Mutuwar Mata Masu Jego

0
19

Duk mai jegon da bayan haihuwa ko da da kwana 1 ne ballantana a ce an kwana uku da haihuwa ta ji alamun zazzaɓi, ko ciwon kai, ko ciwon ƙirji da sauransu. Toh lallai ta sanar a hanzarta kai ta asibiti kar a kuskura! ina maimaitawa kar a kuskura! a ce ai ba komi ta sha paracetamol ko a ce za a nemo Maganin ulcer kurum a ba ta babu komi. Hakan tamkar tallafawa me ƙoƙarin kashe kai ne.

Sau tari a yanzu akan zo taron suna me jego ba lafiya sosai, amma tai ta juriyar banza saboda cutar da kai, alhalin ƙwayoyin cuta sun sami hanya ta dalilin jinin nifasi da ke fita sun shiga cikin jijiyoyin jininta suna haifar matan da puerperal fever da zai kai ta ga “Puerperal sepsis” yai ta cinta a jika tana zaton abu ne da zai zo ya shige ƙarshe sai gawa.

Galibi wannan shi ke kashe masu jego in kika cire batun zubar jini bayan haihuwa, musamman bayan kwana 3 da haihuwa zazzaɓin ya fi somawa domin incubation period ɗin kenan na ƙwayoyin cutar, shi yasa wata sai bayan an yi taron suna ana murna kurum a ji an wayi gari wance ta mutu, mutuwa me duka.

Kada a taɓa ɗaukar hakan da wasa, ko baka da kuɗi ranto ka kai ta asibiti, matuƙar me jego tace ba ta lafiya ƙasa da kwana 40 da haihuwa kar ai wasa.

Ku kuma ƙananun jami’an lafiya da ke bibiyar rubutuna kodayaushe ku sa wannan cikin kanku, kar me jego tace:-

– Tanajin kasala,
– Kanta na ciwo
– Zazzaɓi
– Fitar farin ruwa ko jini me ɗoyi
– Ciwon Mara
– Zafin fitsari
– Ko har yau girman cikinta yana nan da sauransa kamar ba ta haihu ba ko kamar da sauran jariri a ciki

Ku ce za ku ba ta maganin rage zugi kurum ku sallame ta, ko kuwa ku ce za ku yi gwajin Malaria don haka in ya nuna Negative sai dai ku ba ta pain reliever, ko kuma in aka yi kiciɓis ga Malaria positive ku ce iya Malaria ke damunta.

Kuke buɗe tunaninku sosai for differentials diagnosis, kada a ce komai in ya haɗu da ciwon kai kurum Malaria ko Bp, ko Typhoid ne, duk macen da kuka ji ta yi muku ƙorafin ɗaya ko biyu daga waɗancan alamun na sama kai tsaye ku yi treating ɗinta for puerperal infection muddin me jego ce, domin hakan na da alaƙa da haihuwarta. Mai jego ita ce wadda ba ta wuce kwana 42 da haihuwa ba. Don haka ko da ta yi wata da haihuwa duk da haka tana cikin hatsari har na zubar jini.

Ya rage naku ku je ku yi biyayya ga manyanku da kuke aiki ƙarƙashinsu, su ilmantar da ku magungunan da alluran da ake amfani da su wajen addressing din matsalar, don ba kowanne antibiotics ake ba su ba, in su ma ba su sani ba toh ku je sahihan journals na obstetrics and gynecology ku yi binkice ku ilmantar da kanku ba wai google ba. Wannan lamari ne da kan zamo Medical Emergency.

Wannan tasa ko ɓari mace ta yi sai an ba ta magungunan antibiotics, haka ma bayan haihuwa domin riga-kafi koda ƙwayoyin cutar sun maƙale to zai magance su kafin su yi ƙarfin da za su shiga jini tunda ido bai iya ganinsu. AMMA wasu marasa tunanin cikin mata ba sa sha, ko in sun fara sai su bar sha tun kafin ya ƙare, toh masu irin wannan ku kuka da kanku, Domin ba zubar jini ne kurum abin tsoro ba bayan haihuwa.

In muka kiyaye wannan za mu taimaka wajen rage wasu mace-macen na masu haihuwa.

Allah yasa mu dace.

Danna nan don karanta Rashin Kogon Al’aura Ga Mata

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceSumbatar Mace Ga Me Azumi
Labarin na GabaShan Azumi Ga Matafiya