Shin Mutum Na Da Buƙatar Gyara Don Zai Aure

0
80

Duk da cewar ina mace wannan Rubutun Bai Kamata nayi saba amma abin dana duba yin rubuta zai taimakawa al”umma wanda suke shirin aikata hakan sudaina zai taimakawa AI’umma sosai shiyasa zanyi Allah yasa wasu karsuyimun wata Fassara.

Zan so naja hankalin mu game da wani muhimmin al’amari dake faruwa na baiwa Samari ko Matasa da aurensu yazo dab shawarar shan maganin karfin Maza kamar yadda a ɗaya hannun iyaye kan ɓata lokaci wajen shirya ƴaƴa mata.

Zanyi jan hankalin ne ganin yadda abin ya kai ga fara jawoma matasan mu mutuwar tsaye, wanda kuma aqalla na sami cases huɗu kenan cikin wata guda kan matsalar, wanda na tabbatar a sauran asibitocin mu na Nigeria suma suna samun masu matsalar dakan je musu. 

Masu cikakken hankali tare da nazartar al’amura cikin mu a yau zasu iya gane ko rubutu ne a media inya zamto an sirka yasashshen zance ko Batsa ciki yafi jan hankalin mutane, anfi tururuwa kansa.

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

Wannan ke nuna irin yadda mutane suke baiwa al’amarin sha’awa muhimmanci a yau. Wanda abin har ya wuce mizanin lafiyayyen hankali.

A kwanakin da suka gabata mun sami wani mara lafiya da aka kawo asibiti ta emergency da wata matsala da muke cewa “FRIYAFIZIM” Wato miƙewar alƙalami yaƙi kwanciya, komi irin ƙoƙarin ganin ya kwanta ɗin da za ai kuwa bazai ba, kuma in aka matsa ma tsab zai karye. 

A tsarin aiki na jiki shi namiji gabansa bai miƙewa tsaye cak ya sami erection face sai idan jini yana kwaranyowa yana cika jijiyoyin azzakarinsa. Wanda idan jinin ya cika jijiyoyin taf shine gaban zai miƙe tsaye cir ai abinda za ai, shi kuma wannan jinin yana shiga ne ta jijiyar ATIRI (artery) tare da fita ta cikin jijiyar Ben (Vein) a guje batare da jinkiri ba, continuous circulation.

Toh amma idan ya zamto jinin ya shiga jijiyar ATIRI amma hanya ta kulle ya kasa yin gaba ko baya zuwa jijiyar Vein balle ya fice to shine azzakari zai kasance tsaye cak, ya ɗau ɗumi, ko me mutum zai abin bazai taɓa kwanciya ba wato friyafizim kenan.

Wanda shi dama maganin ƙarin karfin maza aikin da yake yi shine buɗe jijiyoyin jinin azzakari su tale, su cika dam da jini don ya zamto ansami erection tare da qarawa zuciya gudu.

Domin karanta bayani akan Matsala Ta Rashin Karfin Mazakuta Ko Rashin Tashin Gaba Gaba Daya Danna nan

Babbar damuwar kamar yadda na faɗa a baya ita ce; a yau zaka sami matasa zarar mutum zai aure misali ga maza Zakaga daga cikin abokansa wasu na kokarin bashi shawara tare da son fahimtar dashi cewa lallai fa yana bukatar yasha irin wnn maganin na ƙara kuzari… Saboda da yawa sun jahilci al’amarin jima’i, wasu ma fa cikin masu bada shawarar basu da auren, har ko a riƙa nunawa mutum cewa bazai taɓa mutunci gun Matarsa ba inba wannan…. Subhanallah. 

A gaskiya wannan muguwar shawara ce, kuma ina ƙalubalantar duk me ɗora mutane kan irin wannan muguwar shawarar da sunan taimako akan ya fito yai baje koli hujjojin da ya dogara dasu, ya dace mutane suji tsoron Allah, koda kudi zamu nema to kada mu zamto masu yi ta hanyar saka rayuwar mutane cikin hatsari, ta yadda kudin kurum muke hange, domin abin na neman zama kamar wani normal alhalin IS NOT Normal medically.

Domin da magana ta fatar baki kacal kana iya dora mutum kan abinda zai iya halaka wanda in shi bai gane kai ka cucesa ba’ ya ɗauki mataki toh zade ku haɗu a gaban ubangiji. 

Shi wannan patient ɗin irin tsutsayin da ya haɗu dashi kenan bayan da ya biyewa gurguwar shawarar abokansa, suka samo masa tare da sanya shi shan maganin a daren ranar daurin aurensa, inda karshe ya sami firiyafizm, gabansa ya kasance miƙe yaqi kwanciya tsawon awonni sama da ashirin da biyu, kuma bai tunanin zuwa asibiti ba farko ganin hakan, yaje ya sami wanda suka bashi shawarar akan abinda ke faruwa amma sun rasa taya ma zasu taimaka masa, domin iya abinda suka sani shine in ansha za’a sami mikewar gaba yadda ko anyi release kai tsaye za’ai saɓi zarce… Amma menene matsalar da ka iya biyo baya sam babu wanda yasan komi.

