarautar ki.Litattafai da aka duba:
Babul Wasiyyatu binnisa’i
Riyadus Salihina.Lacca:M. Bashir Abubakar Takai.
Act of Service
The 5 love languages
Gary Chapman.Abubuwa da ke sawa Mace ta Zamo mafi soyuwa a gurin mijinta.
Aure A MusulunciLove and Respect
Dr. Emerson Eggerichs.