Bayan makaɗan baka sun gama tunanin waƙar da za su yi; sai kuma su zo, su sadar da ita ga al’umma.
Ana sadar da waƙar baka ga Hausawa a ɗaiɗaikun gidajensu da wani wuri da suka shirya wanda ake kira dandali; wato wurin yin wasannin jama’a da a yayin farauta ko noma, musamman a lokacin gayyar noma a fadojin sarakuna, da lokacin bukukuwan al’umma da kuma taruka na makarantu da sauransu.
A ma’ana ta lugga ko ta ƙamus, Ƙamusun Hausa (2006:380) ya bayyana kalmar sada tana nufin (i)gama (ii) isar da (iii)sulhunta. Shi kuma littafin Ƙamus na Keɓaɓɓun Kalmomi wato Hausa Metalanguage (Muhammad, 1990 UPL Ibadan:104) cewa ya yi, kalmar Sadarwa da Ingilishi tana nufin Communication.
Shi ma Awde (1996:135) yana ganin kalmar Sadarwa tana nuni ne Communications da Ingilishi.
Sadarwa a ilmin waƙar baka tana yin nuni ne game da wasu dabaru; waɗanda ake amfani da su wajen isar da waƙoƙin baka ga waɗanda ake yiwa su. Ana isar da waƙoƙin baka ta hanyar rera wa mutane a wasu wurare da lokuta da yanayi.
Domin karanta cikakken bayani a kan Lokaci da Yanayin Sadarwa a Waƙar Baka danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Yabo A Waƙoƙin Baka danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Aiwatarwa Da Sadarwa A Waƙoƙin Baka Na Hausa wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.