Tag: ƙasar Hausa

  • Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa 2

    Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa 2

    Aure wani zama ne halastacce tsakanin mace da namiji bisa ga matsayin miji da mata, wanda al’adar Bahaushe da kuma addinin musulunci suka amince da shi. Babban dalilin da yasa ake yin aure shi ne, don samun yaɗuwar jinsi a doron ƙasa gami da wanzuwar al’umma. Aure ba ya inganta sai da waliyyi (mace waliyyi, namiji kuma wakili), siga, sadaki da kuma shaidu.

    Abubuwan da suke da alaƙa da aure a ƙasar Hausa

    1. Samartaka (Zance ko hira).

    2. Sallama/ nuna kai.

    3. Toshi.

    4. Baiko / sa rana.

    5. Sa lalle/ rufi.

    6. Ɗaurin aure.

    7. Wankan amarya.

    8. Biki (gidan su amarya da ango).

    9. Biɗar kai/ buɗan kai.

    10. Sayen baki.

    11. Kai Gara.

    12. Gai-da surukai.

    13. ‘Yar zaman ɗaki/ ƙanwar rana.

    Danna nan don karanta rabe-raben auren Hausawa

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Muhimmancin Aure a Ƙasar Hausa

    Muhimmancin Aure a Ƙasar Hausa

    Muhimmancin Aure – Aure abu ne mai matuƙar muhimmanci a wurin Bahaushen mutum; wannan ta sanya da zarar yaro ya tasa za ka ga an yi masa aure.

    Kuma ma har idan an ga wani ya aikata wani abin da bai dace ba; wanda cikakken mai hankali ba zai yi ba, sai ka ji an ce ‘Ai ba shi da aure’.

    Ko kuma idan saurayi ko yarinya kansu na rawa, sai ka ji an ce, ‘A yi musu aure ko sa nutsu’.

    Kenan aure sababi ne na nutsuwar mutum a wurin al’ummar Hausawa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Muhimmancin Aure A Rayuwa danna nan

  • Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa

    Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa

    Waƙoƙi : Masana sun yi ƙoƙarin bayyana asalin samuwar waƙoƙi baka a ƙasar Hausa.

    Daga ciki akwai ra’ayin Satatima (1999:30) inda ya bayyana cewa: “Al’ummar ƙasar Hausa sun sami basirar kiɗa..

    Harda waƙa daga tsofaffin daulolin Ghana da Mali da Songhai wanda wasu sassa na ƙasar Hausa suka kasance ƙarƙashin mulkinsu

    kafin ƙarni na sha tara.

    Masu wannan ra’ayi har sun kai ga cewa daga waɗannan tsofaffin dauloli Hausawa suka samu kayan kiɗa irinsu kakaki, wanda aka samu daga Songhai cikin ƙarni na sha shida. Algaita kuwa an samo ta ne daga Songhai da Mali”.

    A wurin Gusau (2003:5-6) kuwa, ya kawo hasashe guda uku waɗanda yake ganin su ne asalin waƙar baka.

    Waɗannan hasashe kuwa su ne:

    Ra’ayi na farko, suna ganin ana jin ɗan’adam ya ƙagi waƙa ne tun lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar farauta, daga nan ya gano noma sai waƙa ta ƙara haɓaka.

    Ra’ayi na biyu kuwa, an nuna cewa, ana ganin waƙa ta samo asali ne daga wani maroƙi ‘Sasana’.

    Domin haka, a wannan ra’ayi ana jin makaɗan Hausa jikokin wannan mutum ne.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Kiɗa da Makaɗi danna nan

  • Masu Yin Kiɗan Fiyano A Ƙasar Hausa

    Masu Yin Kiɗan Fiyano A Ƙasar Hausa

    Bayan samun fiyano a ƙasar Hausa, an samu makaɗa da dama da suka sayo ta; kuma suka buɗe shaguna a wurare daban-daban domin yin kaɗe-kaɗe na fiyano.

    Daga cikin masu kiɗan fiyano a ƙasar Hausa akwai:

    1. Ahmad Mahmud Gusau

    2. Basiru Bala Maigoro, Sokoto

    3. Dauda Adamu Kahuta (Rarara)

    4. Faruq Nagudu

    5. Rabi’u Dalle

    6. Firdausi Yar Dubai

    7. Aminu Garba Maidawayya

    8. Usaini Kaɗo Ƙofar Na’isa

    9. Zainab A Baba

    10. Adamu Hassan Nagudu

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mawaƙan Da Ake Yi Wa Kiɗan Fiyano danna nan.

    Domin karanta bayani akan Muhallan Da Ake Waƙoƙin Fiyano Na Hausa danna nan

  • Taƙaitaccen Tarihin Ƙasar Hausa

    Taƙaitaccen Tarihin Ƙasar Hausa

    Alhassan (1981:1) ya bayyana Ƙasar Hausa ta asali tana Afirka ta Yamma; a farfajiyar dake tsakanin hamadar sahara da dazuzzukan da suka doshi gaɓar tekun Atilantika daga kudu.

