Tag: kashi na biyu

  • Physiology da Hausa Kashi na Biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam

    Physiology da Hausa Kashi na Biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam

     

    Daukacin Abubuwan dake jikin ɗan Adam namiji wanda nauyinsa ya kai kilo 70

    Ruwa: Kashi 60

    Kitse: Kashi 18

    Sinadarai: kashi 7

    -CHO: ƙasa da kashi 1

    -Ganin yadda ruwa yake da kaso mafi yawa a jiki, hakan yasa ruwa ya kasance mafi amfanin a jikin ɗan Adam. Idan aka rasa da yawa daga cikin ruwan jiki, rayuwa za tai wahala a cikin yan kwanaki masu zuwa, saɓanin idan an rasa cin abinci, mutum yakan iya rayuwa har tsawan wata ɗaya.

     Rabe raben kaso na ruwa a mutane daban-daban

    Adadin ruwan jikinmu na da alaƙa da shekaru da jinsi da kuma girman jiki.

     Shekaru: Ruwan jikinmu na raguwa yayin da muke ƙara shekaru, ma’ana yara sun fi manya yawan ruwa a jiki.

    Jinsi: Maza sun fi mata yawan ruwa a jiki saboda yawancin mata na da kitse fiye da maza.

    Girman jiki: Sirara sun fi masu ƙiba yawan ruwa a jiki, saboda yawan kitse da masu ƙiba ke da shi.

    Abin da ruwan jiki ya ƙunsa

    Kamar yadda muka bayyana a baya cewa, ƙwayoyin halittu na ɗauke da ruwa a cikin su, haka zalika a zagaye suke da ruwa.

    Muka ce kuma ruwan jiki ya rabu kashi biyu;

    Ruwan dake ciki da kuma wajen ƙwayar halitta.
    • A inda ruwan dake cikin ƙwayar halitta ya ƙunshi kashi 2 cikin 3 na ruwan jiki gaba ɗaya, ko kashi 40 cikin ɗari na nauyin jiki baki ɗaya.
    • Ruwan dake wajen ƙwayar halitta.

    A inda ruwan dake wajen ƙwayar halitta ya ƙunshi kashi 1 cikin 3 na ruwan jiki gaba ɗaya, ko kashi 20 na nauyin jiki. 

    Ruwan dake wajen jiki ya rabu kashi 3
    • Ruwan dake cikin jijiyoyi kaso 25 cikin 100.
    • Ruwan dake tsakanin jijiya da ƙwayar halitta kaso 75 cikin 100.
    Abubuwan dake sauya yanayin ruwan jiki
    • Osmosis wato adadin gishiri dake jiki.
    • Sodium potasium pump, wato shiga da fitar sinadarai na sodiyom da potashiyom a kowace ƙwayar halitta,

    Ƙarin bayani duk inda sinadarin sodiyom ya je ruwa na biye da shi.

    Saitin adadin ruwan jiki
    • Adadin ruwan jikinmu na da alaƙa da adadin ruwan da muke sha a rana.
    • Adadin ruwan da muke sha na da alaƙa da buƙatuwarmu ga ruwa, wato shan ruwa
    • Adadin ruwan dake jikinmu na da alaƙa da rashin ruwa a cikin jiki, sanadiyyar wata cuta, misali gudawa ko amai(haraswa).

    Yana dakyau ku karanta na farko wato Ilimin Fisiyoloji (Physiology ) Cikin Harshen Hausa Kashi na Farko Masaitin jiki (Homeostasis)