Domin karanta Hiv/Aids Cutar Kanjamau (Sida) Danna nan

Karshe kurum nuna masa ya koma ga iyali sukai, irin ai Normal ne sha’awar sa ce bata gama karyewa ba, alhalin duk ya gama yiwa yar mutane rauni, tun ana abu na daɗi ya koma wahala, haka ya zauna tun alƙalamin bai fara zafi ba har ya fara… Wanda saida ya fara fita hayyacinsa, yaji ba sarki sai Allah sannan ya nemi san uwansa aka kawo asibiti a jigace.

Nan mukai tambayoyin da suka dace don sanin makamar fara aiki, a gaggauce muka fara ƙokarin ganin yadda zamu taimake sa domin a awoyin da ya dauka munsan gaban na iya mutuwa, Tunda gashi ya fara fita daga hayyacinsa saboda azaba.

Kai tsaye muka zira allurai jiki muka fara kokarin zuqe jinin da ya zamto trapped cikin azzakarin, tare da flushing da ruwa sama da liter 1 da rabi, da sauran allurai, wanda bayan shafe kusan awa guda, muka fara samun nasarar kwantar da ita, saide bayan baifi minti 20 ba da gama wannan wahalar abar ta qara mikewa tsaye wato Recurrent stuttering priapism… A nan ne fa ya zamto bamu da zaɓi sama da musa wuƙar mu ta fiɗa “surgical blades” mu lumata ciki kan kaciyarsa don samun kwaranyowar jini sosai, haka mukai ta fama kafin Allah ya bamu sa’ar kwantar da ita, wajen sama da awa 2 muna aikin abu guda

In taƙaice muku de dalilin wannan illar da yai ma kansa da tsawon lokacin da ya dauka kafin zuwa ga likita rashin jinin dake circulation yasa tsokokin azzakarin sun lalace, ya gamu da Probable permanent Erectile dysfunction, Wato gabansa bazai kuma tashi ba koda yaji sha’awa ballantana ma sha’awar ita kanta ta taɓu. 

Abu daya ne ya rage shima sai in yana da gata ko hali shine; ai aiki asa masa penile implant “Wato dashen robobi cikin azzakari”, robobi masu kamar rehu da inyaso jima’i zai riƙa matsatsu kamar irin yadda ake matsa robar jikin abun awon hawan jinin nan “spygmanometer” da ake matsawa yake qara tsamke hannu, inyaso in angama jima’in sai ya kwance kan robar iskar ta fita’ gaban ya kwanta.

Saide ko shi wannan ɗin yana bukatar kusan Naira Milyan 5 zuwa 10 koda a Nigeria za ai aikin, kuma ba tabbas ma in anyi adace. Sannan ko andace bazade ka taɓa kwatantashi da natural erection ba.

Wannan shine yadda sauraron kowanne irin taci barkatai din shawarwari kan kai mutum ya barosa. Yanzu amaryar da shi yaso birgewa shin zata iya haƙuri ta rayu dashi ahaka kuwa? Wannan can zasu warware ta, amma da kamar wuya de kam. 

Don haka kamar yadda nake faɗa muji tsoron Allah, mu sani in wani fa yai rawa an watsa kudi wani inyai duka zai ci. Eh Mun yadda muna iya zamowa mutane baki daya… To amma fa ginin halittar jikin mu na kowa ya bambanta da juna, kamar yadda kakannin mu da kalar surar mu suka bambanta dana juna. 

Baka bukatar shan komi don kurum zakai Aure! Bai dace mu zamo birkitattu marasa lissafi ba. Ko zinace-zinace ka saba yi kake zaton kana da matsala yana da kyau ka fahimci jima’i da Macen da aure ne tsakaninku yasha bamban da wacce ita kuɗi ne tsakaninku. Ka lura da cin fruits, tsafta, wanka, wanki, shafa turare, iya magana, da kyautata mu’amala shikenan kurum. 

Duk wata matsala da zaka ga alamun kamar kana da ita a sanda kai sabon aure kurum ka kau da kai ka bata lokaci, ba matsala bace har sai kaga kun shafe watanni 6 cir batare da abin ya kau ba…. sannan ne zaka iya tabbatar da matsala, inba haka ba koda saurin inzali bai amsa cewa akwai sa har sai kai wata 6 kana jima’i batare da jin ka gamsu ba.

Amma daga lokacin da ya zamto kuna gamsuwa to ko minti 2 kake sunansa jima’i kuma lfy kake, ba sharadi bane duk jima’i sai an shafe tsawon mintoci masu yawa, ba yadda yake a finafinan Batsa ba yake a zahiri. Kuma wannan ina bayani ne akan duk wani maganin karin karfi walau na Hausa kona bature. Bakai bashi, muddin ba’a son a shiga wahala. 

Kuma in kana tunanin matsala fara zuwa babban asibiti Urology center, Teaching hospital, FMC, ko Specialist hospital tukun kaga likita, bawai garzayawa ga masu magungunan gargajiya ko Islamic Chemist ba, asibiti ne matakin farko basai abu ya lalace ka doso mu ba.

Karant maganin Matsala Ta Rashin Karfin Mazakuta Ko Rashin Tashin Gaba Gaba Daya

labarin da ya wuceHiv/Aids Cutar Kanjamau (Sida)
Labarin na GabaHawan Jini Ga Mace Mai Juna