Samuwar Fiyano A Ƙasar Hausa

0
431

Gusau (2008:6) ya bayyana fiyano wani abin kiɗa ne baƙo ga Hausawa da suka samu ta hanyar hulɗa ta Turawa”.

Samuwar waƙoƙin fiyano na Hausa ya kawo wani sabon al’amari ga manazarta waƙoƙin Hausa. Hakan kuwa ya faru ta yadda waƙoƙin suka zo da wata siga. Ga su kamar rubutattun waƙoƙi, amma sun yi kama da waƙoƙin baka.

Binta (2011:77)

Ta bayyana cewa, “Shigowar kiɗan fiyano zuwa ga Hausawa; yana da dangantaka da sha’awar kallo da sauraron kaɗe-kaɗen fina-finan Indiya da Hausawa suka tsinci kansu a ciki.

Domin kuwa waɗannan fina-finai na Indiya su ne suka zamanto fitilu masu haske ga yawancin masu shirya fina-finan Hausa.

Ƙoƙarin kwaikwayon kaɗe-kaɗen waɗannan finafinai ne yasa Hausawa suka dinga amfani da kiɗan fiyano suna rera waƙoƙin Hausa, suna sakawa a cikin fina-finai da ake kira na Hausa.

Ado Ahmad Gidan Dabino ya fito da fim ɗinsa mai suna ‘In Da So Da Ƙauna’; wanda aka yi kiɗan fiyano na farko a fim”.

Gusau (2011:8)

Ya bayyana cewa, “Daga bisani, bayan Hausawa sun iya karatu da rubutu na Ajami da kuma na Boko, sai aka samu wasu mutane suna rubuta waƙoƙi, amma sai su ɗora musu rauji na karin murya, sa’an nan su rera su tare da amon kiɗa (sauti na kiɗa)…

Har wayau, kayan kiɗan da ake amfani da su wajen rera waɗannan waƙoƙi sun ƙunshi kayan kiɗa na zamani ne kamar: Mandiri da fiyano da jita da gangunan Turawa da makamantan su”. 

Har akan jinjina kafin a iya rarrabewa tsakanin waƙoƙin na baka ko rubutattu. Wanda ya zama wani ƙalubale ga manazarta waƙoƙin Hausa. Domin kowa da yadda yake kallon su. Wasu na yi musu kallon waƙoƙin baka, wasu na cewa rubutattun waƙoƙi ne. Wasu kuwa sun kira su da waƙoƙin zamani.

Waƙoƙin fiyano na Hausa sun samu karɓuwa sosai da sosai wajen mutane, don kuwa waƙoƙin kullum sai ƙara bazuwa da karɓuwa suke yi. Kuma suna samun masu saurare, musamman matasa maza da mata. Haka kuma, kullum manazarta suna sauraren su, suna aiki a kansu.

Yaɗuwar Waƙoƙin Fiyano

Yaɗuwar waɗannan waƙoƙi na fiyano ta nuna cewa, sun samu karɓuwa, kuma sun yi tasiri. Saboda duk abin da ba ka da sha’awa a kansa, ba za ka mayar da hankali a kai ba. Don haka, yawan jin su a ko’ina, a wayoyin hannu da motoci da kantuna da gidajen rediyo na gida da na waje, ya nuna cewa sun samu karɓuwa.

Daɗin daɗawa, waƙoƙin a kullum ƙara yawaita suke yi, mawaƙan na ta ƙara samun basirar rera waƙoƙin. Har ta kai sukan yi irin waɗannan waƙoƙi a ƙungiyance.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Wuraren Da Ake Kiɗan Fiyano (Situdiyo) danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake (Recording) Ɗaukar Videon Abin Da Ake Gabatarwa A Fuskar Kwamfutarka Mai Ɗauke Da Windows
Labarin na GabaMasu Yin Kiɗan Fiyano A Ƙasar Hausa