Sauya Akalar Kiɗan Gado Zuwa Na Fada Da Na Game-Gari

0
28

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun tun yana cikin aiwatar da kiɗa na Gayauna; wato tun kafin a naɗa shi Sarautar Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun yake shigowa da wasu halaye masu jan hankali; da buɗa ido a yanayin kiɗan da ya taras iyaye da kakanni suna yi a gidansu.

Domin haka tun a aiwatar da waƙoƙin baka na Gayauna Musa Ɗanƙwairo yake shiryawa da sadar da:

i) Waƙoƙin Noma

A waƙoƙin noma, Makaɗa Musa Ɗanƙwairo, ya yi farin jini sosai, jama’a sun so waƙoƙinsa, musamman waƙoƙi na noma; waƙoƙi ne da suke ƙunshe da lugga da zaɓaɓɓun kalmomi. Ga kuma zayyana faruwar abubuwa da adonta harshen waƙa tun ma ba a turken yabo; da ɗiya na zambo da ba’a da sauransu ba. Sannan ga Ɗanƙwairo da murya mai zaƙi da kaurara zance kuma mai jan hankali mai sauraro.

ii) Waƙoƙin Fada

Waƙoƙin fada, waƙoƙi ne waɗanda Ɗanƙwairo ya yi wa ‘ya’yan Sarakuna da Sarakuna kansu da Hakimai; da Dagatai da masu riƙe da muƙaman Sarauta da sauran masu jinin Sarauta da makamantansu.

iii) Sarkin Kiɗa

Makaɗa Abdu Kurna Maradun (1899-1962) yayan Ɗanƙwairo, ya lura da irin tumbatsa cikin ƙwarewar da Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya samu a kiɗan noma da na fada (Sarauta); inda kuma ya dinga kai gayaunan kiɗa, ya sutta kuma ya jima.

Abdu Kurna ya dinga jan kunnuwan Musa Ɗanƙwairo, yana yi masa kandarki, har dai wata rana ya gaya wa ubangidansa, Sarkin Ƙayan Maradun da bakin waƙa yana shaida masa:

Jagora: Sarkin Ƙaya wa Ƙwairo faɗa,
‘Y/Amshi: Bai barin halinai,
Jagora: Daga zuwa Maƙera, ni maikiɗi,
: Ban ji labarinai ba,
: Sai can zuwa Ɗanmanau,
: Na Ruwan Kiɗi sa sirdi,
‘Y/Amshi: Hau ko kana gane shi,
: Na Ruwan kiɗi hau doki,
: Tahi ko kana iske mai,
: Shi yay yi damben girma,
: Jikan Hassan ɗan Iro,
: Sarkin Ƙaya mai gayya,
: Na Magaji ba tagewa.

(Musa Ɗanƙwairo, Waƙar Shi yay yi dambe girma & Gusau, 1988: sh. 224).

iv) Waƙoƙi Game -Gari

Kurwar Musa Ɗanƙwairo ta waƙar baka ba ta keɓe shi ya tsaya a rera waƙoƙin noma ko na fada ba. Musa Ɗanƙwairo ya kawo wani yanayin sussuka da daddare; yayin da ya shigo da aiwatarwa da rera waƙoƙin da a yau nake kira da waƙoƙi Game-Gari (Gusau, 2008a, sh. 161-162).

Waƙoƙi Game-Gari kuwa sun ƙunshi waƙoƙin Malamai da Alƙalai da Lauyoyi da Attajirai; da sauran ‘Yan Kasuwa da Ma’aikata da ‘Yansiyasa da siyasar kanta da Sojoji da Jarumai da Dakaru da sauran Mayaƙa; da Mafarauta da Maharba da masu sana’o’i da Samari da ‘Yanmata da Dabbobi da Tsuntsaye da Ƙwari da Gulabe da Dazuzzuka da sauran madangantan waɗannan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Fitattun Iyayengida Na Ɗanƙwairo a Kiɗan Fada danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceBayanin Manyan Malaman Sunna A Kan Matsayin Sayyidina Husaini (RA) Da Ranar Ashura
Labarin na GabaYadda Falalar Karanta Amanar Rasulu Take
Prof. Sa’idu Muhammad Gusau
FARFESA SA'IDU MUHAMMAD GUSAU, An haife shi a Gusau jihar Sakkwato, (Maris 24, 1952). Ya yi karatun firamare na Islamiyya daga 1965-1969, ya je kwalejin sarkin Musulmi Abubakar daga Junairu 1970 zuwa Yuni 1973. Ya yi Diploma, Digiri Na farko (B.A), na biyu (M.A) da Digiri na uku (Ph.D) duk a jami'ar Bayero, Kano.