Tag: abinsha

  • Yadda Ake Ice Cream Custard

    Yadda Ake Ice Cream Custard

    Ice cream custard ya kasance abin sha mai daɗi, mai sauƙin sarrafawa, ba tare da shan wahala ba, mafi yawanci ice cream custard ya fi soyuwa a wajen yara ƙanana.

    Abubuwan da ake bukata
    1. custard,
    2. madara,
    3. vanilla flavour,
    4. sugar.
    Yadda ake haɗawa,
    1. ki dama custard da ruwan sanyi ki sheƙa ma da na zafi, ya yi kamar koko,
    2. ki sa madara mai yawa a kai, da filabo da sugar, ki juya su sosai, su haɗe jikinsu,
    3. ki bar shi ya huce, ki sa a fridge ki bar shi har dai ya yi ƙanƙara.

    Domin sanin yadda boga ko biredin kwakwa danna nan

  • Yadda Ake Mojito Drink A Sauƙaƙe.

    Yadda Ake Mojito Drink A Sauƙaƙe.

    Yadda ake mojito drink

    Abubuwan haɗawa
    1. Mint leaf
    2. Ƙanƙara
    3. Sugar
    4. Lemon tsami
    5. Sprite
    Yadda ake haɗawa
    1. Ki samu kofi, ki sa mint leaf guda shida, sai ki ɗauko cokali, ki ɗan dake mint leaf din sabo da ya yi releasing ƙamshinsa.
    2. Ki matse lemon tsami rabi a ciki sannan ki sa sugar.

    Ki zuba ƙanƙara.

    1. Sai ki zuba sprite a kai ki juya. Shi kenan juice naki ya haɗu.

    KU KARANTA Yadda ake kunun zaƙi

  • Yadda Ake Kunun Zaƙi

    Yadda Ake Kunun Zaƙi

    Kunun zaƙi

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Gero
    2. Kanunfari
    3. Girfa
    4. Citta
    5. Sugar
    6. Ruwa

    Yadda ake haɗawa

    1. Ki samu gero ki sa ruwa ki wanke, sai ki jiƙa ta, kamar na awa biyu
    1. Sai ki raba shi kashi biyu, kashi ɗaya ki ɗaura ruwa a kan wuta, in ya tafasa, sai ki zuba a kai ki juya. Kashi ɗayan kuma, ki zuba ruwan sanyi akai, sai ki haɗa da ɗayan, ki juya su duka.
    1. Idan ya yi kaurin da kike so, shi kenan inda buƙatar ƙara ruwa, sai ki ƙara. Sannan ki samu abun tata ki tace, sai ki sa suga.

    Ki nemi gora ki ɗura a ciki, sannan ki sa a fridge in ya yi sanyi a sha.

    Domin karanta Yadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo

    Yadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Zoɓo

    2. Kanunfari

    3. kimba

    4. Masoro

    5. Lemon grass

    6. Sugar

    7. Ruwa

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za ki wanke zoɓonki ki sa a tukunya, ki sa ruwa, kanunfari, kimba, masoro, lemon grass ki rufe ki bari ya tafasa sosai sai ki sauke ya huce.

    2. Sai ki tace ki sa sikari. Ki sa a firji in ya yi sanyi sai a sha.

    Domin karanta Yadda Ake Lemon Abarba A Sauƙaƙe danna nan.

  • Yadda Ake Lemon Abarba A Sauƙaƙe

    Yadda Ake Lemon Abarba A Sauƙaƙe

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Abarba
    2. Ruwan sanyi
    3. Sikari
    4. Na’ana
    5. Ɗanyar citta
    6. Ruwan lemon tsami

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za ki ɓare abarba, ki yanka ta ƙanana, ki sa a blender, ki sa ruwan sanyi, sikari, ɗanyar citta ki niƙa su, ki tace.

    2. Sai ki samu serving glass, ki dan daka na’ana, ki zuba pineapple juice da ruwan lemon tsami kaɗan ki juya. A sha lafia.

    Karin bayani

    Ba lallai sai da ruwan sanyi za ki yi ba, za ki iya amfani da ƙanƙara ko kuma bayan kin tace ki sa a firji ya yi sanyi.

    In ba ki da na’ana za ki iya yin sa haka, haka shi ma lemon tsami. Wannan shi ne yadda ake haɗa lemon abarba a sauƙaƙe.

    Domin karanta Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga danna nan.

  • Yadda Ake Kunun Alkama A Sauƙake

    Yadda Ake Kunun Alkama A Sauƙake

    Barkan mu da sake kasance a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake kunun alkama.

