Ranar Haɗuwar Ango Da Amarya

0
23

A musulunce ana so ranar da ango ya fara haɗuwa da amaryarsa ko kuma ranar da aka kawo wa ango matarsa gidansa, ya yi ƙoƙarin yin waɗannan abubuwa masu zuwa kamar haka:

(1) Ango ya jagoranci matarsa su yi Sallah raka’a biyu nafila don miƙa godiyarsa ga Allah da ya cika musu burinsu kamar yadda Ibn Abi Shaiba ya rawaito. (2) Ya ɗora hannun sa a kan goshin matarsa, wato ya karanta ya riƙe, sannan kuma ya karanta wannan addu’a kamar haka: 

“Ya Allah ina roƙonka alherin wannan mata da alherin da ka halicceta a kansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin abin da ka halicce ta a kansa”. ( Bukhari a cikin littafinsa da Abu Dawuda da Ibn Majah da wasunsu ne suka rawaito shi ). 

(3) Gabatarwa da amarya wani ɗan abin kusa da baka, kamar yadda Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) yayi wa matarsa Aisha (Allah ya yarda da ita ). 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

(4) Goge baki kafin kwantawa da amarya, domin kawar da wani hamami, ko wari da ka iya tashi daga cikin baki. Kamar yadda aka samu Muslim da Abu Awana sun rawaito Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) ya yi haka. (5) Yin addu’ar saduwa da mace, kafin fara saduwa da ita. Addu’ar kuwa ita ce:

“ Ya Allah ka nesantani daga shaiɗan ka kuma nesanta shidan daga abin da ka azurta ni da shi”. Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) yace: Idan Allah ya hukunta wa miji da matarsa samun ɗa a saduwar da suka karanta wannan addu’ar, to, shaiɗan ba zai cutar da ɗan da suka samu ba har abada”. (Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ). 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

(6) Yin walima da abin da Allah ya hore, bayan tarewa da saduwa da amarya. Saboda aiwatawar Annabi da kuma umarnin da ya yi na a yi walima. Sannan kuma idan za a kira jama’a walima, to a yi kokarin ganin an tara waɗanda suke mabukata, saboda Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) yana cewa: “ Mafi sharrin abinci walima, wanda ake kiran (ko gayyatar) mawadata a kyale mabukata “. ( wato a ki gayyatarsu ). ( Malik da Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ). 

Daga lokacin da Allah ya hukunta wa Musulmi aurar wata mace, ko kuma ya hukuntawa Musulma auren wani Musulmi, to ya zamar musu lallai su san cewa, a musulunce akwai wasu nauye-nauye da suke tattare da rayuwar da za su fuskanta ta zaman aure, wadanda suka sha bamban da na irin rayuwar da suka faro a baya ta zaman kaɗaici.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceFalalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana
Labarin na GabaNauye-nauyen Rayuwar Aure