Sanƙaran Nono Wato {Breast Cancer}

1
80

Ciwon kansa ne mafi shahara kuma lamba 1 a Nigeria dama duniya baki ɗaya wajen kashe ƴaƴa mata fiye da duk wani nau’in cutar kansa. 

Kansa ce da in akai jinkiri daga nono tana iya ratsa kaluluwa ta shiga lymphatic drainage ta taɓa ƙashi ta haddasawa mutum (bone Cancer) daga nan ta shiga ɓargo ta haddasa (myeloid cancer) ta ɓargo,ta biyo jijiyoyin jini ta haddasa cancer a hantar mutum (Liver cancer) daga nan ta afko zuwa ga huhu ta haddasa (Lung cancer) kai daga nan har ƙwaƙwalwa wato (Brain cancer) har tazo ga kayan ciki ana haka ta baibaye jiki duk baki ɗaya sai kuma jiran lokaci. 

Cutar kansa shu’uma ce, shiyasa a kullum muke jan hankali akoyi zuwa check up saboda Early Detection shi zai tserar da rayuwa ba magani ba,tunda stages ne 1—4 kunga in aka gano tun a stage 1 Toh abin zai fi zuwa da sauki,domin kunji dai yadda cancer ɗaya ta fara ta breast amma karshe tana iya zama cancer 5,ga tsadar magani.

Kansar nono na afkuwa ne ayayin da kwayoyin halittar nono suka fara girma akaran kansu batare da jiki ya umarcesu koya bukacesu da suyi hakan ba.

Domin karant bayani akan Ciwan Kai Na Gado Wato [Migraine] Danna nan 

Matar dake dauke da wannan cutar babu wani alamun ciwo da zataji tashin farko! Kawai dai wani ɗan tsiro karami ko ƙullutu wanda yake jeji ne (cancerous cell) zataji cikin nononta, wanda akarshe ka iya jawo mata babbar illah da zatasa dole acire nonuwan gaba daya inma anyi sa’a bata warwatsu ba kenan.

Kamuwa da cutar ba laifin mutum bane,ba kuma a kamuwa ta hanyar jima’i,ko yin hulda da mai cutar.

Mafita Shine: mace ta ringa kulawa da halin da take,da kuma halin da nonuwanta suke a koda yaushe ta hanyar duba kanta (self breast exams) ko sanya miji ya duba mata ko zuwa ga likita ya duba mata (periodic breast exam).

Ta yadda da taji wani abu daban kamar:
  • Jin ƙullutu
  • Jin suka cikin nonuwa kamar ana tsira mata allura
  • Ganin kumburin nono haka nan
  • Lotsawar wani sashi “dimples a nono
  • Ganin fitar ruwa-ruwa me jini ko clear alhalin bata shayarwa
  • Canzawar kalar wani sashin fatar na nono yai kamar jikin lemon ɓawo ko jaja-jajaa

Toh ta garzaya asibiti wajan kwararru !

Ku karanta Bayani Akan Gyambon Baki {Canker Sore} ha hanyar danna nan 

Duk macen data kai aƙalla shekaru 20 yana da kyau ta koyi yadda ake duba Nono (breast self exams) domin wannan wata hanya ce da mace zata iya ita kaɗai a ɗakinta,ko wajen wanka,ko ita da maigidanta,ta duba mamanta a madubi ko akwai wani canji ajiki. 

Yadda Ake Yi Kuwa Shine: 
  • Mace ta tube agaban ƙaton madubi ta ɗora hannayenta kan kugunta,ta kallesu a natse taga ko akwai wani yanayin canji a fatar ko ƙurji, dimples ko ƙari a jiki,gami da girman su.
  • Bayan nan sai ta juya ta gefe ta sake yin haka (wato ta duba gefen dama da hagu) ta ɗaga hannun ta ta kalli har zuwa hammatarta tunda jelar nonon nan ta shiga.
  • Daga nan saita sake kallon mudubin,tasa hannunta na hagu a bangaren nonon dama (yatsu 3 na tsakiya) ta fara daddannawa tana latsa gefe kamar circle ɗin juyawar kunamar agogon bango har zuwa ciki-ciki, koh daga kasa zuwa sama da karkashin hammata, taji ko zata ji wani ƙullutu.
  • Daga nan saita sake dawowa kan nonon ta matso shi ko zata ga wani ruwa ya fito (idan ba shayarwa take ba kenan). 
  • Idan ta gama da nonon dama sai taje ɓangaren na hagu shima tayi kamar yadda tayi a daman.
  • Sai kuma ta matsa kusa ta ɗaga nonuwan duk biyun ta duba yanayin fatar ƙarkashinsu lokaci guda ko akwai wani miki ko tabo.
Bayan kammalawa
  • Idan babu komai shikenan ta gama sai bayan aƙalla wata hudu 6 kafin ta sake.
  • Amma idan taji wani ƙullutu ko taga ta matso wani kalar ruwa ko kuwa taga wani canjin yanayi a fatar nonon to dole sai taje asibiti an kara bincike.

A asibiti ne zamu tantance kalar ƙullutun kila bayan mun kuma examine sannan munsa anyi hoto,domin akwai wasu yanayin dake jawo ƙullutun amma mune zamu iya tantancewa. tunda galibi ya kan kai ga zama cancer

Sannan akwai gwajin jini na codes din cancer da za’ayi  wanda shine zai tabbatar da yiwuwar cewa wannan mace nada chance din haɗuwa da cancer ko kuma saɓanin haka.

Kamar yadda wata fitacciyar yar shirin film ɗin kasar Indiya me suna ANGELINA JOLIE ta zaɓi likitoci da su cire nonuwanta da ovaries dinta bayan gano tana da chance sama da 80% na kamuwa da ciwon sakamakon sanin ciwon shi ya kashe mahaifiyar ta da yar uwar ta alhalin taga yadda suka sha fama, wanda yi mata wannan aiki yanzu yasa hatsarinta na kamuwa da ciwon ya dawo 2% kasa dana sauran mata ma da babu ciwon a dangin su,wanda kuma tunda da kudi an mata implant wanda baza ma kace ba nono bane na asali tunda aiki ne na kwarewa fatar anyi preserving dinta sosai,nono zaka gani sak a ido,wanda yanzu tana cikin ambassadors na wayarma da al’umma kai game da larurar. 

Domin karanta bayani akan Ba Kowane Ciwon Ƙirji Bane Ulcer Danna nan 

labarin da ya wuceBa Kowane Ciwon Ƙirji Bane Ulcer
Labarin na GabaSanƙaran Bakin Mahaifa (Cervical cancer)

SHARHI ƊAYA