    Kuma ana kiran Ƙasar da suna Sudan ta Yamma, wato tsakanin Tafkin Chadi da gwuiwar Kogin Kwara daga yamma

    A bayanin Ibrahim (1982:1); ya nuna cewa Ƙasar Hausa tana shimfiɗe ne a can Arewacin Nijeriya da kuma Kudancin Jamhuriyar Nijar a cikin Afirka ta Yamma. Daga gabas ta yi iyaka da ƙasashen Borno;

    Haka ma daga yamma ta yi iyaka da ƙasashen Dahomey a gaɓar Kogin Kwara. Daga arewa ta yi iyaka da Ƙasar Adar a cikin Jamhuriyar Nijar; Daga wajen kudu kuma ta yi iyaka da ƙabilun Gwari da kuma ƙabilun kudancin Zariya da na kudancin Bauchi.

    A wannan zamani a iya cewa Ƙasar Hausa yanki ne wanda ya mamaye dukkan Jihar Kano da Katsina da Arewaci Jihar Kaduna da wasu ɓangarorin Bauci da Gwambe da Neja da kuma kudancin Jamhuriyar Nijar.

    Idan aka tayar da saiti daga Arewa zuwa Kudu; Ƙasar Hausa tana farawa daga Azbin har ya zuwa kusurwar Arewa maso Gabas da tsaunukan Jos. 

    Daga nan sai ta shararo ta yi arewa maso yamma ta yi mahaɗa da ƙaton rafi na kogin Kabi. Daga wannan wuri ta karkata ta nufi arewa maso gabas har Azbin. (Birnin-Kudu, 2002:11-12 a cikin Sallau, 2013:481).

    Ƙasar Hausa wadda take shimfiɗe a shiyyar Sudan ta Tsakiya, a tsari na gargajiya a iya cewa ta haɗa da ƙasashen sarakunan Katsina, Kano, Daura, Zazzau, Kabin Argungu, Gwandu, Gumel, Haɗejiya, Ƙwanni, Maraɗi da Tassawa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Nazarin Matsalolin Aure a Ƙasar Hausa Daga Mahangar Zabiya Lawisa da Fatima Jalo Wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wane Ne Bahaushe? danna nan

    Domin karanta bayani akan AL’ADAR BAHAUSHE danna nan

  • Wane Ne Bahaushe?

    Wane Ne Bahaushe?

    Idan muka juya kan sanin wane ne Bahaushe kuwa? A iya cewa mafi yawancin mazauna Ƙasar Hausa su ne al’ummar Hausawa.

    Amma akwai wasu ƙabilu waɗanda suka yi kaka-gida a wannan Ƙasa ta Hausa; har hakan ya sanya suka koma Hausawa a harshe da al’adu da kuma adabi.

    Waɗannan ƙabilu kuwa sun haɗa da Fulani, Buzaye, Barebari, Nufawa, Yarbawa da sauransu. Amma Ibrahim (1981:1) ya bayyana cewa Hausawa su ne mutanen dake zaune a Ƙasar Hausa tuntuni, kuma suna magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa.

    A ra’ayin Adamu (1983:3) kuwa, na ganin Hausawa sun haɗa da mutanen nan waɗanda saboda ƙaura da magabantansu suka yi daga Ƙasar Hausa; zuwa wasu sassa dake maƙwabtaka ta kusa ko ta nesa da Ƙasar Hausa; koda kuwa ba sa magana da harshen Hausa ko yin al’adun Hausawa, sun ɗauka su Hausawa ne.

    Misali, Abakwariga dake zaune a Jihar Taraba ta Nijeriya da kuma wasu dake ikirarin cewa su Hausawa ne; waɗanda ke zaune a ƙasashen Cote de Voire da Burkina Faso da Mali.

    Magaji (1986:3), ya nuna Hausawa dai su ne mutane waɗanda harshensu shi ne Hausa. Haka kuma dukkanin al’adunsu da ta’adunsu na Hausa.

    Haka kuma addinin Musulunci ya yi cikakken tasiri a kansu.

    A ra’ayin Sallau (2000:71) kuwa, na ganin waɗanda saboda ƙaura da magabatansu suka yi zuwa Ƙasar Hausa sun manta da harshensu da adabinsu da al’adunsu na asali sun ɗauki na Hausawa. A taƙaice sun koma Hausawa a harshe da adabi da al’ada. Misalin ire-iren waɗannan mutane sun haɗa da Barebari, Kambarin Barebari, Barebarin Katsina da Buzaye da wasu Fulani.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Nazarin Matsalolin Aure a Ƙasar Hausa Daga Mahangar Zabiya Lawisa da Fatima Jalo wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan