Nazarin Rayuwar Adabin Kasuwar Kano

0
23

Balaga: 1990 zuwa 1995

Nazarin rayuwar Adabin Kasuwar Kano a zamanin da muka kira na balaga ya fito mana da siffofi mabambanta. Da farko dai lokaci ne da littattafan da suka samu wanzuwa daga shekarar 1984 suka samu karɓuwa tsakanin makaranta da masu buga littatafan da kuma masu sayar da su.

A daidai wannan zamani ne na shekarar 1990 zuwa 1995 za a ce Adabin Kasuwar Kano ya shiga tashen balaga, marubutan da suka yi suna da karɓuwa a tsawon shekaru, suka bayyana. Cikin irin waɗannan marubuta akwai Ɗan Azumi Baba Cheɗiyar ‘Yan Gurasa, wanda ya wallafa littatafai guda 9 a cikin wannan tsakani da kuma Aminu Abdu Na’inna da ya fitar da littatafai guda 6.

Akwai kuma irin su Ado Ahmad Gidan Dabino da Bala Anas Babinlata da Badamasi S. Burji da suka wallafa littattafai 4 kowanensu, haka kuma akwai marubuta irin su Balaraba Ramat da Yusuf Lawan Gwazaye da Alkhamees Bature da suka fitar da littattafai bibiyu kowane. Saura kuwa, irin su Ibrahim Mandawari da Ibrahim Sheme da Bashir Sanda, kowane ya fitar da littafi guda.

A ɓangaren mata kuwa, a wannan lokaci ne aka sami fitowar manyan marubuta mata da suka yi tashe a cikin wannan harka da daɗewa, marubuta irin su Bilkisu A. Funtua da Hadiza S. Aliyu da Hawwa Aminu da Atika S. Sidi da suka antayo daga shekarar 1994.

Abin la’akari dangane da wannan zamani na balaga shi ne, yawancin littattafan da aka samar daga cikin sama da 110 da aka wallafa a wannan tsakani sun fito ne daga taskar ƙungiyar Raina Kama da muka yi bayani a baya, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Ado Gidan Dabino.

A daidai wannan lokaci za a fahimci cewa wanda ya fi tashe a cikin wannan ƙungiya shi ne Ɗan Azumi Baba, wanda ya fito da wani salo na labaran aljannu da dodanni da muridai, sai ko Ado Gidan Dabino da ya ɗauki fagen soyayy wanda kuma ya fi kowane daga cikin marubutan shahara saboda alaƙarsa da ‘yan jarida da suka yayata shi da kuma irin rawar da ya taka wajen tallata kansa da kuma ƙwazonsa wajen gina labari.

Daga jadawalin marubutan da muka samu kai hannu kansu, mun fahimci nan ma maza suka fi shahara a fagen rubutun domin kuwa mata 12 ne suka tusgo, alhali maza 60 suka wallafa littattafai a wannan zango na Adabin Kasuwar Kanon (Dubi rataye na 8.0)

Tsufa Da Hayayyafa: 1996 zuwa 2001

Daga lokacin da kasuwar littatafan Adabin Kasuwar Kano ta yi tashin gwauron zabbi daga shekarar 1995  zuwa 1996 amon wannan sabon tsarin rubutu ba inda bai kai ba, wannan ne ya sa harkar ta koma irin ta wani babban kamfani. Ƙungiyoyin marubuta da suka ɓullo daga shekarar  1990  kamar su Kungiyar Matasa Marubuta da Kukan Kurciya da Raina Kama  da Jigon Hausa duk a cikin birnin Kano da Ruwan Dare a  Kaduna da kuma Kungiyar Matasa Marubuta ta Jihar Sakkwato a Sokoto (Adamu, 2006) su ma suka ƙara wa wannan harka martaba da ɗaukaka a idon mutane.

Haka kuma ƙungiyoyin makaranta irin su Dakata Readers Association da Kabuga Readers Association da Tudun Wada Readers Association da Hotoro-South Readers Association duk a cikin Kano sun agaza wajen tabbatuwar wannan harka.

Daga cikin kuma masu sayar da littattafan da suka agaza sosai a daidai wannan lokaci akwai irin su Alhaji Baba  na Jakara City Bookshop da Alhaji Musa Ɗanbala na Sauƙi Bookshop kuma Alhaji Garba Mohammed na Garba Mohammed Bookshop da ke Sabon Gari Kano.

Wannan aure na marubuta da makaranta da masu sayar da littattafai da kuma ƙungiyoyi daban-daban, shi ne za a iya cewa ƙashin bayan wannan fasali na Adabin Kasuwar Kano, wanda ya sanya harkar ta hayayyafa, ta kuma bunƙasa fiye da yadda ake tsammani.

Wannan ne ya sa aka sami yawancin tarin littattafan adabin Kasuwar Kanon masu yawan gaske da suka kai sama da 400, a tsakanin 1996 zuwa 2001. Daga wannan zango ne mata suka fara kunno kai sosai da sosai domin kuwa an sami marubuta mata sama da 50.

’Ya’ya Da Jikoki: 2002 zuwa 2008

Littattafan da aka yi wa laƙabi da ‘ya’ya da jikoki su ne ƙagaggun labaran da aka samu daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2008. Nazarin da aka yi wa waɗannan littatafai an fahimci cewa duk da sauye-sauyen da aka samu na litattafan Adabin Kasuwar Kano a wannan zango, ba a bar fasalin da aka saba ba, wato na yin rubutun bisa tsarin ni na rubuta, ni na gyara, ni na kai inda za a buga mini, ni kuma ke sayarwa da kaina.

