Nafilolin Sallah.

0
1221

Nafilolin Sallah sun kasu gida biyu:

1- Nafiloli sakakku: Waɗannan su ne nafilolin da ba a ƙayyade adadin raka’o’in su ko lokacinsu ba.. Irin waɗannan nafiloli mutum zai yi niyyar nafila ya sallaci abin da ya sauwaƙa, duk raka’a biyu ya yi sallama, amma lallai a yi waɗannan nafiloli a lokacin da aka halatta yin nafila su ne dab da ɓullowar rana da dab da faɗuwar rana, wato bayan sallar Asuba da kuma bayan Sallar La’asar.

2- Nafiloli ƙayyadaddu: Su ne waɗanda nafiloli da suke da adadi da lokaci, sun kasu gida biyu:
a- Ratiban Nafiloli
b- Nafiloli waɗanda ba ratibai ba.

Domin karanta cikakken bayani a kan Ratiban Nafiloli danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFa’idojin Da Sallar Nafila Ta Ƙunsa
Labarin na GabaRatiban Nafiloli