Sanya Contact Lenses Domin Ado Na Birgewa

0
27

Muna cikin wani zamani da koyaushe sababbin abubuwa ƙara ɓullowa suke domin ƙayatar da jiki. Musamman mu mata. Contact lenses glass ne da ke da designing na kalolin ƙwayar ido daban-daban wanda ke tattare da jan hankali tare da maida mace so sexy. 

Akwai kalar baƙi, ruwan toka, ja, blue da sauransu. Babbar matsalar shi ne yadda abin ya fantsama cikin kasuwanni har wasu ke sai da shi tamkar yadda za ka je ka sayi alewa me tsinke alhalin abu ne da a ƙa’ida ba a sa shi da ka, sai an je ga likitocin ido sun ba mutum shawarar wanda ya dace da shi bayan sun auna ƙarfin ganinsa.

Sannan uwa uba wasu da ka suke amfani da shi. Ba kuma su san sharruɗan komai a kai ba. Wanda haƙiƙa amfani da wannan abu yana ba ƙwayoyin bacteria damar shigewa idon mutum 100% domin tamkar mayen ƙarfe haka yake a wajen ƙwayoyin cuta, wannan ta sa yana jawo ciwon idanu, hawan jinin idanu, apolo, gyambon idanu, da makanta baki ɗaya sakamakon irin waɗancan kura-kurai.

Don haka abinda nake so mu sani duk da ƙila bai yawaita ba to idan ma za ki ko za ka yi, tunda har Maza ma na sa wa ku sani:

1.Wajibi ne ya zamto bisa umarnin likitan idanu.

  1. Ba a bacci da shi.
  1. Duk wanda aka sa sau ɗaya ko minti 30 ya yi ba a kuma mai da shi.
  1. Ba a alwala da shi a ido
  1. Ba a wanka ko shower da shi.
  1. Ba a shiga swimming pool da shi.
  1. Ba a wanke fuska da shi.
  1. Ba a yadda a sayo a kasuwa ba domin ba ka san da me aka yi irin wannan ba. 

Wannan su ne matakan kiyayewa, in ba haka ba to fa akwai damar makancewa ɗari bisa ɗari a gareka. 

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceYadda Alamomin Ciwon Sanyi Yake
Labarin na GabaHar Yanzu Akwai Matsala Fa