An dai samu wasu sababbin marubuta ne da irin nasu fasali, sun ɓullo domin taka rawa irin tasu. Sai dai kamar yadda muka fahimta, wannan ba ya rasa nasaba da ganin cewa tsofaffin marubutan da suka yi tashe a baya, wasu sun watsar da rubutun, ko dai saboda sun yi aure ko kuma yayinsu ya wuce, wasu kuma sun koma wata sana’ar, musamman shirya finafinai, ga shi kuma buƙatar litattafan ba ta kau baki ɗaya ba, wannan ya jaza fitowar sababbin marubuta domin nuna irin tasu fasahar. An dai ga cewa an samar da littattafai na wannan zangon kimanin 248.

A wannan zangon kamar yadda muka nazarta, marubuta mata sun sami filin baje kolinsu. Daga cikin littattafan da muka samu kai hannu kansu marubuta mata sama da 76 ne suka yi tashe. Wannan shi ne karon da mata suka yi ambaliya sosai. Haka kuma daga hirar da na yi da makaranta littattafai a wannan zango sun nuna sha’awarsu kan rubuce-rubucen matan, ƙila wannan shi ya ƙara sa yawan marubuta matan.

A cikin waɗannan jerin littattafan na wannan zango, wadda ta fi yawan littattafai ita ce marubuciya Sa’adatu Saminu Kankiya tana da 14 da suka yi fice sosai, wannan kuma alama ce da ke nuna littattafanta sun fi samun karɓuwa ga makaranta. Mai yiwuwa saboda suna ɗauke da labaran da suka shafi soyayya da aure waɗanda bisa ga nazarin da aka gudanar su ne suka fi tashe a wannan zango.

Akwai kuma wasu marubutan mata da suka fi shahara a wannan zango da suka haɗa da Saliha Abubakar Zariya da Hadiza Salisu Sharif da Amina Abdullahi Sharaɗa da Zainab Birged da su Sa’adiya Kankiya da Rahmatu Hassan Sanda.

Duk da cewa yawancin waɗannan sababbin marubuta ne, duk da haka akwai fitattu da suka yi tashe, wasu tun daga haihuwa da ƙuruciya, ba su kuma daina ba har zuwan ‘ya’yan da jikoki. Cikin irin wannan fasali akwai irin su Rahma A. Majid da kuma su Hafsat A. Sodangi da Zuwaira Isa da Bilkisu Ahmed Funtua, da dai sauransu da dama.

Daga cikin maza kuwa, littattafan Nazir Adam Salihi su ne suka fi karɓuwa da tashe kuma ya rubuta littattafai guda 13. Shi kuma yanayin gabatar da jigon littattafansa ya sha bamban da na sauran marubutan wannan zamani, domin wani lokaci za ka ga labaran nasa na soyayya ne, amma cikin ban takaici, wata sa’a ma da ban tsoro. Sai dai irin yadda yake wasa da harshe a cikin littattafan nasa ya sa yawancin masu karatu ke biye da shi a kullum.

Maje El-Hejeej Hotoro shi ma wani marubucin ne da litattafansa da kuma tauraruwarsa, musamman a wannan zango suka yi tashe. Shi ma ɗin yakan yi amfani da jigon soyayya ko kuma jigon ban tsoron da jan hankali.

A daidai kuma cikin wannan zango ne aka soma ganin ɓullar sabon tsarin rubutun Adabin Kasuwar Kanon. Da farko dai an sami marubutan da suka canza akalar rubutun nasu domin ya dace da zamani musamman ganin cewa an sha suka da taƙaddama kan yawaitar rubuce-rubuce kan soyayya da aure. Ire-iren waɗannan marubuta sun haɗa da Bala Anas Babinlata da Ibrahim Sheme da Sakina A. Aminu da Rahma A. Majid da Saliha Abubakar Abdullahi da sauransu da dama.

Daga nazarin da aka yi, an fahimci cewa yawancin waɗannan marubuta ko dai ilminsu na zamani ne da suka yi nisa a ciki ya sa littattafan nasu suka yi armashi; wato kamar Ibrahim Sheme da Rahma Majid da suka nazarci adabin duniya daban-daban, da yake sun yi digiri, Ibrahim Sheme har digiri na biyu ya yi, ko kuma sun dai tsara littattafan ne domin su ɗan sha bamban da waɗanda aka saba ji da gani a wannan zango bisa sani, domin sun ga yadda aka daɗe ana ta kai-kawo game da neman sauyi, wato kamar su Babinlata da Rahma da Saliha da Abdullahi da Mukhtar Yaron Malam.

Duka dai alamu ne da ke nuni da cewa sabon yanka rake na Adabin Kasuwar Kano ya shigo kasuwa. Baya ga wannan kuma ga gasar ƙaga littattafai da ta kunno kai, musamman ta Bashir ƙaraye da aka fara a shekarar 2007, wadda ta ba da dama aka sake ɗaga martabar rubutun da kuma marubutan wannan zango. A nan ana maganar irin su Ibrahim Sheme da Lawan Barista da Maje El-Hajeej da suka cinye gasar rubutun a cikin wannan zango. 

Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

Karanta Adabin Kasuwa A Ƙasar Hausa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceKarin Lafazi (ACCENT)
Labarin na GabaSiffofin Adabin Kasuwar Kano
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.