Physiology da Hausa Kashi na Biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam

0
23

 

Daukacin Abubuwan dake jikin ɗan Adam namiji wanda nauyinsa ya kai kilo 70

Ruwa: Kashi 60

Kitse: Kashi 18

Sinadarai: kashi 7

-CHO: ƙasa da kashi 1

-Ganin yadda ruwa yake da kaso mafi yawa a jiki, hakan yasa ruwa ya kasance mafi amfanin a jikin ɗan Adam. Idan aka rasa da yawa daga cikin ruwan jiki, rayuwa za tai wahala a cikin yan kwanaki masu zuwa, saɓanin idan an rasa cin abinci, mutum yakan iya rayuwa har tsawan wata ɗaya.

 Rabe raben kaso na ruwa a mutane daban-daban

Adadin ruwan jikinmu na da alaƙa da shekaru da jinsi da kuma girman jiki.

 Shekaru: Ruwan jikinmu na raguwa yayin da muke ƙara shekaru, ma’ana yara sun fi manya yawan ruwa a jiki.

Jinsi: Maza sun fi mata yawan ruwa a jiki saboda yawancin mata na da kitse fiye da maza.

Girman jiki: Sirara sun fi masu ƙiba yawan ruwa a jiki, saboda yawan kitse da masu ƙiba ke da shi.

Abin da ruwan jiki ya ƙunsa

Kamar yadda muka bayyana a baya cewa, ƙwayoyin halittu na ɗauke da ruwa a cikin su, haka zalika a zagaye suke da ruwa.

Muka ce kuma ruwan jiki ya rabu kashi biyu;

Ruwan dake ciki da kuma wajen ƙwayar halitta.
  • A inda ruwan dake cikin ƙwayar halitta ya ƙunshi kashi 2 cikin 3 na ruwan jiki gaba ɗaya, ko kashi 40 cikin ɗari na nauyin jiki baki ɗaya.
  • Ruwan dake wajen ƙwayar halitta.

A inda ruwan dake wajen ƙwayar halitta ya ƙunshi kashi 1 cikin 3 na ruwan jiki gaba ɗaya, ko kashi 20 na nauyin jiki. 

Ruwan dake wajen jiki ya rabu kashi 3
  • Ruwan dake cikin jijiyoyi kaso 25 cikin 100.
  • Ruwan dake tsakanin jijiya da ƙwayar halitta kaso 75 cikin 100.
Abubuwan dake sauya yanayin ruwan jiki
  • Osmosis wato adadin gishiri dake jiki.
  • Sodium potasium pump, wato shiga da fitar sinadarai na sodiyom da potashiyom a kowace ƙwayar halitta,

Ƙarin bayani duk inda sinadarin sodiyom ya je ruwa na biye da shi.

Saitin adadin ruwan jiki
  • Adadin ruwan jikinmu na da alaƙa da adadin ruwan da muke sha a rana.
  • Adadin ruwan da muke sha na da alaƙa da buƙatuwarmu ga ruwa, wato shan ruwa
  • Adadin ruwan dake jikinmu na da alaƙa da rashin ruwa a cikin jiki, sanadiyyar wata cuta, misali gudawa ko amai(haraswa).

Yana dakyau ku karanta na farko wato Ilimin Fisiyoloji (Physiology ) Cikin Harshen Hausa Kashi na Farko Masaitin jiki (Homeostasis)

labarin da ya wuceRaunin Da Namiji Da Abinda Hakan Ke Nufi
Labarin na GabaPhysiology da Hausa Kashi na Uku: Excitable Tissues (Sassan motsi na jiki)
Dr. Yasir Aminu Ado
Ni dalibin likitanci ne nayi karatun likitanci a Kasar Sudan, Ina koyar da daliban jami'a masu tasowa ilimin karutun likitaci a saukake cikin harshen Hausa