    Kunun alkama dai yana da ruƙon ciki kuma yana da lafiya a jiki musamman a gurin masu ciwon siga, amma sai dai kada su yi amfani da suga wajen shan kunun.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    1. Alkama
    2. Gyaɗa
    3. Sugar
    4. Citta
    5. Cardamon
    6. Ruwa
    7. Fulawa
    8. Nono ko tsamiya

    Yadda Ake Haɗawa

    1. Ki gyara alkama ki wanke, ki sa ruwa a tukunya ki zuba alkama, cardamom, citta busasshe, ki bari ya tafasa; alkamar ki ya yi rabin nunar sa.
    2. Ki samu roba ki sa niƙaƙƙen gyaɗa da ruwa ki dama sai ki tace. Bayan alkama ta yi rabin dahuwarta ki sa tatacciyar gyaɗar, ki sa sugar yadda kike so. Ki bari alkaman ta nuna yadda ki ke so.
    3. Sai ki dama flour ki kaɗan a wani ƙaramin bowl, ki zuba a kan kunun, ki gauraya. Ki sauke bayan minti huɗu ko biyar.
    4. Sannan ki nemi rariya ki tace nono ko tsamiya sai ki zuba. Wasu a kan wuta suke zubawa wasu kuma sai bayan sun sauke, duk wadda kike so duk ɗaya ne.

    Ƙarin bayani

    Za ki iya saka kimba ko kanunfari a ciki, yana sa kunu ya ƙara ƙamshi sosai.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Shinkafa Da Miyar Attaruhu danna nan.

  • Yadda Ake Koko

    Yadda Ake Koko

    Koko abinsha ne na karin kumallo na hausawa, wanda ake yin sa daga gero. Koko na da daɗin sha, ga matuƙar amfani a jiki.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    Gero
    Citta
    Barkono
    Kanunfari

    Yadda Ake Haɗawa:

    1. A jiƙa gero ya jiƙu sosai, sai a zuba citta, kanunfari da ɗan barkona kaɗan, sai a niƙa.

    2. Sai a tace shi da abin tata, a fitar da dusar da gasarar, sai a bar shi ya kwanta.

    3. A tafasa ruwa a kwano daban, kuma sai a ɗebi kwantacciyar gasarar nan, sai a ƙara mata ruwa a juya ta ɗan yi kauri kaɗan.

    4. Sai a sheƙa mata wannan tafashasshen ruwan zafin da sauri sai a motsa kaɗan.

    Domin sanin yadda ake burabusko danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Kunun gyaɗa na ɗaya daga cikin abin sha mai daɗi da amfani a jikin ɗan Adam.

    Abubuwan da ake buƙata;

    Farar shinkafa

    Ɗanyar gyaɗa 

    Sugar daidai misali

    Yadda ake haɗawa

    A gyara farar shinkafa sai a wanke ta, a tsane tsaf. Bayan haka, a soya gyaɗa sama-sama a murje, bayan an bushe, sai a markaɗa, bayan an markaɗa a tace.

    Sai a zuba tataccen ruwan gyaɗar a tukunya, in ya tafasa, sai a ɗauko wanna shinkafar da aka wanke aka tsane, sai a zuba ta a ciki, su yi ta dahuwa har sai ta dahu sosai.

    Don gudun kada ya tsinke, za ki iya zuba ruwan lemon tsami kaɗan. Idan kuma an ga bai yi kauri ba, sai ki ɗan ɗibi gasarar koko a dama da ruwan sanyi sai a zuba a juya sosai zai yi kauri.

    Domin sanin Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga

    Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga

    Kunun kwakwa yana ɗaya daga cikin abin sha mai riƙe ciki, sannan ba shi da wahalar narkewa a ciki.

    Yana rage hawan suga ga masu ciwon suga, ruwan kwakwa yana wanke koda da samun fitar fitsari cikin sauri da inganta aikinta wajan tace abubuwa da sauransu.

    Abubuwan da ake buƙata:

    Kofi ɗaya na Farar shinkafa
    Kofi ɗaya na Kwakwa
    Kofi ɗaya na Gyada
    Kofi ɗaya na Madara
    Sai a zuba ruwan zuma gwargwadon yadda ake buƙata ko sikarin da suke amfani da shi na masu ciwon siga.

    Yadda ake haɗa kunun kwakwa

    1. Da farko za a wanke shinka fara, sai a jiƙa ta da ruwan zafi tsawon minti talatin (30)

    2. Sai a jiƙa gyadar, a surfa ta, a wanke ta (kamar yadda ake wanke wake).

    3. Sai a juye su (Shinkafa, gyaɗa, kwakwa) a abin da za a markaɗa (blender). A zuba ruwan kwakwar a yi blending sosai; (Za a iya ƙara ruwa idan ruwan kwakwar bai isa ba)

    4. Sai a tace a ɗaura a tukunya a yi ta juyawa har sai an ga ya yi kauri.

    5. Sai a zuba zuma ko sikarin masu ciwon siga (gwargwadon yadda ake buƙata) da madara kofi ɗayan nan a motsa. Sai a kashe wutar, a bar shi ya kama jikinsa kamar na minti biyar

    Wannan abin shan, yana da kyau ga masu ciwon siga da ‘yan sama da shekara arba’in (40). Su mayar da shi abincin darensu, domin ƙarin lafiyarsu.

    Domin sanin yadda ake Buredin Kwakwa danna koren rubutun nan.

    Domin sanin yadda ake Yadda Ake Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread) danna koren rubutun nan.